A kwanakin baya ne aka gudanar da taron kaddamar da wani littafi mai suna “Sanin Yadda Ake Sallar Jana’iza Ga Matattu A Ilimance Da Kuma Aikace” a garin Jingir da ke karamar Hukumar Bassa, Jihar Filato. Wani matashi mai suna Malam Ukasha Hamza Abubakar Jingir ya rubuta da harshen Larabci. Bayan kammala taron kaddamar da littafin ne wakilinmu ya tattauna da marubucin, kan abin da ya
Sai mu fara da jin tarihin rayuwarka a takaice ko?
Ni dai an haife ni ne a ranar 25 ga watan 2 na shekara ta 1982, a nan garin Jingir da ke karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato. Farko na yi makarantar allo a wajen kakana, Malam Abubakar Sulaiman Jingir. A wajensa ne na fara koyon karatun Alkura’ani. Bayan haka na koyi karatun Alkura’ani a wajen malamai da dama a wannan gari na Jingir, har Allah Ya sa na sauke. Daga nan wani kawuna mai suna Malam Muhammad Sadisu ya dauke ni, ya kai ni babbar makaranta, School for Higher Islamic Studies da ke Sarkin Mangu a garin Jos. Bayan da na kammala wannan makaranta a shekara ta 2002 sai kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, ta tura ni zuwa garin Jega da ke Jihar Kebbi domin na karantar.
Nayi shekara 11 da kwanakin 19 ina karantarwa a can kuma na rika zuwa zaurukan manyan malamai ina daukar karatun litattafai. Kuma a garin na Jega akwai reshen makarantar School for Higher Islamic da aka bude. Na shiga wannan mkaaranta na yi karatun diploma. A wannan gari na fara rubuta wani littafi wanda yake karantar da ma’anonin haruffan Larabci da ma’anoninsu na asali, a shekara ta 2011.
Bayan zaman da na yi a garin Jega, sai kungiya ta Izala ta dawo da ni zuwa wannan gari na Jingir, domin na ci gaba da karantarwa a makarantar haddar karatun Alkura’ani da ke garin a shekara ta 2012. Ganin irin ci gaban da ake samu a wannan makaranta, sai shugabannin malaman wannan gari suka bukaci na bude wata makaranta ta koyar da haruffan Larabci. Allah Ya ba mu babbar nasara a wannan makaranta da na bude, a cikin shekaru biyu da watanni aka sami dalibai 42 da suka sauke karatun Alkur’ani mai girma. Har yanzu ina nan zaune a wannan gari namu na Jingir, kuma ina ci gaba da karantarwa kuma ina da mata biyu da ’ya’ya 6.
Ma ye ya karfafa maka gwiwar rubuta wannan littafi, wanda yake bayani kan Sallar jana’iza?
Babban abin da ya karfafa mani gwiwar rubuta wannan littafi shi ne, na yi nazari ne na gano cewa mafiya yawan mutane, musamman ma matasa suna da kokarin zuwa Sallar jana’iza amma ba su san addu’o’in da ake karanta wa mamaci ba. Kuma ga shi addu’o’in da ake karanta wa mamaci, liman ba ya iya dauke wa wani. Don haka na yi kokarin rubuta wannan littafi, domin na ilmintar da al’umma kan yadda ake sallar jana’iza da addu’o’in da ake yi wa mamaci. Bayan da na yanke shawarar rubuta wannan littafi, sai majalisar malamai ta kaungiyar Izala suka yanke shawarar karfafa mani gwiwar rubuta wannan littafi.
Wadanne abubuwa ne wannan littafi ya kunsa?
Shi dai wannan littafi mai suna ‘Sanin Yadda Ake Jana’iza Ga Matattu A Ilimince Da Kuma A Aikace A Mazahabar Malikiya’ ya kunshi babi guda uku. Babi na farko ya kunshi yadda za a iya yi wa mamaci idan ya zo gangara, kafin ya rasu, da bayan ya rasu, da abin da ya kamata a yi wa mamaci kafin a yi masa wanka da yadda ake yi wa mamaci wanka da siffofin da mai wankan ya kamata ya kasance da kuma yadda ake sanya mamaci a likafani.
Babi na biyu kuma ya kunshi bayani kan Sallar jana’iza da hukumcinta da sunnoninta da mustahabbanta da abubuwan da suke bata ta da limanci a cikin Sallar jana’iza da dai sauransu. Babi na uku kuma ya kunshi yadda ake Sallar jana’iza a aikace da yadda ake daukar mamaci da yadda ake raka shi da yadda ake binne mutum daya ko mutane da yawa da yadda ake ta’aziya da cin abinci a wajen ta’aziyya. Wannan babi duk ya yi magana a kai.
Kana da burin fassara wannan littafi zuwa harshen Hausa?
Babu shakka ina da kudurin ganin na fassara wannan littafi zuwa harshen Hausa, domin amfanin jama’a ga baki daya.
Baya ga wannan littafi ko kana da burin ci gaba da rubuta wasu littattafai?
kwarai, ina da burin ci gaba da rubuta littattafai, musamman kan addinin Musulunci, domin akwai bugun wannan littafi na biyu yana nan tafe. Bayan haka, nan gaba ina son na rubuta littafi kan jinin haila na mata. Sannan kuma ina son na rubuta littafi kan yadda ake yin tarbiyya a addinin Musulunci.