Tsohuwar sana’ar tallar gasasshen mama ko tsire yanzu ta tasamma zama tarihi a kasar Hausa, inda yanzu mahauta suka fara daina zagawa don yin tallar.
Binciken Aminiya ya gano cewa yanzu akasarin masu sana’ar sun koma hada naman sannan su zauna a shagunansu ko tukubarsu suna jiran masu saye su zo inda suke.
- Ango ko Iyayen Amarya: Wa ya fi dacewa ya yi kayan daki?
- ’Yan sanda sun cafke wanda ya kashe dalibar Jami’ar Jos
A shekarun baya dai, tallar gasasshen nama ko soyayye sananniyar sana’a ce, inda masu sayarwa kan sanya naman a cikin daro su rika zagawa kwararo-kwararo suna talla.
Wani tsohon ma’aikacin gwamnati da ya yi ritaya a Birnin Kebbi, Mu’azu Bala, ya shaida wa Aminiya cewa a zamanin kuriciyarsa, ya san mahauta kan zaga wurare a kauyuka da birane don tallar naman.
Ya ce a da can, akan gan su a kasuwanni suna gasa naman, kafin daga bisani su dauka su shiga gari da shi.
A cewarsa, duk da haka wasu mutanen sukan gwammace su je kasuwa su sayo, saboda a can za su samu sabon gashi.
“Dadinta shi ne ba sai ka shiga neman su ba, kana zaune a kan layi za su zo, su suke yawon neman masu saye.
“Amma yanzu zamani ya sauya sana’ar fawa kamar sauran bangarorin rayuwa, inda yanzu yawancin mahauta suka koma zama a wuri daya a tukubarsu, sabanin yadda aka sani a baya.”
Wani mahauci da ya shafe shekara 30 yana sana’ar fawa, Muttaka Magawata, ya ce a da can ba kowa ke iya sayen nama ya ci a-kai-a-kai ba kamar yadda ake yi a yanzu.
Muttaka ya ce hakan ce ta sa a da can din dole mahauci ya fita ya yi talla domin samun masu sayen namansa, ko kuma ya yi kwantai.
Ya kara da cewa sana’ar fawa wani bangare ne na rayuwar al’umma, don haka dole ta rika tafiya da yanayin al’amura.
“Yanzu mahauta da yawa sun kammala jami’a, kuma duk abin da ’yan boko suke cikinsa dole ya samu sauye-sauye.
“Yanzu ba ma yawon talla saboda bai dace da zamani ba. Abubuwa sun canza, haka ma sana’armu.
“Yanzu sayar da suya ba shi da wahala kamar a shekarun baya, inda sai ka zaga gari ko garuruwa biyu, watakila ma har sau biyu a rana kana yin talla.
“Ya kuma kamata a lura cewa a wancan lokacin idan mahauci bai fita ya nemi masu saye ba, kwantai namansa zai yi. In ya ci gaba da hakan kuma jarinsa karyewa zai yi,” inji Magawata.