✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na zama Halifan Mamman Shata – Sanusi Shata

A ranar Asabar da ta gabata ne kungiyoyin masoya fitaccen mawakin Hausan nan marigayi Dokta Mamman Shata Katsina suka gudanar da taron karrama shi, inda…

A ranar Asabar da ta gabata ne kungiyoyin masoya fitaccen mawakin Hausan nan marigayi Dokta Mamman Shata Katsina suka gudanar da taron karrama shi, inda suka gabatar da dan marigayin a matsayin Halifan Mamman Shata. An yi taron ne a filin wasanni na Katsina, (Open Threatre). Aminiya ta gana da Halifan Shatan, inda ta tattauna da shi a kan rayuwarsa da al’amuran da suka shafi waka:

Aminiya: Mene ne takaitacen tarihin rayuwarka?

Halifan Shata: Sunana Muhammadu Sanusi Mamman Shata Katsina. Kuma ni ne dan Mamman Shata Katsina na 24, kuma ni ne autan Shata. Game da karatu na yi karatu na zamani daidai gwargwado. Kuma bangaren karatun addini ma mun samu abin da Allah Ya so.
Aminiya: Kasancewarka autan Shata, to shekarunka nawa?
Halifan Shata: Akalla na kai shekara 32 ko da 33.
Aminiya: Yaya aka yi ka fara yunkurin farfado da wakoki mahaifinku ka shigo fagen waka?
Halifan Shata: Madalla, na ji dadin wannan tambaya. Wato abin da ya faru, abin yana yi mini zafi, yana yi mini kuna; a ce yau yadda Shata ya aje tarihi a duniya ba wai a kasar Hausa ba, ba a taba yin wani mawaki kamar Alhaji Mamman Shata ba, kamar yadda tarihi ya nuna, amma bayan rasuwarsa, an rasa samun wanda zai cike wannan gurbi. Sai wasu can a gefe, ba su cikin ’ya’ya, ba su cikin dangi, sai su ce su ne Shatan gari kaza, wannan ya taso ya ce, shi ne Shata, wancan ya taso ya ce shi ne Shata; wane Shatan wuri kaza, wane Shatan gari kaza. Kuma har daga cikinmu akwai wasu da suka dan jarraba, amma ganin abin ba za a kai inda ake son a je ba, suka bari. Ni na san yadda Allah Ya yi ni; na kuma fahimci abin da Allah Ya yi min, shi ya sa na ga da in boye kaina, in zalunci al’adar kasarmu; in zalunci masoyanmu; in yaudari kaina, gara in fito wa mutane a fuskar da Allah Ya yi ni. Wannan shi ne dalilina na fito na kama gidanmu na rike. Don haka yanzu duk wani mai tunanin cewa, shi Shata ne ko wane na Shata ne, to ni dai ga ni na fito. Shirye nake, kuma na shirya. Waka da nake yi, ko wadda na sa kaina, ni ma ban san zan yi ba. Allah ne Ya kaddari in yi. Kuma abin da nake gaya wa mutane a fagen waka, wallahi billahi, yanzun nan in ka tsare ni ban san abin da na ce ba jiya. Ka kuwa ga jiya mun yi wasa gabanka, ban san abin da na ce ba, amma idan mun zo, mun zauna filin wasanmu abubuwan suna zuwa. Suna zuwa in mun zo mun zauna. Yanzu idan ka ce mini wakar wa da wa ka yi jiya, sai dai in ce maka na yi wakar Sa’in Katsina yana zaune wurin da kuma ta Sarkin Daura. Akwai wakar masoyinmu, kuma garkuwan mahaifinmu Alhaji Surajo Mai Asharalle yana zaune wurin, amma sauran ni ban san yadda aka yi ba.
Aminiya: Shin ka yi tilawar wakokin Shata ne, tun da ba ka taso ka bi shi yana waka ba?
Halifan Shata: Eh, to maganar tilawa ban yi ba, kuma ba a yi da ni ba. Abin da dai kawai na sani, a iya shekaruna da wayona, duk inda mahaifina Alhaji Mamman Shata zai tafi, yakan sanya ni a gaban mota mu tafi tare. Wasu wurare a yi wakar ina nan, wasu kuwa an yi ba na nan. Kuma ni a yanzu haka ba ni da kaset kwara daya na Mamman Shata. Babu kuma wakarsa a cikin wayata, sai ta amsa kira (ringtone). Idan na tsinkayi mutane sun sanya don ra’ayin kansu, kuma na zo wurin, to zan yi hakuri in saurara, amma maganar in yi irin abin nan da mutane ke ce wa bita (rehearsal) ban yi ba, domin in da na yi, akwai wakoki da na yi kamar biyar zuwa 10, wadanda kuna wurin, ai da ban yi su ba in bita nake yi. Domin a wurin aka kirkire su kuna nan. Yawwa, to abin zuwa yake yi, in ya zo sai a yi shi. In bai zo ba, bai yiwuwa. Ka ji yadda lamarin yake.
Aminiya: Wadanne nasarori ka samu zuwa yanzu?
