✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abubuwa 5 game da sabon Shugaban PDP, Damagum

Kafin nadin nasa, Damagum ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa shiyyar Arewa.

A wannaan Talatar Kwamitin Zartaswa na jam’iyyar PDP na kasa, ya bayyana Iliya Umar Damagum a matsayin shugaban rikon kwarya na kasa.

Debo Ologunagba, kakakin jam’iyyar PDP ne, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja.

Nadin ya biyo bayan umarnin da wata Babbar Kotu ta yi na haramta wa Ayu bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa.

Ga wadansu abubuwa biyar day a kamata a sani game da sabon shugaban jam’iyyar PDP na rikon kwarya na kasa:

1. An haife shi a ranar 10 ga watan Agusta 1963 a garin Damagum, wanda a yanzu ya zama Karamar Hukumar Fune a Jihar Yobe.

2. Ya yi makaranatar Firamare ta Damagum daga 1971 zuwa 1977. Daga nana ya zarce Kwalejin Gwamnati ta Maiduguri, inda ya yi karatunsa na sakandare daga 1977 zuwa 1982.

Ya kammala digirinsa na farko a Jami’ar Maiduguri a fannin Ilimin Tsangaya a 1988. A shekarar 2003 zuwa 2004 ya yi digirinsa na biyu a fannin harkar kasuwanci a Jami’ar ta Maiduguri.

3. Kafin nadin nasa, Damagum ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa shiyyar Arewa.

4. Ya kasance jakadan Najeriya a Romania daga 2004 zuwa 2007.

5. A 2019, ya yi takarar gwamna a Jihar Yobe a karkashin jam’iyyar PDP, amma ya sha kaye a hannun Mai Mala Buni na jam’iyyar APC.