A farkon makon ne Fadar Shugaban Kasa ta fitar da sanarwar korafi da bukatar bincike a kan aikace-aikacen Kungiyar Kare Hakki dan Adam ta Duniya (Amnesty International) reshen Najeriya bayan Rundunar Sojin Najeriya ta yi zarge ta da shirin jawo rabuwar kai a tsakanin ’yan kasa. Aminiya ta zanta da Mai taimaka wa Shugaban Kasa kan Al’amuran Watsa Labarai, Malam Garba Shehu, inda ya yi bayani a kan lamarin da kuma wasu batutuwa:
Kun fitar da bayanin zargi da gargadi ga Kungiyar Amnesty reshen Najeriya, shin me kuka gano?
Abu na farko shi ne bayanan da suka fitar a kan kashe-kashe da suka auku a tsakanin Fulani makiyaya da manoma, inda su ka rubuta littafi a kan fitinar na tsawon shekara uku da suka wuce. Abin la’akari a nan shi ne, shin tun a wane lokaci ne aka fara wannan rikici? Duk wanda yake karanta tarihi ya san cewa rigimar makiyaya da manoma ta fara ne tun lokacin mulkin mallaka, wannan a rubuce yake. Shi ya sa a lokacin Gwamnatin Arewa a karkashi Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato aka fitar da tsarin burtali tun daga Arewa har zuwa bakin teku tare da alamta cewa wannan hanya ce ta dabbobin makiyaya don a samu zaman lafiya a tsakaninsu da manoma. To a yanzu duk an cinye filayen nan da gonaki da gidaje da wasu abubuwa, kusan duk burtalin da aka sani babu su, wannan ba shi ne maganar da muke yi ba. Idan mun koma kan batun da muke yi, tambaya a nan ita ce shin me ya sa littafin da suka rubuta ya kauce wa ambato fitinar tun a lokacin Bature? Me ya sa rubutunsu bai taba fitinar a lokacin Jamhuriya ta Farko ba? Aka zo aka yi zamanin mulkin soja, sannan lokacin mulkin farar hula na Obasanjo, ga na marigayi ’Yar’aduwa, sannan na Jonathan, sai aka tsallake gaba dayan wannan tarihi, aka takaita lamarin a kan shekara 3 na mulkin Buhari, wanda a kididdige barnar da aka yi a tsakanin Fulani da makiyaya a karkashin mulkin Jonathan da Obasanjo ya ninka na yanzu sau da dama.
Kada ka manta cewa a karkashin gwamnatin da ta gabata, a yini guda an kashe Sanata da dan Majalisar Tarayya. Sannan akwai jihar da aka cire Gwamna mai ci dalilin rigimar manoma da makiyaya, amma duk sai aka kau da kai a kan wadannan abubuwa ba a yi ko tsokaci a kansu ba, sai kawai shekara 3 na mulkin Buhari kadai aka ware a nuna wa duniya cewa an yi kashe-kashe.
Sannan abu na biyu shi ne, la’akari da lokacin da aka fitar da littafin, wato lokacin da ake dab da yin zabe da bai wuce kwana 60 ba. Don kawai a samar da makami da za a kai wa Buhari hari da shi a yi masa illa. Wannan shi ya sa muke ganin akwai wata manufa da ake so a cimma a cikin lamarin. Sannan littafin idan akwai adalci a cikinsa sai a nemi jin ta bakin jami’an tsaro, a kan me ya sa hakan ya kasance. Bayanin da sojoji da sauran jami’an tsaro suka fitar shi ne babu wanda ya neme su a kan wannan lamari don jin ta bakinsu. Wannan ya nuna a fili cewa fitina ce ta siyasa kuma muna da yakinin haka. Kuma bayanin Shugaban Kasa a kai shi ne Gwamnatin Najeriya ba ta adawa da kungiyar Amnesty ta duniya, ba ta adawa da manufofinsu, tana ma sha’awar gwagwarmayar da suke yi na neman kwatar hakkin ’yan Adam da kungiyar ta duniya take yi.
Amma bukatarsa ita ce hedikwatar kungiyar ta binciki reshenta na Najeriya a kan aikace-aikacensu, shin gwagwarmayar suke yi ko siyasa suke yi? A takaice yaki da ta’addanci da wannan gwamnati take yi ya kasu kashi biyu, akwai yaki da Boko Haram a daya bangaren sai kuma yaki da kungiyar Amnesty a daya bangaren, sai mu san shin da wanne za mu ji.
