✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa na yi rajista da Hukumar Tace Fina-Finai – Adam Zango

Fitaccen jarumin fina-finan Hausar nan, Adam A. Zango ya bayyana cewa ya yi rajista da Hukumar Tace Fina- Finai da Dab’i ta Jihar Kano ce…

Fitaccen jarumin fina-finan Hausar nan, Adam A. Zango ya bayyana cewa ya yi rajista da Hukumar Tace Fina- Finai da Dab’i ta Jihar Kano ce domin kawo karshen matsalolin da abokan sana’arsa suke fadawa a cikin na rashin amincewa da fina-finansu.

Jarumin ya bayyana cewa hakan zai ba shi damar zuwa Kano domin gudanar da sana’arsa ba tare da shamaki ba.

A cewarsa, “Na dawo na yi rajista da hukumar ce saboda dalilai biyu: na farko shi ne, furodusoshina da suke yin fina- finai da ni a Jihar Kano suka fi yawa. Sannan kuma yarana da nake tare da su da wadanda nake mu’amala da su duka suna samun matsaloli don ba a kiransu wajen yin ayyuka a dalilin wannan rajista da ban yi ba. Wadansu ma sun yi rajista amma ba sa samun aiki saboda suna tare da ni.”

Tauraron dan wasan ya kara da cewa bai kamata son zuciya ya sanya shi ya zama silar hana wadansu da ke kusa da shi samun aiki ba.

Sai dai ya ce har yanzu bai koma Kungiyar  Kannywood  ba, yana mai cewa “Ina nan a matsayin dan wasan fina-finai mai zaman kansa da ke Kaduna.”

A watan Fabrairu ne Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta ce dole tauraron ya bi dokokinta idan yana so ya je jihar domin gudanar da harkokin fim.

A wancan lokacin Adam A. Zango ya fito a wani bidiyo da tauraruwa Rahama Sadau ta wallafa a Instagram yana yi wa masoyansa Kanawa albishirin cewa zai je jihar domin kallon fim din ‘Mati A Zazzau.’

Sai dai jim kadan bayan haka ne wasu kafafen sadarwa na zamani suka ambato Shugaban Hukumar Malam Isma’ila Na’abba Afakallah, yana shan alwashin kama tauraron idan ya sanya kafarsa a jihar kamar yadda BBC ya ruwaito.

Amma a tattaunawarsa da BBC, Afakallah ya ce ba su hana tauraron shiga jihar ba amma suna da dokoki game da zuwansa. “Idan zuwa zai yi ya kalli fim kawai ya tafi shi ke nan, akwai wadanda ba su da rajista kuma suke zuwa su yi kallo su tafi babu ruwanmu da su. Kwanakin baya wannan hukuma ta yi kokarin tantancewa da tsabtace masu ruwa-da-tsaki a wannan harka kamar yadda doka ta ba ta dama,” inji shi.

Idan ba a manta ba, a watan Agustan bara ne jarumi Adam A. Zango ya bayyana a tattaunawarsa da Aminiya cewa ya koma Legas da harkokinsa bayan ficewarsa daga Kannywood.

A lokacin da Adam A. Zango ya bayyana ficewarsa da Kannywood, ya ce zai ci gaba da gudanar da harkokinsa na  fim  da waka a matsayin kashin kansa ba a karkashin wata kungiya ba, lamarin da ya jawo cece-kuce a wancan lokaci.

Sai dai bai yi karin haske ba game da abin da yake nufi da fita daga Kannywood, ganin cewa akwai kungiyoyi da dama da suke cikin Kannywood din.

Amma ya yi zargin cewa “Ana yin shugabancin kama-karya da rashin hukunta mai karfi ko arziki saboda kwadayi da son zuciya,” kamar yadda BBC ya kalato.