Ko shakka babu Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo yana daya daga cikin masu ruwa-da-tsaki da za a dama da su a zaben badi a daidai lokacin da ake kara samun masu son neman tikitin takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar APC.
Duk da cewa Farfesa Osinbajo, bai fito ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar Shugaban Kasa a badi ba, amma kungiyoyi da jama’a da dama da ke goyon bayansa sun yi kaurin suna wajen ganin gwanin nasu ya amsa kiran ya fito takarar.
- AFCON 2021: Karon battar abokai tsakanin Salah da Mane a wasan karshe
- ’Yan bindiga sun kashe mata da yara kusan 20 ana tsaka da sallar Juma’a a kauyukan Zamfara
Kungiyoyin da suke goyon bayansa suna tuntubar masu ruwa-da-tsaki a fadin kasar nan duk da shelantawar da jagoran Jam’iyyar APC na Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi na cewa zai nemi takarar Shugaban Kasar a badi.
A shekarar 2015 ne Tinubu ya ba da sunan Osinbajo a matsayin mataimaki ga takarar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari domin ya kawar da damuwar da ta kunno kai a lokacin ta Shugaba Buhari Musulmi ne da ake ganin dole ne ya dauki mataimaki da ba Musulmi ba, hakan ya haifar da samuwar Farfesa Osinbajo.
Burin Farfesan Shari’a mai shekara 64, kuma yake Mataimakin Shugaban Kasa tun shekarar 2015, shi ne na samun kakkarfan goyon baya daga wadansu sarakunan Arewa da kuma wadansu gwamnoni hudu na Arewa, biyu daga Arewa maso Yamma da biyu daga Arewa ta Tsakiya wajen mara masa baya, saboda abin irin biyayyarsa ga Shugaban Kasa.
Shin Osinbajo zai iya samun nasarar wannan tafiya ta neman takarar Shugaban Kasa cikin kwanciyar hankali? Wannan wani batu ne da ke bukatar samun amsa don magance wasu kalubale da manazarta suka gano kan niyyarsa ta neman ya gaji Shugaba Buhari.
Wannan hasashe da Aminiya ta yi ya fito da wasu kalubalen da dan siyasar wanda ya fito daga Jihar Ogun kuma yake zaune a Jihar Legas zai iya fuskanta, wadanda kuma za su iya kawo masa cikas a burinsa na zama Shugaban Kasa.
Matsalar da zai samu da Tinubu
Masu fashin baki suna ganin babbar cikas ta farko da Osinbajo zai fuskanta ita ce ta maigidansa wanda shi ma yake da burin zama Shugaban Kasa wato Tinubu, wanda ga alama ya fi samun farin jini a Arewa da Kudu maso Yamma kasancewar ya ci gaba da zama a jam’iyyar adawa kafin APC ta doke PDP a zaben 2015, bayan ta shafe shekara 16 tana mulki.
Suna ganin cewa dole ne Osinbajo, wanda ya taba rike mukamin Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a a karkashin Tinubu, ya yi kokarin ganin ya samu goyon bayan tsohon Gwamnan na Jihar Legas, don ya samu kara haskaka masa damarsa a zaben fid-da-gwani na Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC da za a yi a badi.
Wani babban dalilin da ya sa Mataimakin Shugaban Kasa ya zama dole ya samu goyon bayan maigidansa shi ne yadda yake da cikakken ikon juya jam’iyyar a Jihar Legas kuma yana da goyon bayan wadansu masu rike da mukamai da tsofaffin gwamnoni a cikin jam’iyya mai mulki da ke iya tantance inda za a yi zaben.
Sai dai kuma masu sharhi na ganin yiwuwar sulhun na fuskantar barazana ba wai kawai yakin neman zabe da magoya bayan jiga-jigan masu neman tikitin takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC su ke yi ba, har ma da shelar da Tinubu ya yi cewa zama Shugaban Kasa shi ne burinsa a rayuwa, wanda hakan ya tabbata ne lokacin da ya yi magana bayan ganawarsa da Shugaban Kasa a ranar 10 ga Janairun nan.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai kan bayanin da shugaban ya yi na cewa bai damu da wanda zai gaje shi ba, Tinubu ya ce: “Abin da muke yi ke nan wanda shi ne dimokuradiyya kuma shi dan dimokuradiyya. Bai nemi in tsaya ba, bai ce kar in tsaya ba. Domin wannan shi ne burina na rayuwa.
“To me ya sa nake tsammanin ya yi fiye da haka? Kuna gudanar da tsarin dimokuradiyya kuma dole ne ku rungumi ka’idoji da dabi’u da kyawawan dabi’un dimokuradiyya.
“Shi ke nan.”inji shi.
Tsoron tade shi
Wani babban tarnaki da mafarkin da Mataimakin Shugaban Kasar zai fuskata shi ne tsoron nuna masa kyama daga al’ummar Musulmin Najeriya, domin a matsayinsa na babban fasto na Darikar Pentikostal, bai taba boye ra’ayinsa na addini ba, sabanin ’yan siyasar Najeriya.