Kafin korafi kan Amnesty akwai yunkurin dakatar da ayyukan Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF). Ba ku ganin irin wadannan matakai za su sa kungiyoyin su ma su dora wani zargi?
Al’amarin UNICEF wannan Kwamandan soja ne da ke kula da Arewa maso Gabas ya dakatar da su a iya yankin. Kuma kafin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai ga sa baki a lamarin, su kansu shugabannin soja a mataki na koli sun yi nasu, inda suka nuna ba haka ya kamata a yi ba, a dai gindaya mauu sharadi. Sai dai matakin da Kwamandan tun farko ya dauka ya biyo bayan samun bayanai ne a kan Hukumar UNICEF kan wasu abubuwa biyu na ayar tambaya. Na farko shi ne UNICEF ta zakulo mutane daga daukacin kananan hukumomin Jihar Borno tare da tara su a waje guda tana ba su horo. Horon da take ba su ba a kan yadda za su ba da agajin gaggawa ne ba, ba a kan yadda za su nemo abinci su taimaki wadanda ba su da shi ne ba, ko kan yadda za a samu malamai da za su ba da ilimi ga ’ya’yanmu da kuma na Boko Haram da suka zama marayu a sansanoni da sauran matsugunonan da ke watse a jihar ne ba. Abin da ake ba su horo a kai shi ne yaya za su sa ido a kan sojojin Najeriya don su rika ba da rahoto a kansu, rahoto kuma munana masu kama da leken asiri. Wannan shi ne aka gano suna koya wa matasa, soja ba za su yarda da wannan ba. Abu na biyu kuma shi ne bayanin da ya fito cewa sukan yi rikon sakainar kashi a kan kayan agajin da suke samarwa a yankin kamar abinci da sauransu. Misali, sai a loda motoci da kayan abinci a kama hanya zuwa wani waje, sai a ce mota ta lalace, ’yan Boko Haram su fito su kwashe abincin su shiga daji da shi. Sojoji a tunaninsu anya babu hadin kai a wannan abu da ake yi? Wannan shi ne ya sa aka fitar da sanarwar dakatar da su a farko. Sai dai an sa baki an ce su zauna da sojan Najeriya su samu yarjejeniya a kan yadda za su rika tafiyar da aikin a tsakaninsu ba tare da cin amana ba.
Wannan gargadi da kuka fitar a kan Amnesty idan lamarin bai sauya zane ba, akwai shirin daukar wani mataki?
To ba wata kasa, ina tabbatar maka a duniya da za ta bari ana yi mata irin wannan yankan baya. Domin tsarin dokokin yaki daban ne kuma babu wata kasar da tana fuskantar yakin sannan ta yarda a rika yi mata irin wannan zagon kasa. Idan Amnesty za ta binciki reshenta na Najeriya tsakani da Allah ina tabbatar maka cewa babu tababa za su gano cewa siyasa ta shiga cikin lamarin. Saboda haka lallai su dauki mataki a kai, idan ba su dau mataki ba, to duk matakin da Gwamnatin Najeriya ta dauka daga bisani to su yi kuka da kansu, ko ba komai ta dai yi kashedi.
Akwai korafin cewa jagororin rundunonin tsaro na kasar nan sun wuce wa’adin da ya kamata su yi kuma sakamakon haka ne ake samun akasi a yaki da ta’addanci. Me ya sa gwamnati ta doge a kan kin maye gurbinsu da wadansu?
Ina ganin akwai salon siyasa biyu a game da wannan korafi. Siyasa ta farko ita ce ta rashin fahimtar mene ne hurumin Shugaban Kasa kan nada jagororin nan ko dakatar da su? Shugaban Kasa a tsarin mulki shi ke da ikon nadi ko cire masu irin wannan mukami. Idan ya gamsu da wanda ya nada, ya gamsu yana yin aiki, babu wanda ya isa ya ce masa sai ya cire shi. Ashe tunda bai cire ba ya nuna ya gamsu da aikin da suke yi ke nan. Siyasa ta biyu ita ce a duk lamari ba ka rasa ’yan cikin gida ’yan cin dudduge. Wadanda watakila gani suke yi nasu lokaci ya zo, wadanda suke kai su kauce su ma su samu su hau kan kujerar. Wannan abu ne da ke faruwa a ko’ina,, kai hatta a gidajen jaridu watakila wani zai duba ya ce editanmu ya dade a kan kujera, gara a kawar da shi ni ma in hau; duk wannan yana faruwa.