Talakawan Najeriya na ji a jikinsu yayin da ake zargin masu kudi na saye amfanin gona a sassan kasar suna boyewa don ya yi muguwar tsada.
A bana dai ba a ci gajiyar saukin da ake samu na abinci a lokacin kaka ba, saboda farashin amfanin gonar ya ci gaba da hauhawa a daidai lokacin da kaka ta shigo.
- ‘Magidanci ya kama matarsa na soyayya da tsohon mijinta‘
- Yadda ’yan Arewa ke kaura daga Ibadan bayan rikicin Sasa
- Yadda ‘dattawa’ ke goya wa matasa baya suna ta’asa a Jos
Alamu sun kuma nuna cewa dillalan-zaune da ake kira ’yan baranda na neman fin manoma cin ribar shirin bunkasa noma da gwamnati ta fito da shi don wadata kasa da abinci.
Binciken da Aminiya ta yi a wasu jihohi ya kuma gano cewa tsadar kayan aikin gona da bude iyakokin kasa na daga cikin dalilan da kayan abinci musamman masara da shinkafa da gero da dawa suka yi tashin gwauron zabo a daidai lokacin shigar kakar.
’Yan baranda na saye abinci su boye
A Taraba, Aminiya ta gano cewa ’yan baranda da ke sayen masara da wake da gero da shinkafa da dawa sun fito ne daga jihar da wajenta.
A garuruwan Mutum Biyu da Garba-Chede da Iware da Maihula da manyan kasuwannin hatsi na jihar, dillalan-zaunen na da yaran gida da suke bai wa makudan kudi su saya musu daruruwan buhunan abinci su ajiye a sito-sito zuwa lokacin da farashinsu zai tashi kafin su sayar.
Kuma a bana, ana fara girbe amfanin gonar dillalan-zaunen suka fara sayewa inda kafin farashin ya tashi sun sayi amfanin gona mai yawa.
Wani manomi a garin Bali mai suna lbrahim Abubakar, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan barandar sun fi manoma samun riba saboda akasari kananan manoma na sayar da amfanin gonarsu da sauki.
Ya ce a farkon kakar bana an sayar da buhun masara Naira 8000, amma yanzu ya kai Naira 17000 a jihar.
Ya ce duk dan barandar da ya sayi masara a farkon kaka yanzu riba ta doki uwar kudi.
Ya ce kananan manoma kan yi awo kafin sabon amfanin gona ya zo domin sun sayar da abin da suka noma a farkon kaka.
Wani manomi mai suna lbrahim Lawal ya ce bayan ’yan barandar akwai masu ba manoma bashin kudi da iri da maganin feshi su kuma manoman su biya su da amfanin gona.
Ya ce wannan tsari na ‘Ba-da-kaka’ salo ne da masu hannu da shunin ke cutar manoma a yankunan karkara.
Ibrahim Lawal ya ce a karkashin tsarin ana ba manoma bashi kan za su bayar da buhun masara ko shinkafa a kan Naira 4,000-5,000 koda ana sayar da buhun a kan Naira 10,000 a kasuwa.
Tsadar kayan noma
A Jihar Bauchi, wadansu ’yan kasuwa da manoma sun ce haraji da tsadar man fetur da wutar lantarki da rashin tausayi da tsoron Allah na cikin abubuwan da suke sa tsadar abinci a kasar nan.
Wani manomi a jihar, Alhaji Isa Mato ya ce shinkafa ta gagari marasa karfi saboda tsada, inda ya ce farashin buhun shinkafa ya fara daga Naira 15,500 har zuwa dubu 22.
Sai ’yar kasar waje Naira dubu 26 zuwa dubu 28, kuma kwanon shinkafa ’yar gida ya kama daga Naira 500 zuwa 700, yayin da ’yar waje ya kai Naira 800.
Alhaji Mato ya ce hakan ya faru ne saboda tsadar noma inda ya ce in za a noma eka daya sai an kashe Naira dubu 250 zuwa dubu 300, kafin ta iso gida.
“Ka je kasuwa yanzu ka taya buhun taki, na Naira 5,500 ya kai Naira 10,000 ko fiye,” inji shi.