Halifan Shata: To, alhamdulillahi. Babbar nasarar da na samu addu’ar uwa da sauran iyaye mabiyanta. Mahaifiyata ta amince mini kan abin da na sanya kaina, don ba ita ta yi ni ba, Allah ne Ya kaddari in yi. Inna dai ba ta yi jayayya da nufin Allah ba. Kuma na samu goyon bayan ’yan uwa. Baya ga haka abin da nake alfahari a rayuwata ko yanzu na bar wakar na ci nasara, domin yaran mahaifina, wadanda ya yi waka tare da su, masu kidi da masu amshi, tun bayan rasuwarsa, ba su kara bin kowa ba, babu wanda ya kara daukar kalangu a cikinsu ya buga sai fitowata bayan shekara 15 da rasuwar Shata. Ka ga kuwa a baya akwai wadanmda suka jarraba yin wakar, amma wadannan yara na mahaifina ba su yarda sun bi su ba. Sai fitowata ni karamin da a gidanmu. Suka zo, suka yi mubaya’a, kuma suka rungume ni, ni kuma na bi su a matsayin iyaye. Yanzu haka duk inda nake tare muke. kafata, kafarsu, ban dauki wasu sababbin yara ba. Makadan mahaifina suke yi mini kida; masu amshin mahaifina suke amsa mini waka; babu bare a cikin hidimar.
Aminiya: Ko za ka gaya mana sunayen yaran mahaifinka da kuke tare da su?
Halifan Shata: Daga cikinsu kamar yadda kake gani, ga Sa’idu Sasuwai, mutumin Jos. Duk wanda ya san Shata ya san shi tare da Sa’idu Sasuwai. Ga Baban Yara, Ibrahim; ga Magaji Mahuta. Alhamdulillahi kuma ga Sarki Usaini. Wadannan duk suna bangare ne na kidi, kuma sun yi rayuwa tare da mahaifina. A gefen masu amsa mini waka akwai su Iliya mutumin Kano; akwai su Salisu danyauyau, muna nan tare da shi a Funtuwa. Akwai su Isa Zaki da su Bello Bagobiri da dai sauransu. Duk ina tattarawa ina hakuri da su, domin iyayena ne. Ko zan yi wani yunkuri ba yanzu ba, sai na yi kauri. In ma na yi kaurin dai uba, uba ne.
Aminiya: Na ji ana ta ce wa Halifa, yaya aka yi, mutane ne suka nada maka Halifa?
Halifan Shata: To, alhamdulillahi. Na ji dadin wannan tambaya kwarai. Kalmar Halifa kalma ce mai nauyi. Domin halifanci ana samunsa daga cikin magada. Gado kowa zai iya yi; kowa zai iya gadar wanda ya gada, amma halifanci sai wanda ya dauke dabi’u da wasu al’amuran magabacinsa, kana za a kira shi halifa. Yau kai ka ji ba ni na gaya maka sunana Halifa ba. To, wannan suna Halifa daga cikin gidanmu, yayyena da iyayena, su suka sanya mini suna Halifa. Kuma su suka shaida wa duniya mahaifinsu ya bar Halifa, daga nan har sauran mawaka da sauran masu sha’awar abin da kungiyoyi na masoya Mamman Shata da kungiyoyi na mawakan kasar Hausa, suka rika kirana, suna gayyata ta suna gaya wa mutane cewa ga Halifan Mamman Shata. Asalin wannan suna Halifa daga cikin gidanmu ya fito; tsakankanin ’yan uwana da iyayena.
Aminiya: Sababbin wakoki nawa ka yi?
Halifan Shata: Ni dai wakar Shata ban iya ce maka ga adadi daga sa’adda na fara. Domin duk wakar Shata da ka fadi, zan yi maka yanzu a nan. Kuma wakokina na yi su a wurare da dama. Na yi su gaban sarakuna, irin su Sarkin Bauchi; irin su Sarkin Dass, irin su Lamidon Adamawa, su Sarkin Zazzau da hakimansu. Babu wanda ban je fadarsa ba, ga ni ga shi. Ga hakimansu na yi musu wakoki, na wake masoyansu da dai sauransu. Wadannan wakoki nawa ne; in na yi na Shata, sai in juya in saka nawa.
Aminiya: Ganin cewa, Marigayi Mamman Shata ya fuskanci kushe da hassada, shin wane kalubale kake fuskanta a rayuwa?
Halifan Shata: To, daidai ne. Rayuwa kam an wuto wuri mai nisa, ga alamu yanzu muna wuya, ma’ana mun kusa shanye kan abin. Abin da dai zan iya cewa, Allah Ya ba mu nasara, domin kalubale dai kam akwai shi.
Aminiya: Kana nufin ka shawo kan matsalolin rayuwa?
Halifan Shata: A’a, duk dan Adam ba ya rasa wani abu da ke ci masa tuwo a kwarya, amma akwai iyayenmu, iyayen gidanmu da ke tallafa mana. Akwai ubana, ubangidana, ubangidan mahaifina, wato Alhaji Sahabi Liman kaura, dan Masanin kauran Namoda, mai arziki ne, basarake ne, dattijo ne, kuma uban kasa uban al’umma. Abin da zan iya tunawa a rayuwata ta waka, shi ne mutumin da ya fara karfafa mini gwiwa in fito in gaji gidanmu. A fagen waka, Alhaji Sahabi Liman shi ne mutumin da nake alfahari da shi cewa in fito in gaji gidanmu. Domin duk abin da uba ke yi wa da, idan na tafi wurinsa yana yi mini. Ni kuma ban yar ba, domin duk abin da da ke yi wa ubansa, ni ma babu abin da ba na yi masa.