Har yanzu a cikin kowace haihuwa dari a Arewacin kasar nan sai mata akalla biyar sun mutu.
Wato idan aka haihu a gida dari a unguwa, to mata biyar suna iya rasa ransu sakamakon abubuwan da za mu zayyana a kasa:
1. Hawan jini: Wannan ya fi kama mace a haihuwar fari musamman idan akwai mai hawan jini a danginta. Shi yake sa jijjiga da suma har da rasa rai a wasu lokutan. A wurin awo ne ake gano ko akwai wannan ciwo a mai juna biyu ko babu.
2. Tsinkewar jini: Iri biyu ne akwai wanda kan tsinke kafin haihuwa akwai kuma na bayan haihuwa.
Wanda ke tsinkewa bayan an haihu ya fi hadari sosai domin ya fi zuwa da yawa kuma da karfinsa zai ta zuba ta yadda idan ba a dauki mataki ba, jinin jiki kan kare nan da nan.
3. Doguwar nakuda: Duk matar da ta yini ta kwana tana nakuda a sama mata lafiya a kai ta asibiti, domin nakuda bai kamata ta wuce awa 14 ba, ko da haihuwar fari ce.
Ita doguwar nakuda ta fi jawo salwantar ran jariri fiye da na uwa. Takan jawo wa uwa galabaita sosai don takan iya sa ciwon yoyon fitsari.
4. Jinkirin zuwa asibiti: A likitance akwai jinkiri guda uku da sukan sa salwantar rayuka a mata masu juna biyu fiye ma da abubuwan da muka lissafa a sama.
Jinkiri na farko shi ne wanda kan faru kafin a fito daga gida; akan dauki lokaci idan abu ya faru ga mai juna biyu kafin a fito daga gida, misali haihuwa ta zo matar ita kadai ce a gida.
Sai kuma jinkiri na tafiya asibiti. Wato idan an yanke shawarar a tafi asibitin, to tafiyar ma kan zamo wani jidali musamman idan daga lungu ko kauye za a fito.
Sai kuma jinkiri na uku, wanda akan samu a asibiti kafin a fara kula da marar lafiya. Wato dole sai an bata lokaci, a ce sai an yanki kati, sai likita ya zo, sai an yi gwaje-gwaje da sauransu.