Dokta Aliyu Ibrahim Kankara, malami ne a Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma. A kwanakin baya ya fitar da sabon littafin tarihin marigayi Alhaji Mamman Shata, wanda ya sa wa taken SHATA: Mahadi Mai Dogon Zamani. Mun fara tattaunawa da shi a makon jiya, yau kuma ga ci gaba:
Bayan kun kammala rubuta littafin an kaddamar da shi, me ya biyo baya?
Da aka kammala littafi ana ta neman kudin buga shi a madaba’a. Kwaram sai Dokta Aliyu Modibbo Umar ya biya kudin buga kwafi 1000.
An kaddamar da littafin ranar 6/8/2006 a Kaduna. Kafin ranar, sai aka bude wa littafin asusu a Bankin Habib, kuma Ibrahim Sheme da Yusuf Albasu kadai aka amshi sa hannunsu a bankin, su kuma kadai ke da ikon sa hannu su fitar da kudi. Ni da Ali Malami aka ce ban da mu, kuma muka hakura. Amma duk aikin nan da aka yi, na rantse da Allah ko kwabo ban samu ba, na tashi a tutar babu. An kaddamar da littafi amma bisa ga amana, ya dace mu zauna mu hudu mu kasafta dan abin da aka samu, kowa a ba shi koda a hannu ne. Sai ba a yi haka ba, kodayake an samu cikas, ba a samu yadda ake so ba. kusan wadanda aka gayyata ba su samu damar halartar taron ba, ’yan siyasa da kuma manyan gwmnati. Shi ma babban mai kaddamarwa bai ba da Naira miliyan biyu da ya yi alkawari ba. Amma duk da haka, jimillar kudin da aka tara da wadanda aka yi alkawurra kusan Naira miliyan shida da rabi ne.
Shi dai Sheme shi ne shugabana, su kuma su biyu daga Kano sai Tijjani yake wakiltarsu. Kudin da ba a amso ba daga mahalarta taro da suka yi alkawari sai Sheme ya ce ya ranci gudunmawar Sarkin Zazzau ta Naira dubu 200, wadda dama shi aka aiki wadansu fadawa suka kai masa kudin har Abuja. Ganin haka, sai shi ma Albasu da ya amso kudin Badaru Babura (Gwamnan Jigawa na yanzu, Naira dubu 100) ya ranta shi ma. Gudunmawar Alhaji Dahiru Mangal ta Naira dubu 250 nake tababa ko sun amsa ko ba su amsa ba? Tunda na ji shiru ita ma ba a rasa amsarta. Sauran kudin ban san hanyar da suka bi suka amso su ba daga hannun jama’a ba.
A lokacin da aka gama kaddamarwar, kai kana ina?
A lokacin wannan hidima ta tarawa da kasafta kudin ina can Daudawa, wani lungu cikin daji ina koyarwa a makarantar ’yan mata, su kuma abokaina suna Kano da Abuja, inda wadanda za a amshi kudin daga wurinsu suke.
Yanzu ga shi Ibrahim Sheme Ya fitar da sabon littafi, kai ma ka fitar da sabo, me ya kawo haka?
Duk da asarar da na yi na ’yan uwana sun rabe kudin littafi sun manta da ni, ban damu ba, don babana ya ba ni hakuri ya ce ‘ba rabona ba ne, rabon na nan tafe a gaba.’ Na ce su zo a sake buga wani, sai suka ce su sun gaji, idan ni ina da sarari in tafi in ci gaba. Kafin wannan lokaci, mun hadu a magana daya cewa kowannenmu na iya daukar littafin ko wani sashensa ya rubuta wani abu game da Shata a gaba. Na rantse abin da Sheme ya ba da shawara ke nan kuma sauran suka amince, suka yarda. Daga baya sai suka yi mini gardamar maganar don sun ga ba rubutawa muka yi ba, ga kuma wani littafi ina ta kokarin fitarwa. Don sun ga littafin ne ya sa suka canja magana.
Amma dalilan da suka sanya na ware, na hada rundunata ni kadai su ne: Na daya, na sha wahalar Sheme a littafin farko. Bai cika daukar shawara ba, abin da kuma ya ga dama shi yake sanyawa ko yake cirewa koda kuwa mu ba mu so haka ba, alhali an ce tafiya ce ta mutum hudu. Ai don ana so a samu idea ta kowa shi ya sanya aka game. To mene ne amfanin hadewar? A ce cikin mutum hudu, mutum daya shi kadai za a dauki ra’ayinsa dole? Ka ga ko tafiya ta tafi wata rana sai an samu sabani. Duk labarin da na kawo masa sai ya tace ya zubar da fiye da rabi, sannan ya sanya sauran. Bangaren tarihin Shata da ya fi gardi da gishiri da nuna, sai na ga Sheme ba ya son nan wajen. Alhali abubuwan da ya zubar su ma masu amfani ne. Mahaifin Shata maharbi ne kuma gagararre, duk hatsabibancinsa Shata ya gaje su. Don haka komai iya yin mutum ba ya raba Shata da wannan hatsabibanci don gadonsa ne, sai dai in ba ya son gaskiya, kamar kwatsam a ga ya bace ko a gan shi cikin fili ba tare da an ga isowarsa wurin ba.
