Alhaji Sa’idu Garba Dala, tsohon Sakataren Jam’iyyar PRP ne a Dala da ke Jihar Kano kuma shi ne Shugaban Jam’iyar SDP na farko a Ƙaramar Hukumar Dala, ya yi Mataimakin Shugaban Jam’iyar PDP na Jihar Kano.
A yanzu yana ɗaya daga cikin dattijan ’yan siyasa a jihar.
A zantawarsa da Jaridar Aminiya bayan gabatar da taron addu’o’in tunawa da Malam Aminu Kano a makon jiya, ya bayyana wasu bambance-bambance da ke tsakanin siyasa a jiya da yau:
Me za ka ce game da bambance-bambancen siyasar da da ta yanzu?
Gaskiyar magana akwai bambance-banbance masu yawan gaske da zan iya ce maka ya fi tazarar sama da ƙasa.
Misali idan da ɗan siyasar da ya rasu shekara 30 zai dawo yanzu zai ce maka ba siyasa ake yi ba a yanzu, sai dai canji idan ya zo ana karɓarsa ne kawai.
Misali idan muka ɗauki lokacin Jam’iyyar PRP, a wancan lokaci ana magana ce ta aƙida kuma jam’iyya ce kaɗai take zaɓa da tsayar da waɗanda za su yi mata takara, sannan jam’iyyar ce take ɗaukar nauyin komai lokacin kamfe kamar buga fasta, riguna, huluna, baji, domin samun kuɗin shiga da za a gudanar da harkokin jam’iyya.
Haka idan za a je kamfe jam’iyyar ce ke ɗaukar nauyi da taimakon masu wadata a cikinta, haka kuma za ka ga mambobin jam’iyar suna taimakawa wajen sayen abinci da na sha kai har da kama wajen kwanciya kuma za ka ga duk garin da aka je su ma ’yan jam’iyyar suna fito da nasu taimakon kayan shimfiɗa da abinci da sauransu.
Saboda haka idan suka ci zaɓe za ka ga dole ne su yi biyayya ga shugabancin jam’iyya, kuma za ka ga suna bin tsarin mulkin jam’iyya sau- da-ƙafa.
Babu yadda za a yi ka ga zaɓaɓɓe ya tsallaka shingen tsarin mulkin jam’iyya saboda kowa ya yarda jam’iyya ce uwa da ubansa, amma yanzu abin ba haka yake ba.
Me za ka ce kan lokacin da aka yi siyasar SDP da NRC?
A lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Janar Ibrahim Babangida ya zo da jam’iyyun SDP da NRC haka abin yake kamar lokacin PRP da NPN.
Abubuwa ba su canja ba a lokacin, na shugabanci Jam’iyyar SDP a Ƙaramar Hukumar Dala kuma muka tsaida ɗan takara kuma muka yi nasara amma ina tabbatar maka babu wani muƙami da ba a teburina aka naɗa ba, kansiloli marasa gafaka, Sakataren Ilimi, Sakataran Mulki na Ƙaramar Hukuma, masu ba da shawara da sauransu.
Haka Shugaban Ƙaramar Hukumar da Mataimakinsa dukkansu mambobi ne na Kwamitin Zartarwa na Ƙaramar Hukumar Dala kuma muna iya kiransu su zo taro duk lokacin da muke da buƙata, kuma za su zo su ba da gudunmawarsu sosai.
Haka a wancan lokaci muna duba ƙoƙarin mutane da wahalar da suka yi wa jam’iyya domin naɗa su muƙamai, haka abubuwa suke tafiya gwanin sha’awa cikin girmamawa da mutuntawa. A lokacin za ka samu ’yan jam’iyya suna taimakawa sosai
Yaushe abin ya fara canjawa?
Abubuwa sun fara canjawa lokacin da aka dawo mulkin farar hula aka samu jam’iyyun PDP da APP da sauransu wanda aka yi zaɓe Obasanjo ya zama Shugaban Ƙasa.
Tun daga lokacin abubuwa suka lalace suka canja sosai aka samu bambance-bambance masu yawa da girma kusan duk abin da ake yi a da, ya zo aka rusa shi.
Waɗanne bambance-bambance da aka samu?
A wancan lokacin jam’iyya ita ce uwar kowa, ita take kashe kuɗinta ga kowane ɗan jam’iyya kuma babbar hanyar samun kuɗinta shi ne buga fasta, baji, riguna, da sauransu.
Haka idan za a je taro ’yan jam’iyya su suke tara kuɗinsu su je, amma yanzu ba haka abin yake ba idan jam’iyya za ta taro sai an ba ka kuɗin mota, abinci, masauki da sauransu wanda da a gonaki muke kwanciya idan mun yi irin wannan tafiya.
Yanzu magana ake ta kuɗi kawai idan ka san ba ka da kuɗi, to kada ma ka fito takara ko zaɓe saboda ba za ka ci ba, ka ga bambancin ke nan.
