Jagoran tawagar masu zanga-zangar neman Shugaban Buhari ya dawo ko ya sauka daga mulki, Mista Charles Oputa wanda aka fi sani da Charly Boy ya ce sun dakatar da zanga-zangar da zaman dirshan din da suka faro a makon jiya, inda ya yi zargin cewa ana yi wa mambobin tawagarsa barazanar kisa.
Charly Boy, ya shaida wa manema labarai haka ne a shekaranjiya Laraba a dandalin Unity Fountain kwana daya bayan da ya sha da kyar a Kasuwar Wuse da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja, lokacin da shi da tawagarsa suka kusa kasuwar da karfi don gudanar da zanga-zangar neman Shugaba Buhari ya dawo daga jinyar da yake yi a Ingila ko kuma ya sauka daga mulki.
Sai dai kuma Charly Boy ya ce sun dakatar da boren ne domin su sake dabaru da fadadada ayyukannsu. Kuma ya ce ba su kadu da farmakin da aka kai musu a kasuwar ta Wuse ba.
Hatsaniyar da ta auku a kasuwar ta Wuse dai ta jawo mahukuntan kasuwar sun rufe ta a ranar Talatar don dakile yiwuwar aukuwar rikici, inda jami’an tsaro suka rufe kasuwar wadda daya ce daga cikin manyan kasuwannin Abuja.
An samu yamusti ne a tsakanin magoya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da su Charly Boy da suke neman ya sauka daga mulki bayan da masu neman Shugaba Buhari ya dawo daga jinya ko ya sauka suka kutsa cikin kasuwar da karfi suna ihun Buhari ya dawo ko ya sauka daga mulki in ba zai iya ba.
Wannan ne aka ce ya tunzura ’yan Arewa musamman al’ummar Hausawa da suke kasuwar, inda suka mayar da martani da cewa, “Sai Baba Buhari!” suna cewa “karya ne! karya kake Charly Boy.”
A nan ne lamarin ya koma rikici aka shiga jefe-jefen juna da duwatsu har aka farfasa wa Charly Boy motarsa da na ’yan tawagarsa, inda suka sha da kyar.
Daga bisani ’yan sanda suka zo suka yi ta harbin iska don dawo da doka da oda, kafin sun kori kowa a rufe kasuwar.