Kun san cewa Pele, wanda shi ne dan wasan kwallon kafa da babu kamarsa a duniya, ya koyi murza leda ne a wurin mahaifinsa?
Duniyar kwallon kafa ta sallama cewa Edson Arantes do Nascimento, wanda aka fi sani da Pele, shi ne dan wasan da ya yi wa kowa fintinkau a duniya.
- Yadda Rasuwar Pele Ta Girgiza Duniyar Kwallon Kafa
- NAJERIYA A YAU: Yadda Karin Albashi Zai Shafi Rayuwarku
Sai dai kuma gwarzon ya kwanta dama a ranar Alhamis, yana da shekara 82, mutuwar da ta kidimi duniyar kwallon kafa.
Pele bakar fata ne dan kasar Brazil da aka haifa rana 23 ga Oktoba, 1940, kuma ya bar tarihin da ba zai gogu ba.
Mahaifinsa ne ya koya masa buga kwallo kuma fara buga wasa a kulob din Santos yana shekara 15
Ya fara buga wa kungiyar kwallon kafa ta Brazil wasa yana da shekara 16 kuma shi ne ya fi ci mata kwallo (77 a wasanni 92) — kafin Neymar ya kamo shi a Gasar Cin Kofin Duniya na Qatar 2022 da aka kammala
Shin kadai dan kwallo kafa da ya taba cin Kofin Duniya sau uku a tarihin gasar na shekara 92
Kwamitin Wasannin Olympic na Duniya ta ayyana Pele a matsayin dan wasan da ba a yi kamarsa ba a shekara 100
Shi ne dan wasa mafi kuruciya da ya fara buga Gasar Kofin Duniya yana shekara 17 a 1958 a kasar Sweden
A gasar ce Brazil ta fara cin Kofin Duniya, inda ya ci kwallo biyu a wasan karshe, wanda bayan an kammala abokan wasansa suka duake shi a kafadunsu saboda tsananin murna
Shi ne ya ci kwallon karshe a gasar ta 1970, a wasan karshe tsakanin Brazil da Mexico
Yana daga cikin mutane mafi shahara a duniya a karni na 20 da kuma bakaken fata mafiya shahara a duniya
A 1977 Majalisar Dinkin Duniya ta zabe shi a matsayin halastaccen dan kasa a ko’ina a fadin duniya
Bai taba buga wasa a gasar kasashen Turai ba amma sau uku yana zuwa Najeriya domin buga wasa
Sau biyu yana zuwa buga wasan zumunci a lokacin Yakin Basasar Najeriya a 1969 (a Legas da Benin) wanda ya sa aka tsagaita wuta na tsawon kwana biyu tsakanin bangarorin da ke yaki da juna
Pele ne ya zura kwallaye biyu da kungiyar Santo ta sanya a ragar Green Eagles na Najeriya (Super Eagles a yanzu) a wasan da suka tashi 2-2 a Legas
Gwamnati ta ba da hutu saboda wasan da suka buga daga baya a garin Benin, wanda mutum sama da 25,000 suka je kallon a lokacin Yakin Basasar Najeriya
Ya dawo Najeriya ya buga wasa a karo na uku tsakanin Santos da Racca Rovers na Najeriya a Filin Wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna, a 26 ga Afrilu, 1978.
Bayan wasan Gwamnan Tsohuwar Jihar Filato, Air Commodore Dan Suleiman, ya yi masa ado da Babbar Riga da hula Zanna Bukar
Yana sanya riga mai lamba 10, lambar da babban abokin hamayyarsa, Diego Maradona na Ajentina ke goyawa; Magajin Maradona a Ajentina, Lionel Messi, ma lambar da yake goyawa ke nan.
A lokacin da yake Santos ya lashe gasanni 10; sau shida suna cin kofin Campeonato Brasileiro Série A, sai Copa Libertadores guda biyu, da kuma Intercontinental Cup sau biyu.
Ya yi wasa gasar Kulob din kasar Amurka da zummar tallata wasan tamola.
Sarauniya Ingila Elizabeth II ta karrama shi da lambar girma ta NBE