Lafiyayyar rayuwa kan sanya mutum ya kasance a cikin farin ciki.
Duk da cewa samun lafiya kan bukaci sauyin abinci ko tsarin rayuwa, akwai abubuwan da lafiyayyun mutane kan yi na daban a kullum.
Ga wasu daga cikinsu:
Motsa jiki
Mutum na bukatar motsa jiki domin samun ingantacciyar lafiya da tsawon kwana.
Bincike da dama sun nuna cewa motsa jiki na minti 30 ya wadatar.
An kuma gano wasu nau’ukan motsa jiki na minti 15 da fa’idarsu ta kai na awa daya.
Shan wadataccen ruwa
Shan isasshen ruwa muhimmin abu ne wurin inganta lafiya.
Ana bukatar mutum ya sha lita biyu zuwa uku na ruwa ko abu mai ruwa-ruwa a kullum.
Hakan na da amfani mai tarin yawa ga
Samun isasshen barci
Mutane masu basira da cikakkiyar lafiya kan yi kokarin samun isasshen barci na kamar awa 8 a kullum.
Isasshen barci na kara kuzari da nishadi tare da kawar da gajiya.
Nau’ukan abinci
Cimaka na da tasiri ga lafiya, shi ya sa lafiyayyun mutane kan yi kokarin cin abinci nau’ukan abinci masu samar wa jiki isassun sinadarai.
Idan da hali sukan ci kayan ganye ko ‘ya’yan itatuwa sau biyu zuwa uku a kowace rana.
Kwanciyar aure
Baya ga biyan bukata ta sha’awa, yin jima’i na kara lafiyar dan Adam.
Yana debe gajiya, yaye damuwa tare da sanya jin dadi da kara dankon kauna.
Samun lokaci da abokai
Yin abota da lafiyayyun mutane na da dadi matuka.
Bincike ya nuna mutane masu yawan abokai sun fi samun farin ciki da lafiya mai inganci.
Karin ilimi
Wani sirrin samun farin ciki a rayuwa shi ne ilimi.
Kasance a kullum mai neman karin ilimi da koyo da kuma sanin sabbin abubuwa.
Wannan fahimtar za ta saukake maka mu’amala da jama’a.
Tsufa ba ya hana neman ilimi.