✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abokan hulxa miliyan 8 ne suka rungumi bagiren aika sakonni – Hukumar NCC

Hukumar Kula Da Al’amuran Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce tsarinta na samar da bagiren aika sakonni domin wayar da kan abokan hulxar kamfanonin sadarwa…

Hukumar Kula Da Al’amuran Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce tsarinta na samar da bagiren aika sakonni domin wayar da kan abokan hulxar kamfanonin sadarwa yana samun nasara, kasancewar ya zuwa yanzu mutane miliyan 8 ne suka aika sakonnin nuna bakataunsu na kin jinin sakonnin ba gaira ba dalili. Wanda hakan ya karu matuka daga mutane miliyan xaya da aka samu a Disambar 2016.

Daraktan Hulxa da Jama’a na Hukumar NCC, Mista Tony Ojobo ne ya bayyana haka a garin Obollo Afor na karamar Hukumar Udenu, Jihar Inugu a yayin gabatar da taron masu ruwa da tsaki karo na 35.

Ya ce a sakamakon wannan tsari, an samu mutane da yawa da suka bayyana bukatunsu tare da bayyana ra’ayoyinsu dangane da tsare-tsare daban-daban da kamfanonin sadarwa suke samarwa ga abokan hulxarsu a kasar nan.

“Hukumar NCC tana gudanar da muhimman ayyuka a matsayinta na cibiyar gwamnati da ke biyan bukatun abokan hulxar kamfanonin sadarwa, ta hanyar kai masu ziyara har wuraren da suke, da nufin shaidawa da tantance irin abubuwan da suke bukata daga kamfanonin na sadarwa. Irin waxannan ayyuka, hukumar na gudanar da su ne da nufin ingantawa da samar da gamsarwa da inganta masana’atar sadarwa ta Najeriya,” inji shi.