Yayin da kowa ke fatan samun mai kaunarsa har zuci kuma wanda shi ma yake so, daga cikin burin masoya akwai na suka kasance tare, mutu-ka-raba.
Amma wani lokaci ana cikin haka, a hankali sai ka ji ai wane da wance, wadanda masoya ne, sun rabu. A ce ya rabu da ita, ko a ce ita ce ta rabu da shi. Ruwa dai ba ya tsami banza.
Hakan ne ya sa Aminiya ta zanta samari da ’yan mata don gano abubuwan suke kyama a cikin soyayya da ke kaiwa ga rabuwa da juna:
Karya:
Imran Gambo, daga cikin matasan da ya ce, karya na daga cikin manyan abubuwan da ke kawo wa soyayayya karar kwana.
“Misali ita tana mishi karya ko shi yana mata, to duk ranar da dayan ya gane cewa karya yake masa, makaryacin zai fara fita maka a rai da hakan har takan iya kaiwa ga rabuwa, gaskiya.
“Soyaya da karya kuma ina amfaninta,” inji shi
Miyagun dabi’u:
’Yan mata da samari sun shaida mana cewa ba sa kaunar yin soyayya da saurayi ko budurwa da ke da munanan dabi’u.
Nusirat Lawal, ta ce miyagun halaye irin yawan shagala da shaye-shaye da kan zubar da mutuncin mutum na cikin abubuwan da ke yin ajalin mosoyya.
Yaudara:
Yaudara, kamar yadda Khadija Abulkarim ta bayyana na shi ma daya ne daga cikin abubuwan za su sa ta rabuwa da saurayi.
A cewarta, soyayya yarda ce da kuma amana da nufin kasancewa tare da juna a matsayin abokan rayuwar auratayya idan Allah Ya yi.
Sai dai ta ce daga mazan har mata babu bangaren da ba a samu yana ha’intar irin wannan yardar a tsakanin bangarorin.
Rashin magana:
Wani matsahi, Abubakar salis ya ce rashin yin magana da juna musaman na tsawon lokaci shi ma yakan kaiwa ga mutuwar soyayya.
“Misali idan ba sa samun lokacin juna, ba a kiran juna, hakan zai iya yana kawo tunani da kokwanto iri-iri, kowa zai rika tunani.
“Shi zai rika tunanin ta yi sabon saurayi, ita ma za ta rika tunanin ya yi sabuwar budurwa.
“In kuma ba haka ba akwai yiwuwar su rika tunanin anya soyayyar da wane ko wance ke min ta kai zuci kuwa? Ai da yana so na da zai rika kira na”, inji ta.
Nisa:
A cewar Nana Yahaya, nisa tsakanin masoya a wasu lokutan na gurgunta soyayya har ma ta kai ga rabuwar masoya.
Idan nisa tsakaninsu ta yi yawa, haduwa da juna zai kasance abu mai wuya, don haka a hankali akan iya samun matsala ko karancin damuwa.
Faruwar hakan na iya haifar da wata matsala da kan iya kaiwa masoyan su raba jiha.
Kadan ke ke nan daga cikin abubuwan wasu matasa suka bayyana mana. Da fatan za a kiyaye wadannan ko za a kiyaye.