Gaskiyar magana tun a 1999 shugabancin jam’iyya ya zama mara tasiri kuma ya yi rauni kusan zan iya ce maka jam’iyyu suna da amfani ne kawai idan za su miƙa sunan ’yan takara ga hukumar zaɓe ko idan jami’an tsaro suna so za su yi taro da su saboda tsaro da kuma ba da shawarwari ga jam’iyyun.
Amma zaɓen ɗan takara duk nagartarsa da iliminsa da cancantarsa da ƙwarewarsa da son da al’umma suke masa, ba zai taɓa samun nasara ba, mutuƙar shugaba ba ya goyon bayansa. Haka abin yake a ƙananan hukumomi, jihohi da ƙasa baki ɗaya. Kuma haka abin yake a kowace jam’iyya.
Ka ga a siyasar da ana ɗaukar shawara daga shugabannin jam’iyya da ’yan jam’iyya kuma za a kira ku a yi shawara da ku, kuma a ɗauka a yi amfani da su sosai.
Amma banda yanzu, inda yanzu kafin a kira ku taro shugaba yana da abin da ya yanke yake so idan kuka zo ko ma me za ku faɗa in dai bai yi daidai da ra’ayinsa ba, to, fa ba zai yi aiki da shi ba.
Idan ka ga an ɗauki shawarka, to, ta yi daidai da ra’ayin shugaba dama ya gama tsare-tsarensa kawai jira yake idan kun tafi abin da yake so zai ɗauka sai dai ku ji an yi komai.
Duk muhimmancin maganarka idan ba ta yi daidai da tasa ba, ba za a ɗauka ba.
Ka ga shugabancin jami’iyyu ya canja ya dawo hannun Shugaban Ƙasa, gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi.
Idan kai ne Shugaban Ƙasa jam’iyya ta dawo hannunka sai abin da kake so, haka idan gwamna kake ko shugaban ƙaramar hukuma.
Me kake gani ya janyo wannan matsala?
Anawara’ayininagawatsi da tsarin mulkin jam’iyyu da son zuciyar masu mulki ya janyo haka, sai kuma kwaɗayi na wasu daga cikin shugabannin jam’iyyun.
Saboda a baya muna magana ce a kan aƙida, amma yanzu an ajiye aƙida a gefe, idan ɗan takara ya zo da kuɗi daga masu mulkin har shugabanni duka suna iya komawa bayansa saboda zai iya saye dukan daligets su zaɓe shi babu ruwansu da wanda suka daɗe a jam’iyyar suka yi mata hidima, aka raya jam’iyyar da su, aka je duba marasa lafiya da su, aka je jana’iza da su, mai kuɗin nan zai iya zuwa lokaci ɗaya ya saye dalaget kuma ya ci zaɓe.
Soboda haka shi kuma idan ya ci zaɓe ya san me ya kashe kafin a zaɓe shi, ka ga sai ya fara mayar da abin da ya kashe kafin ya fara tunanin me zai yi muku domin ya san kuɗinsa ya sa ya ci zaɓe, kuma babu lallai ya tsinana muku wani abu a mulkinsa.
Haka duk waɗanda suka yi adawa da shi sai ka ga maimakon ya jawo su jiki sai ya zama ya kore su daga jam’iyya.
Idan kuma ’yan jam’iyyar ne ya ƙi tafiya da su kuma kowane abu zai bayar za ka ga ya hana su saboda ba su yi shi ba, ba su taimake shi ba har ya kai ga gaci.
Me kake gani za a yi a koma irin lokacin siyasar da?
Gaskiyar magana gyara wannan na da wahala ƙwarai da gaske, amma duk da haka da za ka koma tsari irin na da a riƙa zaɓen ’yar tinke ko zaɓen kaida-halinka, mutane su yi layi su zaɓi wanda suke so, wataƙila za a samu ɗan daidaito kaɗan.
Domin idan ɗan jam’iya ya yarda da mutum mai mutunci kai ko shugaban aikin gayya ne ko ma mene ne shi amma an yarda da inganci da mutunci da ilimi da naƙartarsa, to idan ya zo zai shiga irin wannan zaɓe komai kuɗin mutum ba zai iya kayar da shi ba.
Don a baya an sa kuɗin kuma mutane suka zaɓi abin da suke so, amma kana ganin siyarsar yanzu ka ci, ba ka ci ba, ana haka kusan a kowace jam’iyya.
Wane kira za ka yi ga masu kaɗa ƙuri’a?
Masu ƙuri’a su zama masu hankali, su san kansu a dawo da mutunci a yarda cewa duk wanda ya zama shugaba mu yake takawa mu yarda cewa idan mun zaɓe ka ba ka tafi kawai sai wani zaɓe ya zo za mu gan ka ba. Kuma su zama marasa kwaɗayi da son zuciya. Mu ajiye soyayya a waje ɗaya mu duba cancanta mu ɗauki gaskiya mu yi amfani da ita sosai.
A ƙarshen kirana ga shugabanni su ji tsoron Allah su zama masu adalci, su yarda cewa Allah Yake bayar da mulki.
A yanzu abin da yake faruwa a ƙasar nan ya ishe su darasi ka gama mulkin ka zama ana farautarka kamar tsuntsu ana bin ka saboda cin dukiyar al’umma.