✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa tsofaffin gwamnoni ke son juya akalar gwamnoni masu ci

An mayar da gwamna kamar sarkin sarakuna a siyasar matakin jiha.

Rikicin siyasar bayabaya nan a tsakanin Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa da tsohon Gwamnan Jihar Sanata Danjuma Goje ya sake jefa tambayoyi da tayar da muhawara a tsakanin mutane kan yawan sabanin da ake samu a tsakanin tsofaffin gwamnonin da wadanda suka gaji mulki daga hannunsu.

Kodayake sabanin da ake samu a tsakanin tsofaffin gwamnoni da wadanda suka gaji mulki daga hannunsu ba sabon abu ne ba a kasar nan, amma hakan yana kawo cikas ga ci gaban jiha da kuma mulkin dimokuradiyya, inji masu sharhi.

Ziyarar da tsohon Gwamnan ya kai Jihar Gombe ce ta haddasa rikici, inda dukkan bangarorin biyu suka dora alhakin abin da ya faru a kan daya bangaren.

BBC ya ruwaito cewa, lamarin ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutum biyar, abin da masu sharhin siyasa suka danganta da kokawar neman iko daga bangarorin biyu.

Sai dai Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Gombe Mista Julius Ishaya Lepes, ya zargi Sanata Danjuma Goje da shiga garin ya ta da hankalin al’umma ta hanyar amfani da ’yan Kalare, wanda yin hakan ya saba wa dokar kasa.

A nasa bangaren, Sanata Danjuma Goje, ta bakin mai magana da yawunsa, Lilian Nworie, ya zargi Gwamna Inuwa Yahaya ne da tura ’yan Kalare da kuma mukarraban gwamnati don hana shi shiga cikin garin Gombe, inda suka farfasa masa motoci, suka barnata dukiyar al’umma.

A baya dai an samu wadansu tsofaffin gwamnonin da suka samu sabani da wadanda suka gaje su, lamarin da har ta kai ga matakin ba sa ga maciji.

Wadannan jihohin sun hada da Kano da Kwara da Sakkwato da Zamfara da Kaduna, inda tsofaffin gwamnonin suka raba gari da wadanda suka mika wa mulki.

Sai dai abin mamaki shi ne, yawancin gwamnonin da suke mulki yanzu a baya tsofaffin gwamnonin sun kasance iyayen gidansu a harkar siyasar cikin gida ko ta jiha.

‘An dauki Gwamna tamkar Sarkin Sarakuna’

Wadansu masu sharhi sun ce wannan rikici ba abin mamaki ba ne kuma suna alakanta matsalar a kan wasu abubuwa.

Dokta Tukur Abdulkadir, malami a Sashen Kimiyyar Siyasa a Jami’ar Jihar Kaduna ya ce an mayar da siyasar jiha ta Gwamna, inda wadansu suka dauki Gwamnan a matsayin Sarkin Sarakuna.

A cewarsa, “Gwamna ya mayar da jiha jiharsa ce kawai, gidansa ne, kayansa ne kuma a karshe wanda yake so shi ake bai wa tikitin jam’iyya kuma zai yi wahala ba shi yake cin zabe ba.”

Masanin harkokin siyasar ya ce, “Saboda haka idan dan siyasa ya dauki jiha ta zama gidansa ko masarautarsa zai yi wahala a ce zai iya hakuri idan yaronsa da ya dora a kai ya yi karfa-karfa, ya samu mulki su wanye lafiya saboda abin ba yaki ne na akida ba ko kishin kasa ko kuma burin yi wa jama’a hidima ba.”

Masu sharhi a kan harkokin siyasa sun ce babban burin tsofaffin gwamnonin shi ne su ci gaba da karfa-karfa da babakere a harkar siyasar jihohinsu “Da su da ’ya’yansu da surukansu da kuma wadanda suke shafaffunsu da mai.”

Wadannan abubuwa su ne suke haddasa matsaloli a tsakanin ‘ubangida da yaronsa’ kuma masana sun ce zai yi wuya a daina idan ba a kawo karshen siyasar ubangida a kasar nan ba.

Mummunan sakamako

Masu sharhi sun bayar da misali da Jihar Borno duk da yake Kashim Shettima ne ubangidan Gwamna Babagana Umara Zulum, amma kusan a fili a iya cewa ya kawar da kansa daga sha’anin mulkin jihar tun da ya sauka.

Amma a lokuta da dama bambance-bambancen da ake samu a tsakanin ubangida da yaronsa a harkar siyasar jiha kan rikide zuwa tashin hankali, abin da kan janyo asasar dukiyoyi da rayuka.

Dokta Tukur Abdulkadir ya ce: “Idan ana yin abin don Allah, idan wanda ka goya masa baya ya bijire maka, to, shi ma abin da ya yi maka, za a zo a yi masa.”

Mafita

Masana siyasa dai na ganin mafita ga wannan matsala ita ce a tsaftace hanyar da ake bi wajen fitar da ’yan takara, musamman a harkar siyasar jiha, domin hakan ne zai sa a iya dawo da martabar siyasar cikin gida.

Kodayake sun ce sai an yi da gaske idan ana son a samu ci gaba.

“Matukar ’yan siyasa masu mulki ba su dawo daga rakiyar sai da bazar wane za a iya rawa ba, to, gaskiya ba za a samu ci gaba ba,” inji Dokta Tukur.

Ya ce wannan matsalar za ta yi kamari yayin da zaben 2023 ke kara matsowa kusa, ganin cewa wadansu iyayen gidan siyasa za su so yin katsalandan a harkokin jihohinsu. (BBC).