✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da zan yi a matsayin Jakadan Laliga —Ali Nuhu

Za mu rika yin abubuwa na tabbatar wa masoyan gasar Laliga cewa an ta da su

Fitaccen jarumin, kuma darakta a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu ya bayyana cewa zai yi amfani da matsayinsa na Jakadan Gasar Laliga wajen kara yada gasar a Arewacin Najeriya. 

Aminiya ta ruwaito gasar LaLiga ta Spain ta nada Ali Nuhu a matsayin Jakadan gasar a taron masoyanta wanda ya gudana a Kano, tare da hadin gwiwar gidan radiyon Arewa Radio a Kano.

Da yake yi wa Aminiya karin bayani game da ayyukan da zai rika gudanarwa a matsayinsa na jakadan, Ali Nuhu ya ce, “Dama ni masoyin kwallon kafa ne. Ina son kwallon kafa sosai. Muna da alaka da kwallon kafa kuma ina ma da kungiyar horar da ’yan wasa ta FKD Academy”.

A game da ayyukan da zai rika yi a matsayinsa na Jakadan, Ali Nuhu cewa ya yi, “Abin da yake faruwa shi ne akwai masoya gasar Laliga da kungiyoyin Laliga da yawa musamman a Arewacin Najeriya.

“Amma kuma ka san su masoya sukan so a rika nuna musu cewa an san da su, hakan zai sa su gane cewa ana tare da su, kuma an da zamansu.

“Wannan din ne a matsayina na wanda zai zama tsani tsakanin masoyan na nan da gasar, za mu rika shirya wasu tarurruka wanda ni kaina zan kasance a wajen, inda za mu rika tattaunawa  a kan abubuwan da suka shafi gasar ta Laliga. Wannan shi ne abu na farko.

“Abu na biyu kuma, shi ne ka san akwai wasu wasanni na gasar wadanda suka fi zafi a shekara. Za mu rika shiryawa ta yadda za a rika kallon wasannin tare, a rika tattaunawa a lokacin kallon wasannin. Wannan yana cikin hanyoyin da za mu bi wajen kara yada gasar, sannan su kuma fans din su gane cewa an san da su, kuma ana ganin kokarinsu.

“Sannan za mu kirkiri wani abu, yadda kamar yadda akwai masoya irinsu Barcelo da Real Madrid da suka fi yawan masoya, da ma sauran irinsu Villareal da Real Betis da sauransu da ba su kai irin Barcelona da Real Madrid din girma ba.

“Za mu rika sanya su cikin wasu tsare-tsare, inda har kyaututtuka za su samu. Hakan shi ma zai sa su san cewa lallai gasar Laliga din da suke so, kuma suke bi ta san da su tun da ga shi har wani abu suka samu daga ita”, inji Ali Nuhu.