✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ’yan bindigar Zamfara suka fada min —Sheikh Gumi

Malamin ya bukaci a yi wa ’yan bindiga shirin afuwa irin na Neja Delta.

Shahararren Malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya ce manyan kwamandojin ’yan bindiga sun shaida masa cewa zaman lafiya ba zai wanzu ba har sai ’Yan Sakai sun daina kashe Fulani a Jihar Zamfara.

Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake gana wa da Gwamna Bello Mohammed Matawalle, game ’yan bindiga a Jihar ta Zamfara.

“Kwamandojin ’yan bindiga sun shaida min cewa sojoji na kai hare-hare cikin daji kuma hakan ya shafi kowane dangi, kuma a cewarsu dole ne a daina.

“Game da wannan akwai ra’ayoyi mabambanta; wasu na ganin bai kamata gwamnati ta yi sulhu da ’yan ta’adda ba, wasu kuma na ganin kawai a murkushe su.

“Abin da muka fahimta shi ne mutanen nan ba su da ilimi ko kadan. Amma in har za a ja hankalinsu to ina ganin za su ba da gari,” a cewar malamin.

Sheikh Gumi ya ce yadda sojoji ke kai hari a kan ’yan bindigar ba zai kawo karshen matsalar ba, amma zama tare da nemo mafita tare da masu ruwa da tsaki shi ne abin da ya dace.

Ya shawarci Gwamna Bello Mohammed Matawalle, kan ya tattauna da su ba tare da wani a shamaki ba, saboda a tunaninsa hakan ne ya kawo rashin fahimta a lokutan baya.

Sannan ya ba da shawarar cewa a fito da tsari ga wadanda suka amince su ajiye makamansu ta yadda za a sama musu abun yi kamar yadda gwamnati ta yi a yankin Neja Delta, don samar da zaman lafiya.