✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa ni rawa a gidan gala —Tahir Fage

Fitaccen jarumi da aka dade ana damawa da shi a masana'antar Kannywood, Tahir Fage, ya bayyana dalilinsa na yin rawa gidan gala.

Fitaccen jarumi a masana’antar fina-finan Kannywood, wanda ya dade ana damawa da shi, Tahir Fage, ya bayyana dalilinsa na zuwa gidan gala da kuma yin rawa.

A kwanakin baya ne bidiyoyin jaruman, wanda dattijo ne a masana’antar ya karade kafofin sada zumunta yana tikar rawa da ’yan mata, wanda ya sa mutane da dama suna yin Allah wadai.

Daga baya ne wasu suka rika yada ji-ta-ji-ta cewa asiri aka yi wa tsohon jarumin.

Sai dai a zantawarsa da Sashen Hausa na BBC, jarumin ya bayyana cewa rashin kudi ne ya same shi, ga rashin lafiya shi ya sa ya je ya yi rawar domin ya samu kudi.

“Mutane ba sa fahimtar kaddara; Na kasance ina fama da ciwon zuciya, kuma ba ni da kudin magani.

“A lokacin, idan na yi wa Ali Nuhu magana zai ba ni kudin, amma sai na ji kunya.

“Dama da farko shi ne ya ga wata waya a hannuna, sai ya ce ba zai yiwu ba, suna da rai ina rike irin wannan wayar, sai ya yi waya aka kawo min wata.

“To wayar na sayar na sayi magani; Sai na ji nauyin in sake komawa.

“Lokacin da nake bukatar kudi Naira 265,000, na je wajen Rarara ya ban dubu 20. Maishadda ya ba ni dubu 20, sai Abdul Amart ya ba ni dubu 15.

“Ina cikin wannan yanayi ne sai yaran nan (’Yan gidan gala) suka zo suka same ni suka ce sun sanya sunana a matsayin babban bako, za a bude gidan wasa. Nan take suka ba ni dubu N150,000.

“Da na je, ina zaune, sai suka ce akwai wakar Bazar Kowa wadda Lilisco ya hau, sai suka ce don Allah in hau in kwatanta wa yaran saboda ba su san wakar ba.

“Shi ne na hau wakar, sai kuma aka sa wata ta Hamisu Breaker, shi ne fa aka rika yada bidiyoyin nan,” in ji shi.

Tahir Fage ya ce ya yafe wa duk wadanda suka zage shi.