✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ’yan Najeriya ke bukata daga Sabbin Hafsoshin Tsaro

Abubuwan da ya kamata manyan Hafsoshin Tsaro su ba wa muhimmanci

’Yan Najeriya sun bayyana abun da suka bukata da sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron da Shugaba Buhari ya nada.

A zantawar Aminiya da Ba Jiddah, wani mazaunin Maiduguri a Jihar Borno ya bukaci sabbain hafsoshin s su da su sauya fasalin tsaron Najeriya.

“Sabbin Manyan Hafsoshin Tsaron na buaktar yin muhimman sauye-sauye a salon yaki da ta’addanci.

“Matsalar tsaro ta addabi kusan dukkannin sassan kasar nan kuma magance ta bukatar sabbin jini,” inji shi.

A Kano kuma, Abubakar Kato, ya ce: “Rashin maganar Shugaba Buhari kan sauya fasalin tsaro duk da karuwar matsalar tsaro na tsawon lokaci ya dami yawancin ’yan kasa na gari.

“Gwamnoni, ’yan Majalisar Tarayya, da iyayen kasa duk sun yi wadannan kiraye-kiraye; sallamar tsoffin Hafsoshin Sojin ya kawo sauki ga ’yan Najeriya da ke son ganin an kawo karshen matsalar tsaron a kasar.

“Tabbas zai kara wa sojoji kwarin gwiwar bullo da sabbin dabarun yakar ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga da sauran manyan laifuka.”

Wani mai zane-zanen zamani, Tukur Kwairanga a Kaduna, ya ce, “Ya kamata sabbin hafsoshin su dauki darasi daga kurakuran magabatansu wurin magance matsalar tsaro a kasar.

Shi kuma wani kwararren mai ba da shawarwari, Mustapha Ibrahim, ya ce, “A karshe dai gwamnati ta amsa kira, bayan an jima ana kiran ta da ta sauya hafsoshin tsaron.”

Ya yi kira ga sabbin da aka nada da su yi duk abin da za su iya ta hanyar kirkira da sabbin dabarun soji wajen magance ta’addanci da sauran laifukan da ake aikatawa da makamai a Najeriya.

Misis Bridget Samuel karamar ’yar kasuwa ce, ta bayyana nadin sabbin manyan hafsoshin taron a matsayin alamar abubuwa za su daidaita.

“Ina ganin Allah Zai bude mana sabon babi ne da nadin sabbin hafsoshin da tun tuni ya kamata a yi hakan.

“’Yan Najeriya sun bukaci a sallame su; kuma kamata ma ya yi su ajiye aiki, amma tunda ga yadda kasar da mutanen cikinta suke, sai suka ki.”

A cewar mai sharhi a kafafen sa da zumunta da ke zaune a garin Fatakwal, Jihar Ribas, Wenenda Wali, Najeriya na bukatar ta fayyace mene ne matsalolintsa na tsaro sannan ta fara magance su cikin hikima.

Shi ma dattijo Bright Ogbomudi da ke Fatakwal, cewa ya yi, Shugaba Buhari ya yi abin da ya dace da ya saurari kiraye-kirayen ’yan Najeriya, kuma nadin sabbin hafsoshin tsaron abin a yaba ne.

Saleh Hayatu, Malami a Jami’ar Jos ya ce, “Ina kyautata zaton abubuwa za su gyaru. Manyan Hafsoshin da aka sallama sun dade kuma sai fama muke ta yi da kalubalen tsaro.

“Ina rokon ’yan Najeriya da su yi hakuri tare da bayar da cikakken hadin kai ga hukumomin tsaron kasar nan,” inji malamin.

Sai dai Dokta Plangsat Bitrus Dayel, wanda shi ma malami ne a Jami’ar ta Jos ya ce, “A ra’ayina babu wani sauyin a-zo-a-gani da za su kawo. Amma idan har gwamnati da ’yan siyasa sun mayar da hankali to tabbas za a ga canji.”

“A yadda ake fama da matsalar tsaro a kasar nan, ina ganin za su fi magabatansu tabukawa kuma za su bar kyakkyawan tarihi a zukatan ’yan Najeiya,” inji Anigege Mutiu da ke Yaba a Jihar Legas.

Wani mazaunin Legas, Ismail Aniemu, ya ce sabbin hafsoshin na bukatar sauya dabarun yakin da suka gada sannan su hanzarta mara wa ’yan sanda baya wurin yakar ’yan bindiga, ta’adanci da sauran kalubalen tsaro.

“Su nuna kwarewa da kuma tabbatar da cewa babu ruwan sojoji da harkar siyasa.

“Sannan su dage wajen dawo da martabar sojojin Najeriya da irin nasarorin da suka samu a ayyukan da suka yi na wanzar da zaman lafiya a kasashen Yammacin Afirka (ECOMOG).

“Rundunar Sojin Ruwa kuma na bukatar yin azama wajen magance karuwar matsalar fashi a teku da satar danyen mai a kan ruwan Najeriya da ya dawo a baya-bayan nan.

“A karfafa hadin gwiwa tsakanin Sojin Sama da Sojin Ruwa tare da yin sintiri da jiragen sama a kan ruwan Najeriya domin dakile ayyukan miyagu,” inji shi.

A Abeokuta kuma, Segun Dada, ya ce: “Ina fatan ba za su bata lokaci ba wurin shawo kan matsalolin tsaron.”

Daga Sagir Kano Saleh da wakilanmu: Olatunji Omirin (Maiduguri), Maryam Ahmadu-Suka (Kaduna), Victor Edozie (Fatakwal), Ado Abubakar Musa (Jos) dsa Abbas Dalibi (Legas).

%d bloggers like this: