✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sasanta rikicin Shata da Sarkin Birnin Gwari – Yaron Shata dangwamma

daya daga cikin ’yan amshin Shata kuma mai tattara kudin da aka lika yayin wasa, Malam Ibrahim dangwamma yana daya daga cikin yaran da suka…

daya daga cikin ’yan amshin Shata kuma mai tattara kudin da aka lika yayin wasa, Malam Ibrahim dangwamma yana daya daga cikin yaran da suka bi shahararren mawaki, marigayi Alhaji Mamman Shata yana yi masa amshi da tara kudin da aka yi liki. A tattaunawa ta musamman da Aminiya, ya fadi dalilin da ya sa ya bi Shata, yadda zamansu ya kasance, irin shu’umancin Shata da ya gani da rabuwarsu da shi da sauransu:

 
Ya aka yi ka hadu da marigayi Mamman Shata?
Da farko dai sunana Ibrahim dangwamma. Shekaruna sun wuce hamsin. Ni mutumin Dankama ne ta kasar Bakori, a Jihar Katsina. Na yi gadon roko a gidanmu. Saboda kuruciya, ina jin wakar Shata, sai na je gidansa a Funtuwa na same shi. Na ce masa ina son in bi shi, bai tambaye ni labarina ko na gidanmu ba, kawai sai ya sanya mini suna. lokacin ina dan shekara goma sha biyar da haihuwa. Shi kuma bai yi gardama ba, ya ce mu je zuwa, sai muka fita yawon biki.

Wane biki kuka fara fita da shi?
Bikin da muka fara fita da shi, shi ne na gidan Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris. Mun kwana ba a yi waka ba, sannan da gari ya waye aka yi biki da safe. Ya yi wasa sosai, sannan ya yi wakar Sarkin Zazzau. Mun yi yawo da yawa, wasu ba zan iya tunawa ba. Kuma a duk wakar Shata na fi son ta Sarkin Zazzau, Balaraben Sarki.

Mene ne aikinka a cikin yaran Shata, kai dan share fage ne ko me?
Ina cikin ’yan amshin shata, kuma ina tattara kudi in zuba a buhu ni da wani yaro mai suna Shamsu. Muna yin amshi wani lokaci ne kafin wasa ya dauki dumi, don in ya dauki dumi mu kudi muke tarawa da aka yi liki da su.

A wakar Sarkin Zazau yana cewa: “Ruwa aka bai wa doki, ruwa kadan sai dai mai dokin.” Ko kun tambaye shi me yake nufi, watau tunda ya ja baki, ko ya yi muku fassara?
A’a. Ba mu tambaye shi ba, wani bai tambaye shi ba fassarar abin da yake nufi ba. Ya dai yi wakarsa, mu kuma ’yan amshin Shata mun yi amshi.

Wasu suna sharhin cewa ko wasu sun rage sallamar da aka ba su ne su ba Shata, watau ko ya raina sallamar da aka yi masa?
Watakila hakan ne ko kuma sai shi kadai zai iya yin fassarar bakin da ya ja.

Kun yi yawo da shi, ko kuma yana barinka ne a gida, ya tafi da wasu?
Ai ni ina daya daga cikin ’yan gaban goshinsa a zamanmu na shekaru uku cif-cif. Mun yi tafiye-tafiye da shi da yawa. A ciki, mun je gidajen sarakuna da gun ubangidansa watau Sarkin Daura, da sauransu. In mun je gidan Sarkin Daura yana yin gaisuwa ne, mu yi kwana mu wuce; ba kodayaushe yake yin waka ba.

An ce kodayaushe ya je Daura sai ya sa a dauko masa makullin mota sabuwa ba tare da ya nemi izinin Sarkin Daura ba, ya tafi abinsa, ko an yi hakan da kai?
kwarai kuwa, an yi hakan da ni. Mun je ya ce a dauko masa mukullin wannan sabuwar motar, kuma aka dauko masa ya tuka muka tafi.

A lokacin Sarkin Daura Muhammadu Bashar yana gari?
Sarkin Daura yana nan kuma an yi haka ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Domin shi ma Shata ya ja baki ya fasa a cikin wakar Sarkin Daura, inda yake cewa:
“Sarari mai kare gudun doki.
Lafiya zaki Mamman baban Galadima dan Musa.
Fili mai kare gudun doki dan Musa.
Damo dan Mamuda, yana kallo aka kware shi,
Yana kallo aka cuce shi, bai ce komai ba na Mamuda,
Ka ba ni da kanka, uban Baushe,
Na dau sunanka na saida na karbo.”

