A farkon watan Almuharram ne fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, kuma jigo a Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya cika shekara 98 a duniya.
Baya ga tarin iliminsa da yawan shekaru, akwai wasu tarin baiwa da Allah Ya ba malamin, wadanda ba kowa ne ya san da su ba.
Aminiya ta yi nazari a kansu, inda ta zakulo muku abubuwa 18 da ya kamata ku sani a kansa.
Ga wasu daga ciki:
- Ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a duniya, inda yake da ’ya’ya da jikoki da tataba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani mai girma
- Kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, ya ba shi shaidar girmamawa saboda yawan zuri’a mahaddata
- Yana da ’ya’ya 95
- Yana da jikoki 406
- Yana da tattaba-kunne 100
- ’Ya’yansa mahaddata Alkur’ani 77
- Jikokinsa mahaddata Alkur’ani 199
- Tattaba-kunnensa mahaddata Alkur’ani 12
- Shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da fatawa a addinin Musulunci a Najeriya
- An haife shi a watan Janairun 1927, wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira
- A ranar Laraba aka haife shi a a garin Nafada da ke Jihar Gombe a yanzu
- Kwararre ne a fannin Alkur’ani da Tafsiri da Ma’arifa da Hadisi da Harshen Larabci da Li’irabi da Fikihu
- Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ta ba shi Digirin girmamawa
- Gwamnatin Najeriya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa ta OFR
- Ya musuluntar da dubban mutane
- Yakan yi saukar Alkur’ani duk bayan kwana biyu
- Mutane fiye da 140,924 suka haddace Alkur’ani a makarantunsa da ke fadin Najeriya
- Ya kafa makarantun haddar Alkur’ani sama da 1,500 a Najeriya da wasu kasashen Afirka
- Karkashin gidauniyasa, an gina dakunan karatu guda 133,060 a Arewacin Najeriya
- Ya shafe shekaru sama da 50 yana gabatar da tafsirin Alkur’ani a cikin watan Ramadan