Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, John Odigie-Oyegun ya ce majalisar koli ta jam’iyar ta kara musu wa’adin shugabanci ne da kyakkyawar niyya.
Shugaban jam’iyyar ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Oyegun ya kara da cewa an yanke shawarar kara wa shugabannin jam’iyyar a duk mataki wa’adi ne domin su samu damar gyara-gyare domin fuskanta kalubalen da ke gabansu musamman zaben 2019 da ke tafe.