Osinbajo shi ne fasto mai kula da Lardin Legas 48 na Cocin Redeemed Christian Church of God. Jam’iyyar APC ta dauki fitaccen faston a matsayin abokin takarar Shugaban Kasa domin tabbatar wa al’ummar Kirista cewa akwai daidaito lokacin da Jam’iyyar PDP da ke mulki ta yi hasashen cewa Jam’iyyar APC jam’iyyar siyasa ce ta Musulmi.
Najeriya dai na ci gaba da fuskantar gasa mai tsanani a tsakanin manyan addinan biyu: Musulunci da Kiristanci.
Wannan ya haifar da jin shakkun juna a tsakanin mabiya addinan biyu domin a koyaushe ana yin taka-tsantsan da bin diddigin duk wani mataki na gwamnati da ke kan mulki, wanda ya kai ga yin amfani da kalmomi irin su ‘Musulmi’ da ‘Kirista”’.
A shiyyarsa ta Kudu maso Yamma, masu sharhi kan lamuran siyasa sun ce yana bukatar ya tabbatar wa Musulmi cewa za a kyale batun sanya hijabi da dalibai mata ke yi da sauran batutuwan da suke barazana ga zaman lafiya a yankin a makarantun gwamnati ba tare da tsoma baki kan al’amuran da ake ganin matsayin hakkin dan Adam ne tun asali da dokokin da suke cikin kundin tsarin mulkin Najeriya suka ba shi.
To sai dai halartar Osinbajo wajen taron tattaunawa na addini na 2019 mai taken: “Samar da juriya da yarda da addini” wanda ofishin jakadancin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ya shirya a Abuja da taron Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) da liyafar da Cibiyar Hulda da Jama’a ta Musulmi (MPAC) a karkashin jagorancin Shugabanta, Mista Disu Kamor, ta shirya a bara, ana kallon hakan a matsayin wani yunkuri na dabara da malamin addini ya yi don samun karbuwa a matsayinsa na dan siyasa don ya tabbatar wa da al’ummar Musulmi kudirinsa na inganta zaman lafiya da hadin kan addinai.
Samun goyon bayan Buhari da ‘Kabal’ a fadar Shugaban Kasa
Masu fashin baki sun ce goyon bayan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da na kusa da shi da ake kira ‘Kabal’ zai kara wa Osinbajo damar samun tikitin takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC.
Sun ce yana bukatar goyon bayan Kabal wadanda aka ce sun fusata da yanayin da yake gudanar da al’amuran mulki a lokacin da ya rike da mukamin Shugaban Kasa na riko.
Lamarin da ake ganin ba za a sake amincewa da shi ba, ganin irin yadda ya tafiyar da al’amuran mulki a lokacin da Shugaba Buhari yake jinya.
Kafin halin da ake ciki zuwa yanzu, Osinbajo ya dauki matakai masu muhimmanci dangane da yanayin mulkinsa a baya.
A yayin da Mataimakin Shugaban Kasar ke rike da mukamin Shugaban Riko ne ya mika wasika ga Majalisar Dokoki ta Kasa inda yake neman a tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Tu’annati (EFCC) a ranar 14 ga Yulin 2016.
Sai dai Majalisar Dattawa a karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki, ta ki amincewa da Magu bayan shafe watanni ana dambarwa a kan lamarin.
Haka a lokacin da Osinbajo yake Mukaddashin Shugaban Kasa a watan Fabrairun 2017 ne ya mika wasikar neman tabbatar da Mukaddashin Babban Jojin Najeriya (CJN), Mai shari’a Walter Samuel Onnoghen ga Majalisar Dattawa.
An tabbatar da Onnoghen amma aka kore shi ta hanyar da ta haifar da ce-ce-ku-ce kafin zaben 2019.
Haka Osinbajo a watan Agusta 2018 ya kori Darakta Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Alhaji Lawal Daura, daya daga cikin masu fada-a-ji a gwamnatin, wannan kora ta biyo bayan mamaye Majalisar Dokoki ta Kasa da jami’an tsaro suka yi.
Wasu majiyoyi a fadar Shugaban Kasa sun ce korar Lawal Daura ta fusata mutanen da ke kusa da Shugaban Kasar, don haka aka yanke shawarar ba za a sake mika masa matsayin Shugaban Riko ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, gani yadda Farfesa Osinbajo ke neman shige makadi da rawa, ta sa Shugaban Kasa ya rubuta wata takarda a watan Satumban 2019 inda Shugaban Kasar ya ba shi umarnin ya nemi amincewarsa kafin ya dauki duk wani mataki a wasu hukumomin da yake kula da su.
Kafin wannan sanarwa dai, sai da Shugaba Buhari ya rusa Kwamitin Kula da Tattalin Arziki (EMT) da ke karkashin jagorancin Osinbajo, tare da maye gurbinsa da Majalisar ba Shugaban Kasa Shawara kan Tattalin Arziki (PEAC) a karkashin jagorancin Babban Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tattalin Arziki.
Masu lura da al’amuran yau da kullum dai sun ce dole ne a yanzu Osinbajo ya samo hanyar da zai kwantar da hankalin makusantan Shugaban Kasar tun bayan faruwar wasu al’amura a zamanin marigayi Shugaban Ma’aikata na Fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari.