✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin mamaki

Abin mamaki Wani Bafulatani ne ya hau babbar mota, suna cikin tafiya sai wata karamar mota ta wuce a guje, sai ya ce: “Kai, wannan…

Abin mamaki

Wani Bafulatani ne ya hau babbar mota, suna cikin tafiya sai wata karamar mota ta wuce a guje, sai ya ce: “Kai, wannan ’yar karama da ita take gudu haka, idan ta girma sai ta fi uwarta bala’i.”
Daga Mubarak Katsina, 08125383130

Bahadeje da amala

Wani Bahadeje ne aka ba tuwon amala da miyar kubewa, ko da ya debi lomar farko ya saka a baki sai ta sulbe, bai tauna ba ta fada sulub a cikinsa; shi ne ya tashi yana duba aljihunsa, yana tunanin ko nan ta fada.
Daga Halliru Barau dankawu, UDU, Sakkwato.

kaikayi…

Buba da Ilu Hadejawa ne abokan juna amma suka nemi aure tare. Sai Buba ya auri matar, sai Ilu ya daka guba ya kai wa Buba a matsayin maganin Basir. Buba ya amsa, ya aje bai sha ba. Wata rana Ilu ya je gidan Buba, sai ya kawo masa hura. Ilu ya tsaya hankali kwance ya shanye ta, suka kama hira. Sai ya tambayi Buba cewa: “Ka sha maganin nan wanda na ba ka?” Buba ya ce: Ban sha ba amma na zuba maka shi cikin hurar da na kawo maka yanzu.” Nan take Ilu ya barke da kuka, yana fadin cewa: “Buba ka kashe ni, ai guba ce, gubar ka zuba mani cikin hurar da na sha?”
Daga Amiru Isa Bakori, 07068147933

Aljanna sai an mutu

Wata majalisar mai shayi ce ta cika makil da matasa, can sai ga wani mahaukaci ya zo wucewa ta wajen, sai ya tsaya ya kale su ya ce: “Allah Ya sa duk ku mutu.” Sai dukkansu suka yi banza da shi, sai ya wuce ya rabu da su. Washegari mahaukacin nan sai ya zo wucewa ta wurin, ya kara tsayawa ya ce da su: “Allah sa duk ku shiga aljanna.” Sai dukkansu suka amsa da “Amin, amin.” Sai ya ce da su: “Mahaukatan banza, mahaukatan wofi, kun taba ganin an shiga aljanna ba a mutu ba?
Daga mai lamba 07031012292