Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce ba zai iya ba Shugaba Buhari shawara ba kan abin da zai yi ya ciyar da gwamnatinsa gaba.
A hirarsa da BBC Hausa kan bikin cikar Najeriya shekara 60 da samun ’yancin kai, Sule Lamido ya ce duk da dimbin kalubalen da ake fuskantar kasar, Najeriya ta samu cigaba a bangarori da dama.
- Ba na goyon bayan dakatar da Jonathan – Sule Lamido
- Abinda ya sa aka shirya min tuggu cewa na saci kudi – Sule Lamido
Ya ce, “Ba zai yiwu ka ce babu cigaba a cikin wadannan shekaru 60 din ba, tabbas akwai.
“Amma maganar gaskiya shugabanninmu ba sa yin amfani da albarkatun da Allah Ya ba mu a kasar wajen inganta rayuwar al’umma,” inji shi.
Tsohon gwamnan ya kuma ce ba yadda za a yi ya yi addu’a ko ya bayar da shawara ga mutumin da ya kira shi da barawo bayan ya raba shi da mulki.
Sule Lamido ya ce zabin ’yan Najeriya ne su kyale jam’iyyar APC ta ci gaba da mulki ko su sauya.
Ya ce, “Ni dan jam’iyyar adawa ne, amma duk yadda na kai ga son Buhari ko gwamnatinsa, babu yadda za a yin a shiga masallaci na yi masa addu’a.
“Mutane sun ce mu ’yan PDP barayi ne suka kuma zabi APC, saboda haka yanzu ya rage nasu su yi alkalanci.
“In Buhari yana yin abin da ya dace to ga shi nan su kyale shi ya ci gaba da mulkin Najeriya har illa masha Allah.
“Amma idan kuma ba ya yin abin da ya kamata, to muna gefe mu dawo mu karba daga hannunsa”, inji Sule Lamido.