Shirin Big Brother Nigeria, wanda ake kira BBNaija a takaice, wani shirin talbijin ne da ake shirya kamar gasa da ake haskawa kai tsaye, inda ake zabar tsakanin mutum 12 zuwa 21 su zauna a wani killataccen gida, inda suke zaman kamar na gaske suna rayuwa tare da juna.
Ana zaman ana cirewa daya bayan daya, daga karshe wanda ya rage, zai samu kyautar Dala 171,428.78, misalin Naira miliyan 60 da wasu kyaututtuka da dama.
Asalin shirin
An yi shirin na farko ne, wanda tashar DStv ta dauki nauyi daga 5 ga Maris zuwa 4 ga Yunin shekarar 2016.
Lauya, wanda dan asalin Jihar Anambra Chukwuebuka Obi-Uchendu ne ya kirkiri shirin.
Wanda ya lashe na farko shi ne Katung Aduwak dan shekara 26 a lokacin.
Yadda ake zaman gidan
Ana zama akalla na wata uku, kuma a killace suke kasancewa na tsawon wannan lokaci ba tare da fita ba, ko zuwan baki.
Haka kuma ba a shiga da waya ko wata na’aurar, sannan da Turancin Ingilishi kawai aka amince a yi amfani, sai dai a wasu lokutan akan yi amfani da karyayyen Ingilishi wato Pidgin.
A cikin wata murya da ake ji, wadda ake kira Biggi, wanda ido ne kawai ke bayyana idan muryar za ta yi magana da ’yan gida, kuma wannan muryar ce ake alakantawa da shugaban gidan.
Ana kuma nuna zaton cewa idon na kallon kowa da duk abin da kowa ke yi a gidan
Biggie, wanda muryarsa kawai ake ji yana da karfin ikon aikata komai a gidan, inda yakan yi amfanda karfin ikonsa wajen kawo sauye-sauye a duk lokacin da ya ga-dama.
BBNaija karo 5
A bana, a ranar Lahadin makon jiya ce aka fara shirin, wanda ake sa wa taken “Luckdown” wato kulle domin nuna yanayin da ake ciki na kullen annobar COVID-19.
Akwai mutum 20 a gidan yanzu, kuma masu kallo za su fara zabe tare da cirewa har a samu wanda zai lashe kyautar bana ta Naira miliyan 85.
Yadda ake zaben
Ana yin zaben ta hanyoyi hudu ne. Ko dai ta hanyar sakon waya wato SMS ko intanet ko manhajar DStv to manhajar Gotv.
Amma ’yan Najeriya ne kadai suke iya yin zaben ta waya.
Yadda ake zaben ta waya shi ne, mutum zai zabi wanda yake so, sai ya rubuta vote da sunan wanda yake so ya tura wa 32052. Duk sako daya, yana da maki daya kuma mutum zai iya yin zaben sau 100, kuma duk sako daya Naira 30 ne.
Yadda kuri’a a shirin yake fin na zaben Najeriya
A shirin na bara, wanda aka yi wa lakabi da suna “Pepper Dem” an samu kuri’a sama da miliyan 240, inda a makon karshe kawai da za a fitar da gwanin shekarar, aka samu kuri’a sama da miliyan 50.
Idan aka lissafa kowane sako a kan Naira 30, ya zama ke nan masu shirin sun samu Naira biliyan 7.2 a bara.
A kuri’un da aka jefa a makon karshen kadai, an samu sama da Naira biliyan 1.5.
Da suke cewa kudin da suke samu bai kai haka ba, masu shirya shirin sun ce ba duka kuri’un ba ne ake turowa ta sakon waya, wanda kuma shi ne ake cire Naira 30.
A zaben shekarar 2019, daga cikin masu zabe miliyan 82.3 da ake da su, miliyan 29.3 ne kawai suka zo aka tantance su.
Sannan kuma a karshe kuri’a miliyan 28.6 kawai aka samu. Wanda hakan ke nuna yadda kuri’ar BBNaija ya ninka na zaben Najeriya sau wajen hudu.
Mercy Eke ce ke rike da kambun, bayan ta lashe gasar shirin ta bara.
Ana sa siyasa?
Wasu na ganin cewa ba wai kwarewa ba ko rawar da aka taka ba ce ke ba mutum nasara, kawai yadda ya samu wadanda za su masa kamfe ne.
A kan yi amfani da jaruman fim da manyan mutane musamman masu mabiya da yawa a kafofin sadarwa wajen tallata wadanda suke cikin gidan, tare da nema musu kuri’a, inda wasu ma suke zaben ba tare da sun kalli shirin ba.
A bara, taurao kuma furodusa a masana’natar fim, Ali Nuhu ya rika yin tallar gwaninsa, haka ita ma Jaruma Empire wadda ta yi fice matuka a Instagram da sauransu suka rika tallata gwanayensu.
Batun bata tarbiya
Wasu da dama musamman a yankin Arewa suna ganin shirin yana bata tarbiyar yara, musamman yadda ake nuna masu zama a gidan suna zama kamar na ma’aurata.
Sun ce yadda ake nuna ‘tsiraici’ a shirin ne yake jan hankalin matasa, kuma hakan bai kamata ba domin tarbiyar matasan ake lalatawa.