Malam Nasiru Abdullahi wanda aka fi sani da Babawo shi ne Shugaban Masana’antar Nikan garin Masara mai suna Mai dankunne Maize Flowers Meals da ke garin Jingir a karamar hukumar Bassa ta Jihar Filato. A tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana yadda suka bude wannan masana’anta da irin nasarorin da suka samu zuwa yanzu. Ga yadda hira ta kasance:
Aminiya: A wane lokaci ne kuka bude wannan masana’anta ta sana’ar nikan masara?
Babawo: A gaskiya mun bude wannan masana’anta ne a shekarar 2013 kuma a wannan masana’anta muna sana’ar nikan garin masara ne. Kuma mun yi hakan ne domin dogaro da kai. Muna da injinan nika irin na zamani, muna da injin da yake bushe datti ya cire kwari da kasa, har ila yau muna da injin da yake jika masara ya surfeta. Muna gyara masara ta koma gari da fitar da tsaki na burabusko da fitar da dusa wadda muke sayar wa masu gidajen kaji, ayyukan da muke yi ke nan a wannan waje.
Aminiya: Wadanne wurare kuke kai garin masarar da kuke nikawa?
Babawo: Akalla muna da rassa guda 16 a fadin kasar nan da muke kai garin masarar da muke nikawa mu sayar. Misali kamar a kudancin kasar nan, muna da rassa a garin Benin da Warri.
Haka kuma a nan yankin arewa muna da rassa a garin Magama da Tulden Fulani da ke
karamar hukumar Toro a Jihar Bauchi. Har’ila yau, muna da rassa a garin Jos, babban birnin Jihar Filato da garin Saminaka da ke
Jihar Kaduna. A takaice dukkan wadannan wurare muna kai garin da muke nikawa mu sayar.
Aminiya: Ya zuwa yanzu kuna da ma’aikata nawa?
Babawo: Ya zuwa yanzu muna da ma’aikata shida a shagonmu na nan garin Jingir.
Aminiya: A kowace rana kuna nika masara kamar buhu nawa?
Babawo: Muna nika buhunan masara 40 zuwa 50 a kowace rana.
Aminiya: Wadanne irin nasarori ne kuka samu a wannan waje?
Babawo: A gaskiya mun sami nasarori da dama a wannan waje domin babu abin da zamu ce sai dai mu yiwa Allah godiya. Dukkan wuraren da muke kai garin da muke nikawa mu sayar suna yaba mana kan yadda muke wannan sana’a. Don haka muna ganin mun sami babbar nasara a wannan waje.
Aminiya: Wadanne matsaloli ne kuke fuskanta a wannan waje?
Babawo: A gaskiya babu wata matsala da muke fuskanta a wannan waje wadda ta wuce matsalar wutar lantarki. Saboda matsalar wutar lantarki da ake fuskanta a kasar nan, ba dan matsalar rashin wutar lantarki ba, da mun kara daukar ma’aikata akalla mutum 30 a wannan waje.
Aminiya: Mene ne burinku a wannan masana’anta?
Babawa; Babban burinmu shi ne mu sami fili na musamman mu kara fafada aikinmu, mu kara daukar ma’aikata. Domin wannan wuri da muke zaune a yanzu muna haya ne.
Aminiya: Wane sako ko kira kake da shi zuwa ga al’umma musamman matasa dangane da mahimmancin rungumar sana’a?
Babawo; Ina kira ga matasa kan su fahimci cewa yanzu fa duniya ta
sauya, rayuwa ba ta yiwuwa sai da sana’a. Don haka ina kira ga matasa kan kowa ya tashi ya kama sana’a domin ya rike kansa kuma ya kare mutuncinsa.