✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa za mu bude gidan marayu – kungiyar Masallacin Waff Road

A jibi Lahadi ne kungiyar Masallacin Waff Road da ke Kaduna za ta yi bikin kaddamar da wani sabon gidan marayu a zauren taro na…

A jibi Lahadi ne kungiyar Masallacin Waff Road da ke Kaduna za ta yi bikin kaddamar da wani sabon gidan marayu a zauren taro na Arewa House, Kaduna. A wannan tattaunawar da Aminiya ta yi da Babban Limamin Masallacin Waff Road Malam Muhammad Sani Isah, ya bayyana wasu daga cikin ayyukan kungiyar da kuma abin da ya sa su gina gidan marayun da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:                                                                                         Aminiya: Za mu so mu ji dalilin da ya sa kuka yi tunanin gina gidan marayu?
Abin da ya ja hankalin kungiyar Waff Road Moskue Forum shi ne wannan aikin yana daya daga cikin ayyukan da muke yi tsawon lokaci. Wato muna ziyarar gidajen marayu da gidajen yari don mu kai gudunmuwa kowane wata. Sau hudu muke fita kowane wata. Wannan Lahadin mu kai ziyara gidan marayu, wata Lahadin mu kai gidan yari, wata mu je asibiti da kuma gidajen horan yara. Ilimin da muka samu yau da kullum daga wadannan ayyuka sai ya sa, marayun da muke ganinsu yau da kullum ba haka yakamata su kasance ba, amma masu kokarin mun gode musu. Sai muka ga akwai wasu gyare-gyare da kare-kare da yakamata a yi don inganta zaman maraya a wurin. Kada maraya ya zamana an zaunar da shi ne a ba shi abinci, a ba shi sutura ya sanya.A’a, a gina maraya yadda wanda ma ke da iyaye ba zai fi shi ba. Yadda za a kai mai iyaye makaranta ya samu ingantaccen ilimi. Muna so shi ma maraya ya samu ingantaccen ilimi kamar kowa.
Wannan ya sa muka ga ya dace a gina gidan marayu wanda zai kunshi makaranta da gidansu. Ga bangaren mata, ga bangaren maza. Ke nan a ba su  ilimi, a ba su abinci. A ba su  horo da tarbiyya yadda yamata irin ta addini. Har ila yau, su samu horo irin na sana’ar hannu. Wannan ya sa muka ce bari mu yi namu da kanmu. Mu shigar da wadannan abubuwa da muke so a yi. Saboda muna ganin idan mun kai wa wasu shawara ba za su yi ba. Sun faro kayansu ba dole ne su karba shawarwarinmu ba. Sai muka ga ya dace mu fara wadannan ayyukan don sauran jama’a su koya.
Aminiya: Hakan yana nufin kun daina kai taimako sauran gidajen marayu ke nan?
Madalla, ba za mu ce mun daina kai taimako ba. Amma za mu fi ba da karfi a namu din. So muke ya zama abin koyi da sauran jama’a. Ba za mu ci gaba da taimakon sauran gidajen marayu kamar yadda muka saba ba, saboda za mu kasa samun karfin tafiyar da wannan sabon gidan marayun. Wannan ya sa za mu fi ba da karfi a nan. Amma idan wani abu ya taso na gaggawa, na ceton rai a wasu gidajen marayu, to ba za mu ki taimakawa ba.
Aminiya: Wane lokaci ake fatan bude wannan sabon gidan marayun?
Da farko yana da kyau a fahimci cewa ginan ya yi kusan shekara uku da farawa. Amma idan mun samu yadda muke so lokacin bikin kaddamarwar. Muna fatan bude shi a karshen watan Mayun bana. Kodayake, idan mutum ya je ya ga aikin, akwai saura aiki a gaba kwarai. Kodayake, muna ganin za mu iya cewa mun ci rabin aikin a yanzu. Kuma muna sa ran cewa bayan yin bikin kaddamarwar da neman taimako, muna sa ran abin da za mu samu shi ne za a ci gaba da aikin da shi a cikin watan nan na Maris, ba tare da bata lokaci ba.
Aminiya: Wadannan matakai maraya zai cike kafin ku karbe shi a wannan gida?
Tsarin shi ne za a fitar da takarda wato fom ga marayu masu bukatar zama a wannan gida. Sannan bayan sun cike fom din, sun kawo mana. Za mu bi sahunsu don mu tabbatar da abin da suka rubuta a fom din. Domin mun fahimci cewa a wasu makarantu da suke so su tallafi maraya, sai iyayen su kai sunan ’ya’yansu a matsayin cewa yaran marayu ne. Alhali ba haka ba ne. Shi ya sa  za mu fito da tsare-tsare don kada marayun bogi su toshe wa sahihan marayu damarsu.
