Laraba 1 ga watan Satumba, 2021 ce ranar da ake tunanin ikon kasar Afghanistan zai koma cakokan hannun kungiyar Taliban.
Kungiyar ta mamaye Fadar Gwamnatin Afghanistan ne mako biyu kafin cikar wa’adin janyewar sojojin Amurka daga kasar, shekara 20 bayan sun kifar da gwamantinta a 2001.
Sojojin Amurka sun kammala ficewa daga kasar kafin wayewar garin Talata 31 ga Agusta, 2021.
Ga jerin wasu muhimman abubuwa da suka faru har kungiyar ta karbe iko da kasar cikin ’yan watanni:
– Afrilu 14: Sanarwar janye dakarun Amurka:
Shugaan Amurka Joe Biden ya sanar da shirin fara janye sojojin kasarsa daga Afghanistan daga ranar 1 ga watan Mayu zuwa 11 ga watan Satumba, ko da yake da farko wa’adin da suka amince da Taliban shi ne ranar 1 ga Mayu.
Ya bayar da sanarwar tasa ne bayan shekaru ana tattaunawar zaman lafiya a Afghanistan tsakanin Amurka da wakilan Taliban a birnin Doha na kasar Qatar.
– 4 ga Mayu: Hare-haren Taliban:
Mayakan Taliban sun kai wa dakarun Afghanistan wani babban hari a lardin Helmand da wasu larduna akalla shida.
– 11 ga Mayu: Taliban ta kwace Nerkh:
Kungiyar ta kwace gundumar Nerkh da ke kusa da birnin Kabul, a yayin da rikici ke kara kamari a fadin kasar.
– 7 ga Yuni: Kashe sojoji 150:
Gwamnatin kasar ta sanar da cewa Taliban ta kashe mata sojoji akalla 150 cikin sa’a 24 a yayin da ake ci gaba da gwabza fada a larduna 26 daga cikin 34 na kasar.
– Yuni 22: Hare-hare a Arewaci:
Taliban ta kwace sama da 50 daga cikin gundumomi 370 da ke Arewacin kasar inda ta kaddamar da hare-hare, nesa da yankin Kudancin da take da karfi, inji Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan.
– 2 ga Yuli: Janyewar sojojin Amurka daga Bagram:
A sirrance, sojojin Amurka suka fara janyewa daga babban sansaninsu, Bagram, kusa da birnin Kabul.
Janyewar ta kawo karshen tsoma bakin kasashen Yamma a yakin Afghanistan da Amurka ta shekara 20 tana jagoranta.
– 5 ga Yuli: Tayin zaman lafiya:
Taliban ta ce za ta iya gabatar da tayin zaman lafiya ga gwamnatin Afghanistan zuwa watan Agusta.
21 ga Yuli: Kwace rabin Afghanistan:
Mayakan Taliban sun kwace iko da kusan rabin gundumomin kasar, a cewar wani babban hafsan sojin Amurka, yana nuna girma da saurin mamayar da kungiyar ke yi.
– Yuli 26: Taimakon Amurka ga Afghanistan:
Amurka ta yi alkawarin ci gaba da tallafa wa sojojin Afghanistan “a cikin makonni masu zuwa” tare da tsaurara hare-hare da jirage don taimaka musu wajen dakile hare-haren Taliban.
Yuli 26: Fararen hula da aka kashe sun karu:
Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe ko an jikkata fararen hula kusan 2,000 a watannin Mayu da Yuni a rikicin, wanda shi ne adadi mafi yawa tun daga 2009 da aka fara daukar alkaluma.
Agusta 6: Kwace Zaranj:
Zaranj, babban birnin lardin Nimruz, ya zama hedikwatar lardi na farko a Kudancin Afghanistan da kungiyar ta kwace a tsawon shekaru.
A lokacin mulkin Taliban ba ta samu cikakken iko da Arewacin kasar ba, amma yanzu ta kwace yankin kafin ta tunkari birnin Kabul.
7 ga Agusta – Sheberghan:
Taliban ta sanar da kwace daukacin lardin Jawzjan na Arewacin kasar inda ta kwace gine-ginen gwamnati.
8 ga Agusta – Sar-e-Pul:
Kungiyar ta kwace Sar-e-Pul, babban birnin lardin Arewa kuma na farko a cikin cibiyoyin larduna uku da kungiyar ta kwace a rana guda.
8 ga Agusta – Kunduz:
Kungiyar ta kwace Kunduz a Arewacin kasar, wanda kuma ake gani a matsayin babbar riba ga kungiyar, kasancewar garin mashigar lardunan Arewa masu arzikin ma’adinai da kuma tsakiyar Asiya.
8 ga Agusta – Taluqan:
Babban birnin lardin Takhar, shi ma a Arewa, ya fada hannun Taliban, inda ta saki fursunoni.
9 ga Agusta – Aybak:
Aybak, babban birnin lardin Samangan da ke Arewacin kasar ya koma karkashin kungiyar.
10 ga Agusta – Faduwar Farah:
Kungiyar ta kwace babban birnin lardin Farah, da ke Yammacin kasar.
10 ga Agusta – Pul-e-Khumri:
Ta kuma kame hedikwatar lardin Baghlan da ke tsakiyar kasar.
Agusta 11 – Faizabad:
Hedikwatar lardin Badakhshan da ke Arewa maso Gabas ta fada hannun kungiyar.
12 ga Agusta: Ghazni:
Babban birnin lardin Ghazni da ke Kudu Maso Gabas ya shiga hannun kungiyar.
Agusta – 12: Herat:
Bayan makwanni biyu na gwabza fada, babban birnin lardin Herat da ke Yammaci, kuma birni na uku mafi girma a kasar, ya koma hannun Taliban.
12 ga Agusta – Kandahar:
Birnin Kandahar da ke Kudanci ya koma karkashin ikon kungiyar.
13 ga Agusta – Helmand:
An kwace babban birnin lardin Helmand, Lashkar Gah, a kudanci.
Agusta 15 – Mamaye Kabul:
Mayakan Taliban sun kwace fadar gwamnati a birnin Kabul.
Shugaban kasa ya tsere:
Shugaban Kasa Ashraf Ghani ya tsere daga kasar, ya kuma sanar cewa ya amince Taliban ta yi nasara.
A cewar Mista Ghani wanda jami’an gwamnati kuma suka mika iko ga kungiyar a sassan kasar ya ce ya tsere ne domin kauce wa zubar da jini a kasarsa.
Yanzu haka ya samu mafakar siyasa a Hadaddiyar Daular Larabawa.
Taliban ta mamaye birnin Kabul
Cikin kwana 10 da suka biyo bayan mamaye daukacin birnin Kabul, kungiyar ta mamaye sassan kasar, inda yanzu ta karbe iko, in ban da ’yan tsirarun yankuna inda wasu ke mata turjiya.
Kwanaki kadan bayan karbe Kabul, kungiyar ta yi taron ’yan jarida na farko, inda ta yi alkawarin kare ’yan kasar, aiwatar da shari’ar Musulunci, barin mata su nemi ilimi su kuma yi aiki da kuma afuwa ga tsofaffin makiyansu.
Kakakinta ya kuma sanar cewa kungiyar za ta fitar da sabon tsarin tattalin arziki da fasalin gwamnati, wanda ya ce a wannan karon shugabanninsu za su rika fitowa fili kuma za su kyautata alaka da kasashe.