(Idan ana taron aikin gayya ko na maharba, ba a ganin lokacin da mahaifin Shata za ya iso wurin, sai dai a gan shi a tsakiyar fili, to shi ma Shata ya sha sai dai a gan shi a fili ba a ga ta inda ya zo ba). Da mutum ya cire wannan a tarihin Shata to ya bata shi, kuma zancensa ya tashi daga tarihin makadin ya koma wani abu daban. Ka na iya raba mutum da abin da ya gada? An tabbatar Ibrahim Yaro yana bacewa (ba mamaki ba ne saboda maharbi ne) kuma yana iya shiga cikin kukar gidansu ya kwana 2 bai fito ba. Ko kuma in ya shige ta sai a ga ya bulla a cikin tafkin Musawa. Daga gida kuma yana kiran namun daji su zo wajensa. Tsohuwar matar Shata da suka zauna da shi a Musawa ta shaida mini haka. Ta ce an yi abin a gabanta ba sau daya ba, ba sau biyu ba. Yana kuma ba maharba asirin kama dabba. Don na fadi tarihin mutum ai ba aibata shi na yi ba.
Af, ba hatsabibancin suka sanya shi ya yi kiwon kadoji har daga baya Shatan ya gaje su daga hannunsa ba? Tsofaffin da suka ba ni labarin wasunsu na nan da rai. Bangaren hatsabibancin Shata, Sheme babu ruwansa da wannan, ni kuma bangaren da na fi so ke nan. Ya ce wai babu scientific proof. To Sheme ya je Musawa ya nemo tarihin Baba ya sha mamaki. In kuma an yi musun hakan, to a ce kiwon kadojin ma bai yi ba mana.
Dalili na biyu, a bangaren abubuwan da Sheme ke rubutawa a kan Shata, akwai tawaya. Tun a littafin farko, na jawo hankalinsa a kan matattun wakoki da ba su samu gatancin da aka nade su a faya-fayen garmaho da talabijin ba, cewa sun fi rayayyun wakokinsa (wadanda aka dauka a rediyo da talabijin) gardi da azanci da hikima, tunda su ya riga yi, har zuwa tsakiyar shekarun 1960. To duk wakokin Shata dodon hoto ne, ma’ana suna da kanne ko yayye. Wadanda duk ya yi, to wata rana sai ya wanke ta ya yi samfurin wata irinta, amma Sheme bai yarda da wannan ba. Misali, Bakandamiya iri 130 ce a cikin littafina. Shi a wurinsa Bakandamiya ba ta fi iri 10 ba. A nan ma mun sha bamban. Da za a yi wa tarihin Sheme na Shata kwakwaf, za a gane cewa zunzurutun tarihin Shatan da ya sani ba wani abin a zo a gani ba ne.
Dalili na uku, ko an samu kuskure ko gyara, misali, a kan shekaru na faruwar wani abu, Sheme ba za ya gyara ba, ko da mun lurar da shi a kan hakan. Ga hujja amma sai a yi ta gardama da shi. Da na fahmci haka, koda na ga kuskure sai in yi shiru in kyale shi. Misali, a bikin ’Yan Sarki na su Ado Bayero, na ce Disamba 1952 (tunda Galadiman Kano da Walin Kano da Sabo Dogarai da Inuwa Dalibi duk sun tabbatar mini haka) ne aka yi, shi kuma Sheme sai ya tsaya a kan dole 1954 ne wai don ya ji Shatan na cewa ‘… a zamanin Sanusi Mamman.’ Na ce masa ai sannan Sanusi bai kai ga zama Sarki ba, yana Ciroman Kano, amma shi ya yi hidimar bikin, shi ko Shata babu ruwansa, wanda ya ga yana karakaina a biki shi a wurinsa shi ke da zamani. Misali na biyu shi ne, ba Garba Goga ya fara kai Shata Funtuwa ba, don ya fadi haka a waka ba dole ba ne a ce daidai ne, shi ya san abin da yake nufi da kalmar. Bature Makadi Bakori shi ya fara kai Shata Funtuwa cikin Yuli 1943, sannan bai kai ga sanin Goga ba ma. Ba yadda ban yi ba da Sheme ya canja wannan zance amma ya ki. Irin wadannan dalilan suna da yawa.
Yaya makomar sauran mutum biyu daga cikinku wadanda ba su fitar da sabon littafin Shata ba?
Wallahi ban sani ba, tunda wannan sabon littafin da ya fitar ai duk aikin wancan littafin ne na baya namu, da kuma aikina na wannan sabon littafin nawa. To ko na sa ran za ya sayar da littafin namu ya ba ni kasona, ina yaudarar kaina saboda na san ba za ya ba ni ba, ballantana su da gudunmawarsu a littafin ’yar kadan ce.
Msali a nan shi ne, don duniya ta tabbatar da gaskiyata, ran nan Sheme da kansa ya yi wa Albasu waya cewa mu duka hudun mu hadu a Kano don mu tattauna yadda za a kasafta kudin wannan sabon littafin da ya kira nasa amma tare da wai gudunmawarmu. A gaban matata muka yi waya da Albasu, cewa waccan Asabar mu hadu a Kano. Ina gama waya ta ce ta tabbata ba za ya je ba, kuma zan gani. Sai ga shi maganarta ta tabbata. Wallahi bai je ba, sai ran Juma’a, ana gobe za mu hadu Albasu ya sake yiwo mini waya cewa Sheme ya ce wai za su je rangadi daga ofishinsu a wannan Asabar, saboda haka a ba mu hakuri, sai Asabar ta sama. Ka ga tun a nan za ka fahimci cewa ni da sauran marubutan ba mu san makomarmu ba. To, me za ya hana ban balle na kafa rundunata ba?
Mun kammala