Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya jadadda kwarin guiwarsa na lashe zaben 2023 da ke tafe.
Kazalika, Tinubu ya yi wa abokan hamayyarsa shagube, inda ya ce ba abin da suka iya face cin ‘zarafi’ da ‘zagi’.
- An gurfanar da likitocin bogi 2 a gaban kotun Legas
- Kirsimeti: Hare-haren IPOB sun hana ’yan kabilar Ibo tafiye-tafiyen karshen shekara
“Ba su da wani tarihi da suka kafa, ba su san makamar aiki ba, ba su da nagarta ba abin da suka iya face cin mutunci da zagi. Damuwata ita ce ci gaban Najeriya, kuma shi ne abin da zan sa a gaba,” a cewarsa.
Dan takarar na APC, ya bayyana haka ne a Kalaba, babban birnin Jihar Kuros Riba, a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar ranar Talata.
Tinubu, ya kafa misali da irin nasarorin da ya samu wajen ciyar da Jihar Legas gaba lokacin da yake Gwamna daga 1999 zuwa 2007.
Ya kara da cewar dole da akwai wata gaba da aka taba wa ‘yan Najeriya, amma a cewarsa lokaci ya yi da za a kafa sabon tarihi a kasar nan.
“Laifinmu ne na rashin ciyar da Najeriya gaba tsawon shekara 60, amma yanzu aiki ne gagarumi a gabanmu da ya kamata a yi shi,” a dan takarar.
Tinubu ya kuma sasanta tsakanin dan takarar Gwamnan APC a jihar, Sanata Bassey Out da Sanata John Enoh, wanda suka dauki tsawon lokaci bas a jituwa.
Gwamnan jihar, Ben Ayade, ya ce Allah ne ya kawo Tinubu a daidai lokacin da ya dace don sauya tarihin siyasar kasar nan.
Ya bukaci Tinubu da ya mayar da hankali kan harkar noma da ci gaban al’umma don saukaka wahala da yunwar da ake fama da ita a kasar nan.