Manazarta Halayyar Dan Adam a Najeriya sun ce rashin gaskiya da zullumi ne suka kawo rashin nustuwa da ta sa dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu da na PDP Atiku Abubakar, subutar bakin fara ambato jam’iyyun da ba nasu ba a wurin yakin neman zabe.
Farfesa Sani Lawan Malumfashi na Sashin Nazarin Halayyar Dan Adam da ke Jami’ar Bayero ta Kano ya bayyana cewa bayan Tinubu da Atiku, za a samu karin ’yan siyasa da za su yi hakan a nan gaba.
“Duk shi ya kawo wannan rashin nutsuwar, kuma rashin nustuwar ana fassara ta da rashin gaskiya kan abin da za su fada.
“Kuma za ci gaba da samun haka, saboda akwai fargaba kwarai a zuciyar masu mulki da ma wadanda suke son su yi mulkin kan talakawa,“ in ji Malumfashi, a wani shirin siyasa na gidan rediyon Freedom a Kano.
Tinubu ne dai ya fara subul da bakan a Jos, inda ya fara ambato sunan PDP maimakon jam’iyyarsa ta APC, amma ya yi fargar jaji ya ce APC, kafin daga bisani shi ma Atikun ya yi hakan a garin.
Farfesa Malumfashi ya bayyana , cewa “Wannan subutar bakin za a cigaba da samu daga ’yan siyasa daban-daban, domin abin da hakan ke nufi shi ne an fara kallo-kallo, da kana tsoro-na-ina-tsoronka, tsakanin talakawa da ’yan siyasa, da fargabar abubuwan da suka faru tsakaninsu, da ma wanda zai faru, da tunanin me za su ce wa talakawan, kuma idan sun fada musun ya za su dauke su.”