Ziyarar da Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya kai wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a birnin Landan ba za ta rasa nasaba da wasu abubuwa da suke faruwa a fadar Shugaban Kasa ba, kamar yadda wasu majiyoyi na fadar suka shaida wa Aminiya a shekaranjya Laraba da dare.
Majiyoyin sun shaida wa wakilanmu cewa akwai wani dabam game da ziyarar fiye da kyakkyawan kalamin da Osinbajo ya yi kan samun saukin da Buhari ke yi kuma zai dawo nan ba da jimawa ba.
Daya daga cikin majiyoyin ya ce, akwai babbar barakar a fadar Shugaban Kasar a tsakanin mabiya Buhari da na Mukaddashin Shugaban Kasar. Ya ce, ta bayyana “Wadansu mutane suna wuce iyakarsu.”
Kuma bayanai sun nuna cewa akwai maganganu kan abin da ya shafi kasafin bana da yadda aka jirkita shi ko aka murguda shi don fifita wasu bangarori. “Akwai kuma batutuwan da suka shafi Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu da yi wa ministoci garambawul da makomar Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babchir Lawal da Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa, Ayo Oke wadanda aka dakatar na wasu watanni, sai kuma batun Babban Sakataren Hukumar Inshorar Lafiya. Gaba daya dai ina da yakinin ziyarar ta kwantar da kura,” inji majiyar.
Wadda ta kara da cewa, “Duk da haka wannan yana iya zama kirdado a karshe. Amma ina da tabbacin akwai batutuwa da dama kuma akwai wata baraka.
Wata majiyar ta ce, ta yiwu ziyarar don a nuna wa Osinbajo cewa babu wanda yake da niyyar boye masa wani abu game da abin da ya shafi lafiyar Shugaban Kasar. Majiyar ta kara da cewa, akwai “baraka a kasa” a fadar Shugaban Kasar kuma idan aka lura dangantakar da ke tsakanin ma’aikatan Shugaban Kasar da na Mukaddashin Shugaban Kasar ba ta da armashi kamar yadda take a baya.
Wadansu mutanen Shugaban Kasar an ce ba su jin dadin yadda Osinbajo yake dauka wasu matakai da gudanar da abubuwa. “Bisa abin da muka lura akwai wasu al’amura, kuma ta bayyana akwai baraka, duk da cewa ba furta ta ba. Kuma muna ganin dangantakar ba ta da armashi kamar yadda take a baya. Kuma wani abu game da ziyarar, ina da yakinin ita ce a tabbatar wa Mukaddashin Shugaban Kasar cewa Shugaban Kasar yana warkewa sosai kuma bai kamata a yi masa rufa-rufa ba. In za a tuna hakan ta auku a baya, don haka suke son kauce wa kuskuren da aka yi a baya,” inji majiyar.
Ya kara da cewa: “Wadansu mutane ba su ji dadin wasu canje-canje da Mukaddashin Shugaban Kasar ya yi ba. Amisali wadansu mutane Shugaban Kasar ba su gamsu da canji a Hukumar Fansho da Bankin Masana’antu ba.”
Da aka tambaye shi ko gaskiya ne wasu nadaddu ba su ba Osinbajo girman da ya kamata, sai ya ce: “Ba na jin akwai haka. Na san mutumin, mai saukin kai ne ba mai tsananin son mulki ne da zai rika son ana girmama shi ba. Kuma ban ga wani mutum da bai girmama shi ba.”
A shekaraniya Laraba ce Osinbajo ya je Landan domin duba Shugaba Buhari wanda ya kwashe fiye da wata biyu yana jinya a can, kuma ya ce sun yi doguwar tattaunawa cikin raha kanal’amuran kasa