✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa ba su tafiya yadda ya kamata a Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci shugabannin addinai su kara hada kansu, sannan su tsawatar cikin hudubobinsu game da illar tashe-tashen…

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bukaci shugabannin addinai su kara hada kansu, sannan su tsawatar cikin hudubobinsu game da illar tashe-tashen hankula a tsakanin al’umma, musamman kafin da kuma bayan zaben 2019 da ke tafe. 

Sarkin Musulmin ya ce lokaci ya yi da ya kamata ’yan Najeriya su daina yaudarar kansu game da matsalolin kasar nan, a nemi hanyyoyin gyara kawai. Haka kuma ya shawarci ’yan siyasa su daina yakar junansu game da batun sauya-sheka daga wata jam’iyya zuwa wata “Siyasa ra’ayi ne, kamar dai addini. Don haka ya kamata mu daina fada da juna kan bambancin siyasa ko sauya-sheka,” inji shi.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne a yayin da yake karbar  shugabannin cocin darikar Katolika a fadarsa da ke Sakkwato yayin wata ziyara da suka kai masa a ranar Litinin da ta gabata.

“Ya kamata mu gaya wa kanmu gaskiya sannan mu fadi gaskiya. Abubuwa ba su tafiya yadda suka kamata a Najeriya. Don haka mu daina fakewa a bayan addini ko kabila ko bangare. Na yi imanin cewa muna da matsaloli a Najeriya, kuma mun sansu, to mu daina yaudarar kanmu,” inji shi.

“Babu rigima a tsakanin Musulunci da Kiristanci, sai dai sabanin fahimta a tsakanin Musulmi da Kirista. Don haka ya kamata mu yi kokarin fid da tsattsauran ra’ayi a zukatanmu. Kodayake abu ne mai wuya ka iya tantance batagari a cikin al’umma a lokaci guda, amma kuma wajibi ne mu ci gaba da kokari don tabbatar da samuwar kasa mai cike da lumana da kwanciyar hankali,” inji shi.

Ya kara da cewa: “Babu wata matsala da ba ta da magani a duniya sai dai idan mu ne ba mu son gaskiya. Idan ba haka ba, ya kamata a ce mun kawo karshen wadannan matsaloli tuntuni. Wajibi ne mu ilimantar da mabiyanmu su kara gane cewa baya ga wadannan matsaloli fa dukanmu daga Allah Madaukaki guda daya muke, amma kowa ya dauki hanyar da ya ga ta fi dacewar ya bauta wa Ubangijin a mahangarsa.”

Game da zabubbukan 2019 kuma, ya gargadi ’yan siyasa su nisanci yin amfani da kananan yara da talakawa wajen ta-da- zaune-tsaye. Sannan ya ja kunnen masu kashe mutane haka siddan da sunan addini, yana mai cewa “Wadansu mutane sun jahilci ma’anar jihadi. Ba za ka kashe wani sannan ka yi da’awar aikin Allah kake yi ba. Mai wannan duk yaudarar kansa kawai yake yi,” inji shi.

Tun farko a jawabin Shugaban darikar Katolika ta kasa, Bishop Augustine Akubeze, ya yaba wa Sarkin Musulmin bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen dinke sabani da kuma kulla alaka mai kyau a tsakanin mabiya addinai a kasar nan. 

Shi ma Bishop Kadinal Onaiyekan, ya bukaci hadi kan dukan mabiya addinai wajen tabbatar da zaman lafiya da lumana a tsakanin al’ummar kasar nan. Kamar yadda shi ma Babban Jagoran Katolika na Sakkwato, Rabaran Matthew Hassan Kukah, ya jinjina wa Sarkin Musulmi bisa adalcinsa ga dukan addinai da mabiyansu a kasar nan.