Ya ce mutane suna dora alhakin haka kan tsadar kayan aikin noma da kunci da tsadar rayuwa sai tashin kudaden waje da tsadar mai da kamfanonin taki da na kayan gona ke amfani da shi da tsadar wutar lantarki da mugun halin ’yan kasuwa marasa tausayi da suke saye su boye abincin don ya yi tsada.
Yawancin ’yan kasuwar sun ce mutane sun fi sayen taliya da ake sayar da katan kan Naira 4,000-4,200.
Wani masanin tattalin arziki, Dokta Bala Ahmad ya ce matsalar ta faru ne saboda dalilan da suka hada da rashin niyyar gwamnati ta kyautata wa talaka ko sawwaka masa rayuwa da yawan haraji iri-iri a bankuna da tsadar kudin mai da na lantarki da tsada da karancin kayan noma sai rashin noma isasshen abinci a bara.
Dokta Ahmad ya ce tsadar ba za ta kare ba, sai hukumomi sun dauki matakin da ya dace don kauce wa fuskantar matsalar yunwa.
Matsalar tsaro ta haifar da tsadar abinci
A Jihar Katsina, wani manomi Dokta Mato Mai Magani Lambar Rimi ya ce, abin da ya jawo tsadar shi ne matsalar tsaro da ta addabi sassan jihar musamman yankunan da aka fi noma masara da dawa da wake da gero.
Ya ce hare-haren ’yan bindiga masu satar shanu da garkuwa da mutane sun taimaka sosai wajen jawo karanci abinci.
“A wadancan yankuna da ake fama da matsalar tsaro, baya ga rashin noma wasu gonakin ta kai ana ji ana gani an bar kayan gona sun lalace, wasu an noma amma an hana manoma girbe su, yayin da wasu aka yi raba-daidai da maharan.
“Wasu yankunan sai an biya kudi kafin manomi ya kwashi amfaninsa. Ka ga dole a fuskanci matsalar tsada,” inji Dokta Mato.
Ya ce, sannan idan aka dubi Gabashi da Kudunci da Arewacin jihar, abin da suka noma ba ya isa, ga kuma tsadar noma da aka fuskanta ga karancin takin zamani saboda kamfanoni da dama sun rufe sakamakon cutar Kwarona.
Malam Maharazu Mai’awo cewa ya yi, “Ko cikin damina tiyar wake ba ta wuce Naira 400 ba, amma yanzu Naira 800 zuwa 1,000 ake sayarwa.
“Masara da gero da dawa farashinsu ya gaza tsayawa wuri daya.
“In yau ka sayo buhun abinci gobe in ka koma za ka tarar an kara 1,000 zuwa 2,000, kuma ba shigowa ake yi da shi ba.
“Batun da wadansu ke yi cewa, wai bude iyaka ta kara haifar da tashin farashi, suna yi ne don ba a cikin harkar suke ba.
“Yanzu in ba don shinkafar da ake fada a kanta ba, gaya mini ta gidan yaya farashinta yake?
“Sannan waken suya ko zobo shigowa ake yi da su?
Masu kudi na da hannu a tsadar abinci
“Wannan matsala wadansu daga cikin masu kudinmu sun taimaka, rana daya sai mai kudi ya tura mutane kasuwa su saye mafi yawan abincin da ya lura mutane na bukata ya kai ya boye, sai bayan mako biyu in ya ji an cika nema ya fiddo ya sa farashin da ya ga dama.”
Mutane da dama sun ce akwai masu saye abincin suna boyewa, wadansu ma har bashin bankuna suke ci don yin wannan tanadi.
Bude iyakoki ya kawo tsadar abinci —Sarkin Hatsi
Sarkin Hatsin Saminaka da ke Jihar Kaduna, Alhaji Manu Isah Idris ya ce sake bude iyakokin kasar nan na cikin dalilan da suka jawo tsadar kayan abincin.
Alhaji Manu ya ce, tun shigowar kaka mutane ke shiga yankin sayen abinci.
“Mutanen da ba a taba ganin su ba a yankin nan, bana sun shigo sayen amfanin gona, har daga kasashen Nijar da Kamaru da Chadi.
“Za ka ga mutanen Legas da Maiduguri da Ibadan da Kano suna ta shigowa don su sayi masara.
“Sannan kamfanonin da muka gani ba mu taba ganin irinsu ba.