Hakazalika, ba mu da wata damuwa kan wurin da  maraya ya fito. Za mu karbi marayu daga kowane wuri, ko daga Jihar Enugu ne. Matukar sun cancanci a kira su marayu. Kodayake, za mu fi karbar marayu Musulmi (’ya’yan Musulmi) a wannan gida. Idan ka dauki wanda ba Musulmi ba, wasu sai su ga kamar za ka tilasta masa shiga addinin Musulunci. Da kuma tsoron kada a taka dokokin kasa. Har ila yau, za mu karbi yara tsintattu wadanda suna da iyaye, amma ba za a iya gane su ba.
Aminiya: Ko za ku amince da wanda ya rasa mahaifiyarsa a matsayin maraya?
A’a, saboda ko a addinin Musulunci maraya shi ne wanda ya kasance ya rasa mahaifinsa, ko duka iyayensa biyu, lokacin da yake yaro gabanin ya kai shekarun balaga. Mu ma ta wannan mahangar ce muke kallon batun maraici.
Aminiya: Ko za ku karbi yara marayu daga dimbin sansanonin ’yan gudun hijira da muke da su sakamakon rikicin ’yan Boko Haram?
Eh, tabbas za mu yi maraba da marayu daga wannan wuri?
Aminiya: Wannan aikin ana fatan ya dore har bayan wadanda suka faro shi. Wane tanadi kuka yi don ganin dorewarsa ko bayan ba ko?
A gaskiya muna da wani shiri na samar da wasu makudan kudi don gidan marayun ya mallaki wasu kadarori da za su rika kawo masa kudin shiga ta hanyar kasuwanci. Ta yadda zai iya rike kansa ko da bayan ba mu.
Har ila yau, makarantar kwanan da za a bude tare da gidan marayun makaranta ce da za ta dauki dalibai daga waje wato dalibai masu iyaye wadanda za a yi amfani da kudin makarantar da za su biya wajen ayyukan gidan marayun da ita kanta makarantar. Muna fatan fara makarantar ne da matakin firamare.
Aminiya: Za mu so mu ji takaitaccen tarihin  kungiyar Waff Road Moskue Forum?
An faro wannan tafiyar ne tun a shekarar 1991. Kuma an yi mata rijista da hukuma ne bayan shekara biyu (wato a shekarar 1993). An yi mata rijistar ne a matsayin kungiyar addini musamman saboda yadda ta samo asali daga masallacin Waff Road. Muna da manyan mutane a matsayin mambobinmu, misali shi wanda ya ba mu filin gina wannan sabon gidan marayun wato Alhaji Ahmadu Chanchangi shi ma mamba ne. Akwai Shugaban Bankin Jaiz, Alhaji Umar Abdul Mutallab, a matsayin shugaban kwamitin amintattu na wannan kungiyar. Shugaban kungiyar shi ne Alhaji Bello Dikku Salihu.
Har ila yau, sauran mambobin kungiyar sun hada da: tsohon Alkalin Alkalai Sheikh Ahmad Lemu da Alhaji Bello Damagum da Malam Kabiru Yusuf da sauransu. A gaskiya ’ya’yan kungiyar suna da dama. Muna taro kowace ranar Lahadin karshen wata. Kuma muna maraba da kowane Musulmi, ba lalle sai manyan mutane ba. kofarmu a bude take ga kowane Musulmi.
Har ila yau, wannan kungiya tana gabatar da wa’azi kowace ranar Asabar tsakanin lokacin sallar Magariba da Isha’i. Muna gayyato malamai ne daga ko’ina. Malamai da dama sun gabatar da wa’azi a wannan wuri kamar marigayi Sheikh Jafar Adam da marigayi Dokta Hadi dahiru Usman Bauchi da Malam Ibrahim Bawa Mai Shinkafa da Sheikh Sharif Saleh da Sheikh Muhammad bn Uthman da sauransu.
Aminiya: Wadanne manyan baki ne kuka gayyata wajen bikin kaddamar da taimakon gina sabon gidan marayun?
Akwai Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar wanda shi ne uban taro. Akwai Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu da Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa’i. Har ila yau, kada in yi tuya in manta da albasa akwai Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ko da bai samu damar zuwa ba, muna da tabbacin zai aiko da wakilinsa. Da kuma sauran manyan baki da dama. Za a fara taron ne da karfe 9:00 na safe, a zauren taro da ke Arewa House jibi lahadi. Kuma muna gayyatar kowa da kowa.