✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abubuwa 5 da za su sa budurwa ta so ka

Abubuwan da ’yan mata ke kaunar samu daga masoyansu

A yau Aminiya ta karkata ne zuwa ga ’yan mata da masoyansu da irin abubuwan da suka fi so domin dorewar soyayya a tsakaninsu.

’Yan mata da muka zanta da su sun bayyana abubuwan da ke sa su karkata tare da samun nutsuwa da masoyansu maza.

Ga biyar daga cikin abubuwan da ’yan matan suka fi kaunar su samu, wadanda idan namiji ya yi musu, son shi kan shiga har ya mamaye zukatansu:

  1. Kulawa:

’Yan matan da Aminiya ta zanta da su sun bayyana cewa suna matukar kaunar su ga namiji yana nuna ya damu da su a aikace kuma a kowane lokaci. Wannan kuma ya hada kuma da kyautatawa.

Aisha Abdulkarim ta ce zuciya na kaunar mai kyautata mata don haka kyautatawa na daya daga cikin muhimman abubuwan da take bukatar ta samu daga mutumin da take so.

“Ina so koyaushe ya zama yana kyautata min saboda hakan yana kara dankon soyyaya,” inji Aisha.

Zara Idris, ta ce, “ina son namiji ya rika kyautata min saboda ni ma ina kyautata mishi. Ai kama tudinu tudan,” inji ta

  1. Ba da lokaci:

Budurwa na son ta ga masoyinta yana ba ta lokacinsa ta hanyar tuntubar ta domin sanin halin da take ciki.

A cewar Dausiya Umar tana son gan masoyinsa wajen kasancewa tare da ita kuma sauraronta a-kai-a-kai na daga cikin abubuwan da take kauna sosai.

Dausiya ta ce babu abu mafi muni a wurinta irin ta ga ba ta samun lokacin daga masoyinta, abin kaunarta.

  1. Sauraro:

Suna kuma son namiji ya rika sauraron su da sauraron damuwarsu sannan ya ba su shawara ko taya su da addu’a game da halin da suka tsinci kansu a ciki.

Fatima Abubakar na cikin masu son hakan daga wurin mosayinta, ta ce tana son mutumin da za ta iya dogaro da shi a koyaushe musamman idan tana da bukatar shawarwari ko samun kwarin gwiwa.

Ta ce abin da take so shi ne, ya zama wanda in ta bayyana masa damuwanta zai saurare ta da kyau kuma ya ba ta kyakkyawar mafita.

Sakin hannu:

’Yan magana kan ce yaba kyauta tukwici, Hafsat Salis ta ce tana son masoyinta ya kasance mai kyauta da sakin hannu.

Hafsa ta ce, ita a wurinta kyauta ba ta kadan kuma duk kyautar da aka yi mata tana matukar faranta mata rai da kara martabar wanda ya yi mata ita.

Matashiyar ta ce kyauta na kuma kara dankon soyayya, “inda a yawancin lokuta za ka ji kana shaukin ganin masoyinka kana kuma kewar sa kana tuna shi ta hanyar kyaututtukansa da ke tare da kai.”

  1. Yabawa:

Amina Ibrahim ta ce tana son masoyinta ya kasance mai yaba alheri da  da kuma komai da ya shafe ta a koyaushe.

Ta ce masoyinta ya kasance mai godiya da kuma yabawa da kananan abubuwan da take yi, baya ga manyan yana da muhimmanci a gare ta.

Kadan daga cikin abubuwan da ’yan mata ke bukata ke nan daga masoyansu domin soyayya mai armashi.

To samari, kun ji daga bakin masu ita, da fatan za ku dabbaka wadannan abubawan ga masoyanku.