Tijjani Abdullahi Asase fitaccen jarumin fina-finan Hausa ne, kuma shi ne furodusan shirin ‘A Duniya’ sannan ya taka rawar Kanabaro a ciki. ‘A Duniya’ fim ne mai dogon zango, wanda yake tashe musamman a tsakanin matasa. A tattaunawarsa da Aminiya, ya ce fim din an shirya shi ne domin nuna halaye irin na son zuciya na dan Adam.
A takaice wane ne Tijjani Asase?
Sunana Tijjani Abdullahi Asase wanda kuka fi sani da Damisa ko Asase ko Kanabaro a fim din A Duniya. Idan ka kira ni Adahama ma ba ka yi laifi ba, kuma ni mutumin Kano ne. An haife ni a Unguwar Dandago, na yi makarantar firamare a Karamar Hukumar Gwale, na fara sakandare a Gwale, amma ban gama ba na daina karatu saboda gwagwarmayar rayuwa.
- Bichi ba masaka tsinke yayin ba Sarki Nasiru Ado Bayero sandar mulki
- Abin da ya sa ba za mu gurfanar da tubabbun ’yan Boko Haram a kotu ba – Gwamnati
- Abin Da Ya Sa Hukumomi Suka Kasa Shawo Kan Kwalara
Haduwata da maigidana Alhaji Ado Ahmed Gidan Dabino na taso a karkashinsa yana yin littattafai na fara bin sa har na zama jarumin fim yanzu sanadiyarsa na shiga harkar fim .
Daga wane lokaci ne ka fara harkar fim?
Za a samu kamar shekara 30 .
Yaya aka yi ka shiga harkar fim?
Maigidana Alhaji Ado Ahmed Gidan Dabino marubucin littattafai ne ya bude kamfanin a Unguwar Dandago. Kasancewar ni mutum ne mai zuciyar nema, sai na je wajensa har na samu aiki na hada littattafai a lokacin ina aikin kwandasta (yaron mota). To lokacin idan ya yi littattafai sai mu zo mu yi aikin littattafai da dare.
Daga lokacin da suka fara shirya fim sai ya kasance tunda muna karkashinsa mu ne ’yan aike, sannan muna haska fitila. To da irin wannan aka fara, ka ga mun koyi aikin tun muna kanana ke nan.
A fim din A Duniya ka fito a jarumi mai hada-hadar kayan laifi, kana amsa suna Kanavaro?
A cikin al’ummar Najeriya ko in ce Arewacin Najeriya suna fada wa mutum Kanabaro (Canavaro) ne idan mutum ya zama mai kwakwalwa wato mai fasaha ko wata hikima. Shi kansa Canavaro dan kwallon kafar Italiya idan ka kula ana cewa Canavaro ka ci, ka hana ci. Wato ya ci kwallo kuma ya dawo ya hana a ci. To an samo wannan sunan ne daga wani kasurgumin mai laifi a wani yanki da bana wayayyun mutane ba kuma wanda yake da kwakwalwa tun daga tasowarsa wannan kwakwalwar da yake da ita idan ya lissafa sai ka ga yana ganin kamar abu ba zai iya yiwuwa ba, amma sai a ga ya yiwu.
Wane sako fim din A Duniya yake aikewa ga jama’a?
Fim din A Duniya yana nuna zurfin son zuciya na al’umma ne, mutane ba za su bari a samu zaman lafiya ba, kuma idan kana kallon fim din an kirkire shi ne a kan son zuciya irin na dan Adam. Kowane gida sai da aka ajiye shi kuma Manzon Allah (SAW) yana cewa a jikin dan Adam akwai wata tsoka idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru idan ta lalace dukkan jiki ma ya lalace wato zuciya.
Idan ka kalli gidan su Dan Mama akwai son zuciya a ciki ’yan sanda sun biyo yaronta ya tsallaka katanga ta ce bai shigo gida ba. Idan ka kalli gidan Malam Wa-Katava ya ce ba za a taba dansa ba, saboda son zuciya. Idan ka dawo shi kansa uban tafiyar da aka taba kannensa ya kafa hujjar da bai yarda komai kaddara ba ne saboda son zuciya. Al’umma suna rayuwa ne a kan son zuciya shi kuma dama son zuciya bacin zuciya.
Yaya ka samo inkiyar da yaranka suke fada maka a fim din na ‘Inda Rabbana’ sai ka ce ‘ba wahala’ kuma me ya sa?
Inkiya ce kawai. Akwai kuma irin su ‘a kan haka-haka’ ‘one day-one day’. An sako kalmar ce domin wata kalma ce mai dadi bai kamata ba a ce ta zo a wurin ’yan iska ba. Ban bi mutane ina tambayarsu me ya sa ake amfani da kalmar ba amma yanzu ana fadinta a ko’ina. Ita kuma ‘haka-haka’ a bangaren siyasa ce, to kada ka dauko inkiyar wani sai muka dauko wannan da sauransu.
Daga cikin fina-finan da ka yi, wanne ne ya fi burge ka kume me ya sa?
Fim xin da na fi so na fi alfahari da shi shi ne fim din Ahlul-Kitab. Abin da ya sa nafi son fim din kuwa saboda a dalilinsa an samu wadanda suka Musulunta kuma an yi bikin musuluntar da wadansu da kuma yadda muka samu wasu rubuce-rubuce na wadansu mutane da suka yi na Musulunci .
Mene ne sakonka ga masu kallon fim din A duniya da sauran fina-finan da ka yi?
Ina alfahari da su kuma ni ina so in roke su don Allah duk wani ya ga an yi kuskure, don Allah don son Annabi a zo min da sigar gyara idan aka gyara an taimake mu. Idan wani ya hango mana abu kaza da ka yi ba daidai ba ne ka gyara insha Allah gobe ba za ka kara ganin haka ba. Amma a yi mana ta lafazin da za mu iya karbar gyaran ba ka tafi soshiyal midiya ka ce gaba daya abin da muke yi ba daidai ba ne.