Me ya sa Sarkin Kano ya ce Shata ya yi waka, ya ki yi, sannan ya gudu?
Mun je gun sarkin, sai Shata ya shiga ya yi gaisuwa. Da ya fito sai ya ce sarki ya ce ya yi waka amma ya ce ba zai yi yau ba, sai ya ce sai gobe. Sarki ya ce to shi ke nan. Da ya fito sai ya gaya mana cewa ga yadda suka yi da sarki, sai muka ce ya yi wasa mana; sai ya ce ba zai yi ba. Gari na wayewa sai ya nade kayansa ya ce mu bi shi. Muka bar garin, bai yi wakar ba. Shata ya ja baki ya yi fassara a nan, inda ya ce: Dalilin kuwa in ji Shata si ne, tun da sarkin ya ce in yi waka ba zan yi ba. Ai ba shi ya sa shi wakar ba. Don haka ba ya yi. Muka ce wa Shata, ranka ya dade ya kamata ka yi wakar. Shi ko ya ce ba zai yi ba, don sarki bai ba shi masauki mai kyau ba, ya je ya kwana a otel a Sabongari, kuma ya yi waka? A’a. Da an ba shi masauki da tun a daren ya fara wasa.

Wane abin shu’umanci Shata ya yi da har gobe yake ba ka mamaki?
Mun fito Kano sai ’yan fashi da makami suka tare mu da dare wajen karfe daya, muna dauke da kudi shake a mota. Sai ya ce me kuke so? Sai suka ce kudi. Sai ya ce ba zai bayar ba. Si suka ce suna son rayuwarsa. Sai ya ce na fi karfinku. Ni kuwa da sauran ’yan amshi duk mun tsorata. Sai Shata ya ce kai bi nan, kai bi can; duk ya tarwatsa su. Muka shiga mota muka wuce.

Me ya sa kuka rabu da Shata bayan shekara uku kacal kuna tare?
Wallahi Allah yawo na fito sai na iso Birnin Gwari, yadda Shata ke cewa dadi ya ji ya zauni gari, haka ni ma na ji dadi na zauni gari. Don na hadu da wani da ya zama ubangidana, dangaladima Alhaji Muhammadu Shuraihu, marigayi. Don yanzu ina da aure da iyali na zama dan gari tun da ina aiki a fannin lafiya na karamar Hukumar  Birnin Gwari.

Me Shata ke ce maka?
Zan gaya maka amma kar a buga a jarida. (Dariya).

Ko kun sake haduwa da Shata?
Mun hadu da ya zo Birnin Gwari, da ya gan ni sai ya ce: “Gudu ka yi ka bar ni?” Sai na ce a’a. “Dadi na ji na zauni gari.”

Mene ne dalilin shari’a tsakanin marigayi Sarkin Birnin Gwari Jibril da Shata?
A kan gona ce. An ce sarki ya ba Shata gona har ya sare bishiyoyi sai aka hada su har suka shiga kotu. Da aka tashi sulhu sai Shata ya ce sai sun yi ido-da-ido da sarki. Da Shata ya zo fada, sai Sarki ya ce ma sa: “Shata Dodo.” Sai Shata ya ce: “Ai kai ne Dodo da kansa.” Ka san gaba da gabanta sai ya ce ya hakura. Sai aka sulhuunta, aka janye rigimar a kotu. Da aka nada Sarki na yanzu, Alhaji Zubairu Jibril, sai Shata ya zo ya yi masa waka amma ni ba zan yi wakar ba sai dai ku nema (Dariya). Ya ce: “Uba ba ya kyauta da ya tada.” Sai Sarki ya ce: “Ai ban tada ba.” Sai Shata ya ce ka tada mana tunda ka hana ni wuri.”

In Shata ya je Birnin Gwari yana zuwa gidanka ya sauka, ko kuma sai dai ku hadu a gun wasa?
Yana zuwa gidana mu yi ta hira muna raha ina tuna mai baya, ya yi ta tsokanata (Dariya). Kuma shi duk abin da ya samu yana ci.

Kana da magaji  a harkar roko?
A’a, ban da magaji kuma ni ma ba na yi, don roko a wannan zamani akwai wulakanci a ciki.

Wane suna Shata ya sanya maka?
Zan gaya ma amma kar a bayyana wa duniya (Dariya). Ina kuma mika ta’aziyyata ga iyalan Mamman Shata dangane da rasuwar Hajiya Huraira Mamman Shata.