Malamin Musuluncin da Gwamnatin Kano ta dakatar daga gabatar da wa’azi, Sheikh Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara, ya yi zargin cewa an yi hakan ne saboda bai goyi bayan Gwamna Ganduje ba a zaben 2019.
Sheikh Abduljabbar ya yi zargin ne a raddinsa ga Gwamnatin Jihar Kano wadda ta ce ta dakatar da karatuttukansa a majalisi da kafaren yada labarai ne don kar ya ta da fitina a jihar.
- Gwamnatin Kano ta rufe masallacin Sheikh Abduljabbar kan ‘batanci ga Sahabbai’
- Rufe masallaci: Sheikh Abduljabbar ya yi raddi
“A bude lamarin yake, Ganduje ya sha fadin cewa ba ya yafiya idan aka masa abu.
“Na yake shi a zaben da ya wuce, kuma ya yi alkawarin daukar fansa; wannan hukunci da aka dauka ba siyasa ce kawai don ba shi da wata alaka da addini ko wani furuci dana yi.
“Don haka ina jan hankalin mabiyana da su sabunta katin zabensu, kafin zabe mai zuwa.
“Na gode Allah a kan komai, saboda ina yaki da malamai ne amma gwamnatin ta karbi fadan.
“Wannan ya nuna ba su da amsar tambayoyina.
“Ta ya gwamnati ta san ina kokarin ta da fitina? Sun san litattafan da nake amfani da su wajen kafa hujja? Shin suna ma da ilimi a kan abin da ake magana?
“Yana da kyau a ce sun duba litattafan da nake kafa hujja da su, ba ni na fada ba, suna nan a rubuce, don haka ba su min adalci ba.
“Wannan hukunci ba a yj adalci ba, duk wanda ya ji jawabin Kwamishinan Ilimi, zai fahimci cewar malaman addini da ke cikin siyasa ne suka hura wa gwamnati wuta kan ta yanke min hukunci,” cewar Abduljabbar.
Jarabawa ce —Sheikh Abduljabbar
Sai dai kuma ya ce shi mutum ne mai bin doka, don haka ba zai dauki wani mataki game da hukuncin da gwamnatin Kano ta dauka a kansa ba.
“Ina jan hankalin mabiya da masoyana da su yi hakuri, mu ci gaba da sa ido kan abin da zai faru a gaba, kuma na tabbata za mu cinye wannan jarabawar,”.
Sai dai har yanzu Gwamnatin Kano ba ta yi martani kan raddin da Sheikh Abduljabbar ya yi mata ba, amma ta ce ta yanke hukuncin ne saboda gudun tashin fitina.