Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya (NEF), ta ce ’yan Arewa za su yi la’akari da cancanta wajen jefa wa dan takarar kujerar shugaban kasa kuri’unsu a zaben 2023.
A yayin da Kungiyar ke bayyana takaicinta dangane da yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaza cika alkawarin da ya dauka na tabbatar da tsaro da kuma bunkasa tattalin arziki, ta shawarci ’yan Arewa da su zabi cancanta a zaben na badi a maimakon su yi la’akari da yankin da suka fito.
- Allah Ya yi wa tsohon shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita rasuwa
- Harin bam ya raunata Kakakin gwamnatin Somaliya
Mai magana da yawun kungiyar, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana hakan a yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Asabar a Kaduna.
Kungiyar NEF ta ce ya kamata takarar shugaban kasa ta kasance budaddiya ga kowanne yanki a madadin takaice ta kadai ka Kudancin kasar kamar yadda Kungiyar Dattawan Kudu da Tsakiyar Najeriya (SMBLF) suka bukata kwanan nan a Abuja.
A kan haka ne Dokta Hakeem yake cewa, tsarin dimokuradiyyar kasar ba zai wadatar da ra’ayin yankin Kudu kadai ba, la’akari da cewa Kundin Tsarin mulkin kasar ya bai wa kowane dan Najeriya da ya cancanta tsayawa takara da kuma jefa kuri’a a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
“Kowane dan Najeriya zai iya tsayawa takara matukar jam’iyyarsa shi ta tsayar a matsayin zakara a zaben fidda-gwani, haka kuma ’yan Najeriya ke da alhakin zaben wanda suke da ra’ayin ya jagorance su.
“Dan Arewa da dan Kudu duk sun da ’yanci iri daya na tsayawa takara, sai dai muna kiran yan Arewa da su yi taka-tsan-tsan wajen jefa kuriunsu a zaben 2023.
“Mu abin da kawai ya dame mu shi ne shugaban kasar ya kasance dan Najeriya, idan daga Arewa ya fito ko sabanin haka, mu dai kawai za mu zabi wanda yake da cancanta fiye da sauran ’yan takarar.”
Ya bukaci ’yan Arewa da su zabi sahihan ’yan takara ba tare da la’akari da kabila, ko addini ko kuma jinsinsu ba a zaben da ke tafe.