✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abiodun Oyebanji: Abubuwa 5 game da zababben Gwamnan Ekiti

INEC ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Abiodun Obayemi Oyebanji a matsayin zababben Gwamnan Jihar Ekiti.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ayyana dan takarar jam’iyyar APC, Abiodun Obayemi Oyebanji a matsayin zababben Gwamnan Jihar Ekiti.

Da yake bayyana sakamakon zaben da aka gudanar ranar Asabar, Babban Malamin Zaben, Farfesa Ayode Oyebode Adebowale, ya sanar cewa Oyebanji ya samu jimillar kuri’u 187,057.

Ya ce Oyebanji ya cika duk wasu sharuda da doka ta tanada, saboda haka ya zama zakara a zaben.

“…a matsayina na Babban Malamin Zabe a wannan Zabe na Gwamnan Jihar Ekiti na 2022 da aka gudanar ranar 18 ga watan Yunin 2022, ina tabbatar da cewa… kasancewarsa ya cika dukkan sharuddan da Doka ta tanada, Abiodun Obayemi na jam’iyyar APC ne ya lashe wannan zabe.”

Ga wasu abubuwa biyar game da zababben gwamnan:

Haihuwarsa

Biodun Abayomi Oyebanji wanda kuma aka sani da BOA, dan siyasa ne na jam’iyyar APC. An haife shi a ranar 21 ga watan Disamba, 1967 a Karamar Hukumar Ikogisi-Ekiti da ke Jihar Ekiti. Yana da shekaru 54 yanzu haka a duniya.

Karatunsa

A shekarar 1992 ya kammala digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Jihar Ondo da a yanzu ta zama Jami’ar Jihar Ekiti, Ado-Ekiti.

Biodun Abayomi Oyebanji

Ya samu shaidar digiri na biyu daga Jami’ar Ibadan da ke Oyo a fannin Kimiyyar Siyasa mai hade da kwarewa a Hukunce-Hukunce Kasa da Kasa da Nazarin Dabaru.

Aikinsa

Oyebanji ya fara aiki ne a matsayin malami a Sashen Kimiyyar Siyasa na Jami’ar Ado-Ekiti, inda ya yi aiki na tsawon shekaru hudu daga 1993 zuwa 1997. Daga baya ya yi aiki a matsayin Manaja mai kula da Ma’adanai da Harkokin Kudi na tsohon Bankin Omega wanda a yanzu ya koma Bankin Heritage har zuwa watan Mayun 1999.

Mukaminsa

Gabanin lokaci da ya yanke shawarar tsayawa takarar gwamna, Oyebanji ne Sakataren Gwamnatin Jihar Ekiti a karkashin Gwamna mai ci, Kayode Fayemi.

Iyalinsa

Oyebanji yana auren wata mata wadda ta fito daga gidan sarauta. Babbar Malama ce a Jami’ar Ibadan da ke daf da zama Farfesa.

Aminiya ta ruwaito cewa, Segun Oni, dan takarar jam’iyyar SDP ne ya zo na biyu a zaben da kuri’a 82,211 amma bai samu ko da karamar hukuma daya ba.

Mista Oni, wanda ya taba zama a kujerar gwamnan Jihar ta Ekiti, yana gaban dan takarar jam’iyyar PDP, Bisi Kolawole, wanda ya samu kuri’a 67,457.

A ranar Asabar ce aka gudanar da zaben gwamna a Jihar Ekiti, inda kafin wayewar gari ranar Lahadi, INEC ta sanar da dan takarar jam’iyyar APC, Abiodun Oyebanji a matsayin zakara bayan ya kayar da sauran ’yan takara 15 da jimillar kuri’u 187,057 da ya samu.