“Wasu dillalan kayan amfanin gona da suka kai wa kamfanoni kaya, sai a ce ga wani kamfani ya yi karin kudi kan masarar da yake saye.
“Don haka, sai sun zabi kamfanin da suke so, su kai masa kaya.
“Kusan ko’ina a yankin nan, za ka ga kamfani ya yi rumfar sayen amfanin gona yana tarawa,” inji shi.
Ya ce abin akwai ban tsoro domin tunda ya zama Sarkin Hatsin Saminaka shekara 10 da suka wuce, bai taba ganin irin bana ba.
Ya ce tun shigowar kaka duk mako, sai farashin masara ya tashi sama.
A cewarsa, a baya sai a yi wata uku farashin masara bai tashi ba, amma bana idan mutum ya sayi masara, kafin ya dawo, kudin da ya sayar wa kamfani ba zai iya saya masa kamar wadda ya sayar ba.
“Ka ga farkon shigowar kaka an sayar da buhun masara Naira 11,500 zuwa 12,000. Daga nan ya koma Naira 13,000.
“Bayan bude iyakoki farashin ya ci gaba da hauhawa.
“Yanzu buhun masara ya haura Naira 17,000, ba mu san abin da zai faru gobe ba,” inji shi.
Sarkin Hatsin Sami aka ya ce cutar coronavirus da ta karya tattalin arzikin duniya da sake bude iyakokin kasa sun taimaka wajen tsadar abincin.
Ya ce in aka cire Amurka babu inda ya kai Najeriya arahar masara.
“Don haka tunda aka sake bude iyakokin kasashen makwabta ke shigowa suna sayen abinci suna tafiya da shi.”
Sarkin Hatsin ya ce kamfanonin da suka ba manoma rancen taki da iri da maganin feshi, wani ya ranci tirelar taki 100 da suka zo karbar masarar, hakan ya sa wadanda suka karbi rancen suna saye masarar a kasuwa don biyan kamfanonin.
Abin ya yi tsanani, sai an taimaka
Ya bukaci gwamnati ta tallafa wa manoma da taki da maganin feshi a kan lokaci don a tunkari damina mai zuwa.
“Su kuma manoma a ci gaba da addu’a, domin wannan abu ya zama fitina, ya wuce tunanin manoma, a ce a wannan lokaci buhun masara ya haura Naira 17,000 abin ya zama masifa, don haka mu ci gaba da addu’a,” inji shi.
Farashin kayan miya ya fadi warwas
Sai dai yayin da farashin hatsi ke ci gaba da tashi a sassan Najeriya, farashin kayan miya irin su albasa da tumatir da attarugu da shambo da a baya ya yi matukar tashi, yanzu ya fadi kasa warwas.
Binciken da wakilinmu ya gudanar a Kasuwar ’Yan Tumatir da ke Farar Gada a garin Jos, Jihar Filato, ya gano cewa buhun albasa da aka sayar a watan Disamban bara kan Naira dubu 70 yanzu ya dawo Naira dubu 6.
Sannan babban kwandon tumatir da aka sayar Naira 8,000 da karami da aka sayar Naira 5,000 a Disamban barar, yanzu sun dawo Naira 2,000 da 1,000.
Buhun tattasai na Naira 15,000, ya dawo Naira 4,000; solon tarugu da aka sayar Naira 15,000 yanzu Naira 3,000; yayin da buhun shambo da aka sayar Naira 11,000 ya komo Naira 3,000.
Da yake zantawa da wakilinmu kan faduwar farashin kayayyakin, Mataimakin Shugaban Kasuwar ta Farar Gada, Abdullahi Yusuf, ya ce abin da ya kawo saukar farashin, shi ne kayan gwari na rani sun fito, kuma masu sayen kayan babu kudi a wajensu.
Ya ce duk da faduwar farashin kayan, babu ciniki saboda halin da ake ciki na rashin kudi.
“A bara a daidai irin wannan lokaci, kullum muna samun masu saye a motocin J5 sama da 10, amma a bana ko mota 3, ba sa iya saye, saboda baki masu zuwa sayen kaya sun yi karanci a kasuwar.
“A shekarun baya duk Najeriya ba jihar da ba ta zuwa sayen kaya a wannan kasuwa, amma yanzu daga Fatakwal kadai ake zuwa sayen kaya a kasuwar,” inji shi.