Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ’yan adawa sun yi amfani da Rikicin Boko Haram da sace ’yan matan Chibok da batun tallafin man fetir wajen kada shi a zaben 2015.
Jonathan ya fadi haka ne a yayin kaddamar da littafinsa mai suna, “My Transition Hours” wanda ya gudana ranar Talatar da ta gabata a Abuja.
Littafin wanda ya kunshi Babi 15, ya fayyace irin darusan da tsohon shugaban kasan ya samu da kuma mawuyacin halin karshe da gwamnainsa har zuwa mika mulki ga Muhammadu Buhari. Sannan ya cewa hadama da dogon burin wasu gwamnonin PDP da idanunsu ya rufe a lokacin suka koma AP, da yadda aka rika yada labaran kage da karairayi a kansa da gwamnatinsa, sun taimaka wajen kayar da shi zaben na 2015.
Jonathan ya kuma Dora laifin faduwarsa zabe ga wasu manyan ’yan Arewa wadanda suka so mulki ya koma a Arewa ta kowane hali, cewa sun kitsa makarkashiyar hana shi zarcewa.
“Wasu gwamnonin da suka kammala wa’adin shekarun su takwas, sun nemi zama mataimakin shugaban kasa a zaben 2015, wasu kuma suna hankoron zama shugaban kasa. To sun san idan har na fito takara, babu wanda a cikinsu zai iya cimma burinsa na zama shugaban kasa.
“Yayin da suka canja sheka zuwa APC ana kusa da fara shirye-shiryen zaben 2015, babu wanda ya damu da abin da PDP ta yi ko ba ta yi ba dangane da batun cika alkawuran da muka dauka a jam’iyyance. Sun ki yarda na zarce saboda dogon burinsu na son zuciyarsu kawai. Don haka babu ruwan kowa da ayyukan da gwamnatina ta yi, su dai a kayar da ni kawai shi ne abin da ke gabansu,” inji Jonathan a cikin littafin.
Jonathan ya kara da cewa duk da gudun kaddarar da yawancin gwamnonin da suka koma APC suka yi, hakan bai hana cin mutuncinsu a yanzu da tozarta su cikin gwamnatin da suka taimaka aka kafa ba.
Ya ce tuni dama wasu shugabannin Arewa na kungiyoyin dattawan yankin suka nemi hana shi zama shugaban kasa wanda dokar Najeriya ce ta ba shi wannan damar zama, bayan rasuwar Tsohon Shugaban Kasa, Umaru Yar’Adua a 2010.
Jonathan ya ce duk da irin wannan barazana da suka rika nuna masa da kuma kaifin adawa, sai da ya yi nasara a zaben 2011.
“Dalilin da ya sa na fito ina wannan kururuwar a yanzu shi ne saboda dukkan tuggun da aka kitsa domin kayar da ni zabe, daga kasashen waje ne, musamman daga Amurka.
“A shekarun da na shafe ina mulki a kasar nan, an yi ta danganta ni da labarai na karairayi da sharri, musamman wasu farfaganda da aka rika yi min daga manyan kafafen yada labarai. Kuma duk karya ce, babu wani sunayen da na sa aka dauka na manyan ’yan adawar da na shirya kakkabewa daga doron kasar nan.
“Sannan kuma maganar wasu makudan kudade har dala milyan 49.8 sun salwanta, duk karya ce. Su kan su wadanda suka yi wannan zargin da yarfe, sun san cewa duk labaran kanzon kurege ne kawai.”
“Babu abin da ya fi bakanta min rai sai da aka rada wa gwamnatina ko kuma ni kaina wai “mai dakusassar kwakwalwa.” An kau da kai daga gagarumin ayyukan alherin da gwamnatina ta samar. Kada a manta fa a lokacin gwamnatina ce, a cikin 2013 Najeriya ta zama mafificiyar kasar da ta fi ci gaban tattalin arziki a Afirka. Sannan kuma a lokacin gwamnatina dan Najeriya a karon farko ya zama shugaban Bankin Inganta Tattalin Arziki na Afirka,” inji Jonathan.