✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Abin da ya sa na rungumi sana’ar gyaran waya duk da kasancewa ta mace – Falmata

Wata kungiya ce dai ta ba ta horo kan gyaran wayar tun da farko

Wata budurwa mai suna Malama Falmata Mafa ta zama mai gyaran wayar salula daya tilo da aka sani a Karamar Hukumar Mafa ta Jihar Borno.

Malama Falmata Mafa ta shirya biki na musamman ne don nuna jin dadinta ganin yadda kusan dukkan mutanen yankinta yanzu sun dogara da aikin hannunta na gyaran wayar hannu.

Wata kungiya ce mai zaman kanta ta kasa da kasa da ke mayar da hankali wajen inganta ’yancin yara da daidaito ga ’yan mata mai suna Plan International ce dai ta bata horo kan wannan sana’ar ta gyaran wayar salula.

Ta nuna jin dadinta ga kungiyar da ta ba ta horon da har ta ke dogaro da kanta wajen samun abubuwan bukatun ta da na iyali ta.

A cewarta, “Kafin na koyi wannan sana’a ta gyaran waya, ’yan uwanmu maza ne kawai suke gyara wayoyi kuma bukatar ta yi yawa a Karamar Hukumar Mafa. Yanzu kuma ga shi cikin hukuncin Allah a matsayina na ’ya mace na iya gyaran.

“Don haka na gode wa wannan kungiya don horar da ni da kuma tallafa mini da wasu kayan aiki kamar mita, inji, allo da sauran kayan aikin gyaran waya.”

“A baya, ba ni da aikin yi amma saboda wannan taimako na kungiya a cikin al’umma ta, ya sa ina da sana’a ta kaina,” in ji Falmata.

Ta kara bayyana yadda ta jure matsi daga mutanenta, wadanda suke ganin sana’ar ba ta dace da jinsinta ba, a matsayinta na ’ya mace.

“Ko da mutane suka yi kokarin hana ni shiga cikin wannan aiki na gyara waya amma duk da haka ban yi kasa a gwiwa ba wajen jajircewa wajen koyon yadda ake gyaran waya.

“Yanzu zan iya gyara fuskar waya, canza abin magana da wajen caji, zan iya yin wasu gyare-gyare masu yawa.” in ji Falmata.

A cewarta, ta lura cewa a yanzu tana cikin farin ciki domin hatta mutanen da suke sanyaya mata gwiwa a baya, a yanzu sukan kawo mata gyaran wayarsu.

“Wadanda ke kara min kwarin gwiwa su ma suna kawo wayoyinsu domin a gyara musu,” in ji ta.