Hukumar Kula da Masu Yi wa Kasa Hidima ta Najeriya (NYSC) ta ce, ta rufe sansanonin atisaye a fadin kasar ne da nufin kauce wa yaduwar cutar kurona.
Babban Daraktan Hukumar Bigediya Janar Shuaibu Ibrahim, wanda ya bayyana hakan ta wayar salula ga Daily Trust, ya ce an dauki matakin ne duk da cewa ba a samu mai dauke da cutar a wani sansani ba domin riga-kafi.
“Zaman zullumi na karuwa a sansanonin, inda da zarar an ji wani ya yi tari ko atishawa ko yana zazzabi sai ka ga hankali ya tashi,”in ji Birgediya Ibrahim.
Da safiyar yau Laraba ne dai Hukumar ta bukaci masu yi wa kasar hidima su bar sansanonin sun tafi wuraren da aka tura su su yi aiki.
Birgediya Ibrahim ya ce, ko a lokacin da aka samu bullar cutar Ebola, an takaita ayyukan masu yi wa kasa hidima duk da suna sansanonin a lokacin.
Ya kuma ce ko da yake tuni hukumomi suka dauki matakan hana kamuwa da cutar, akwai bukatar dakatar da ayyuka don ganin ba wanda ya kamu.
Sannan kuma, a cewar Babban daraktan na NYSC, tun da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarni dakatar da Gasar Wasannin Motsa jiki ta Kasa, to ya kamata hukumar tasa ta dauki irin wannan mataki.
Ranar Alhamis 12 ga watan Maris aka kaddamar da Ayari na Farko na ’Yan Yi wa Kasa Hidima na 2020 bayan sun shiga sansanonin ranar Talata 10 ga wata da zimmar za su kammala ranar 30 ga wata.
Sai dai kuma Bigediya Janar Ibrahim ya ce idan aka tsallake wannan siratsin za a dawo da masu yi wa kasar hidima don sun yi atisayen da suka saba.