Wani mai maganin gargajiya mai suna Dokta Mato Mai maganin gargajiya a Lambar Rimi ya bayyana wa Aminiya cewa, abin da yas a yake koya wa matasa sana’ar shi ne, ba ya so ya ga suna zaman banza.
Mato ya ce, matashi abin kulawa ne matuka ta yadda zai yi rayuwar da za a amfana da ita ba sai a wajen aiwatar da wani aiki na assha ba.
“A yanzu akwai yara akalla 100 da suke gudanar da wannan sana’a ta sayar da maganin gargajiya a karkashina. Kuma daga cikinsu babu wanda yake biyana ko sisi domin in koya masa, hasali ma da rigunan da suke sanyawa na shaida da katin shaida duk ni ke yinsu a aljihuna domin kara musu kwarin gwiwa, saboda ko ina za su shiga ba za su samu wata matsala ba saboda ina da rajista da duk wata hukumar da ke kula da wannan bangare,” inji shi.
Dokta Mato wanda ya ce, kafin shigarsa sana’ar maganin gargajiya ya yi sana’ar tukin mota wadda a sanadiyarta ce ya ko yi sana’ar maganin gargajiya kuma ya fahimci yadda wasu matasan ke gararamba ba tare da samun abin dogaro da kai ba. “Sai in mutum na yawo zai ga irin yadda mafi yawan matasanmu suke gudanar da rayuwar takaici. Za ka ga matashi in ba ya cikin kungiyar barayi, to ka gan shi a bangaren shaye-shaye ko ta ’yan sara-suka ko bangar siyasa, a karshe in ba Allah Ya kwato matashi ba, zai iya gama rayuwarsa a cikin kunci ko gidan yari. To hangen irin waccan matsalar ce ya sa na fara neman yaran da za mu rika yin sana’ar tare da su. Na fara da nan inda nake, wato Lambar Rimi, amma yanzu ni kaina ba na iya cewa da wadansu ga daga inda suka fito. Kuma kafin mu fara mu’amala da mutun sai ya cika takardar yarjejeniya ta yadda zai rike sana’ar ba tare da ya gurbata ta ba, ka san batun magani yana bukatar kulawa ba ma kamar na gargajiya,” inji shi.
Dokta Mato ya ce, kusan jihohin Arewa babu inda babu irin wadannan matasa masu gudanar da wannan sana’a ta maganin gargajiya a karkashinsa. “Ba wai matasa ba, a yanzu har magidanta suna zuwa suna koyon wannan sana’a a wajena, kuma babu wanda nAke karbar wani abu daga hannunsa don zai koyi sana’ar. Babbar bukatata in ga mutum ya san ciwon kansa kuma yana dogaro da kansa. Kuma daga cikin masu wannan sana’a ina iya cewa yanzu har mai karatun digiri a ilimin boko akwai cikinta kuma har yanzu ni ke koya masa sana’ar don ban yaye shi ba. A ce a dogara ga gwamnati abin ya yi mata yawa. Aikin gwamnati duka nawa ne? Sannan masu nemansa miliyan nawa muke da su? Amma mutum ya samu wata sana’a ko kasuwanci ya rike shi ne mafi alheri fiye da shiga duk wasu ayyuka na assha. Yanzu mu dubi halin da muke ciki musamman ta fuskar ayyukan barna. Duk ba rashin samun abin yi ba ne ke jefa matasa halaka? Da ma wadansu batagari na neman abokan tafiya, maimakon ka tsaya ka nemi na kanka, sai a fara shafa maka mai a baki, daga nan shi ke nan sai abu ya ci gaba. To duk ranar da ka nemi abin da aka saba ba ka tunda da ma ba kai ne ka nemo ba, to shiga cikin ayyukan ta’addanci ya samu kofa,” inji shi.
Ya yi kira ga jama’a musamman masu yin sana’o’i ko kasuwanci su rika janyo matasa suna koya masu koda kuwa na unguwarsu ne, domin ta haka sauran kasashen da muke ganin sun ci gaba suka samu hanyoyin ci gaban da muke gani.
Dokta Mato ya bayar da misali da kasar China wanda ya ce, babu kamarta a yanzu ta fuskar maganin gargajiya, kuma matasa ne ke yi.