A karshen makon jiya ne Hukumar Kididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar da wata sanarwa da ta nuna cewa Najeirya ta fada masassarar tattalin arziki karo na biyu cikin shekara biyar.
Hakan na alamta irin mawuyacin halin da kasa za ta sake shiga bayan wanda take ciki.
Wannan ya sa Aminiya ta samu damar tattaunawa da Dokta Abdussalam Muhammad Kani, Malami a Sashen Tattalin Arziki na Kwalejin Sa’adatu Rimi da ke Kano, kuma mai sharhi a kan al’amuran da suka shafi tattalin arziki a kafafan watsa labari ciki da wajen kasar nan.
Mun tattauna batun Masassarar tattalin arziki da kasa ta fada, da sauran su. Ga yadda tattaunawar da kasance:
Me ake nufi da Masassarar tattalin arziki?
Tana daukar ma’anoni daban-daban wasu suna kiranta karayar tattalin arziki wasu kuma koma bayan tattalin arziki.
Kadan daga cikin ma’anonin Masassarar Tattalin Arziki sune:
Wani lokaci ne da adadin arzikin da kasa take samarwa ya ragu cikin wata shida a jere ba tare da ya farfado ba.
Idan muka duba 2020 zamu ga tattalin arzikin Najeriya ya ragu da kaso 6.1 cikin kaso dari a zango (tsawon wata uku) na biyu, a zango na uku kuma ya ragu da kaso 3.62 a cikin kaso dari.
Hukumar Bincike a kan Tattalin Arziki dake kasar Amurka (2009) ta fassara shi da cewa “wani lokaci ne da ake samun matukar raguwar hadahadar tattalin arziki da raguwar kudade a hannun mutane da karancin ayyukan yi da kasuwanci har tsawon wata shida ko shekara daya, wanda yake zuwa da matsaloli a sassa daban-daban na tattalin arzikin kasa”.
Wasu kuma suna ganin masassarar tattalin arziki da wani yanayi da ake samun raguwar kayayyaki da ayyuka da ke da alaka da kasuwanci da nunfasawar tattalin arzikinta, tsawon zango biyu ko fiye da haka.
A takaice za mu iya cewa masassarar tattalin arziki shi ne koma baya da kasa take samu a bangaren da kayayyaki da ayyuka da raguwar kudade da kudaden haraji da ayyukan yi da kayayyaki da aikace-aikace da kamfanoni suke yi da raguwar siyar da kayayyaki.
Shin fadawa a masassarar tattalin arziki bakon abu ne a duniya?
Yana da kyau mu gane cewa masassarar tattalin arziki ba bakon abu ba ne a duniya ba ki daya, domin a 1929 zuwa 1940 an yi masassarar tattalin arziki a Amurka wanda nasu sai da a karshe ya koma durkushewar tattalin arziki (depression) da ya shafi duniya gaba daya.
A 1973 zuwa 1975 ma duniya ta taba shiga masassharar tattalin arziki.
Haka nan a shekara ta 1982 masassarar tattalin arziki ta faru.
A baya-bayan nan an yi masassarar tattalin arziki a duniya daga 2007 zuwa 2008 (world greatest recession), wadda har sai da ta kai wata 18 kafin a fita (daga Disambar, 2007 zuwa Yunin, 2008).
Ko a yanzu wasu daga cikin manyan kasashe suna fama da wannan masassarar a halinzu.
Me ya janyo duniya ta fada cikin masassarar a wancan lokacin?
Abubuwan da suka janyo afkuwar hakan a 2007 zuwa 2008 sun hada da ba da basussuka sasakai, zuba hannun jari a inda bai dace ba da rashin gogewar hukumomin da suke kula da harkar bashi.
A yanzu haka da muke magana kasar Jamus da Canada da Faransa, Afirka ta Kudu da sauransu suna cikin masassarar tattalin arziki.
Wadanne alamomi ne ke nuna cewa kasa za ta shiga masassarar tattalin arziki?
Alamomin da suke nuna alamun kasa za ta shiga masassarar tattalin arziki sune:
- Matukar yawaitar rashin aikin yi da cin karamar riba ga manyan masana’antu.
- Gazawar wadanda suka ci basussuka wajen biya.
- Tashin goron zabo na farashin kayayyakin da mutane ke bukata yau da kullum
- Gazawar kamfanoni da manyan masana’antu wajen samar da ayyuka
- Samun matsala a hadahadar kasuwancin gidaje da na hannun jari.
- Da kudaden da ya kamata ai kasuwanci da su ana amfani da su wajen bukatun yau da kullum.
- Sai raguwar kayayyaki da ayyuka.
Me ya jawo Najeriya ta shiga masassarar tattalin arziki?
Dalilan da suka sa Najeriya ta shiga masassarar tattalin arziki sune kamar haka:
- Karyewar farashin danyen mai a kasuwar duniya da raguwar danyen mai da Najeriya ke hakowa.
- Yawaitar basussuka
- Karuwar kudaden da ake kashewa wajen gudanar da gwamanti
- Karancin kudade a cikin asusun ketare
- Sai raguwar zuba hannayen jari daga ketare
- Yawaitar kudaden ruwa a bankuna
- Da karyar da gwiwar masu zuba hannayen jari
- Uwa uba rashin isashshen tsaro
- Da rashin baza koma a bangaren noma da masanaantu
- Dogaro da kudaden da ake samu daga danyen mai
- Rashin hanyoyin samun kudaden waje
- Da kuma rashin yin tanadi a lokutan da ake samun rarar kudin danyen mai.
Ya ake gane kasa ta shiga masassarar tattalin arziki?
Ana gane kasa ta shiga masassarar tattalin arziki idan kayayyaki da kasa take samarwa da ayyuka da ake yi masu alaka da kasuwanci da nunfasawar tattalin arzikinta suka ragu cikin wata shida a jere ba tare da sun karu ba ko sun farfado ba.
Tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa da sauran al’umma wa abin zai fi shafa?
Matsala ce da take shafar kowa da kowa. Idan muka dauki ma’aikata, tana kawo musu raguwar kayayyakin da albashinsu zai iya siya saboda karuwar hauhawar farashi da ake samu a lokacin.
’Yan kasuwa kuma tana shafar kudaden da suke samu. Bayan haka adadin kudin da suke kashewa domin gudanar da kasuwanci zai karu, sannan akwai yiwuwar cinikin da suke yi zai ragu.
Manyan kamfanoni da ke sarrafa kayayyaki su ma matsalar tana shafar su domin dole su rage adadin abubuwan da suke sarrafawa duba da yadda yanayin yake zuwa da rashin kudade a hannun mutane. Raguwar samar da kayayyaki da suke yi yakan sa su kori ma’aikata.
Ita gwamnati tana yin asarar kudaden shiga idan aka shiga masassarar tattalin arziki.
Yana hafar da gwamnati ta waiwayi manyan ayyukan da take kashe kudi a kansu domin dakatar da su tunda babu kudaden shiga na cikin gida.
Shi kuma dakatar da ayyukan da gwamnati take yi ya kawo karuwar rashin aikin yi.
Bayan wadannan, wadansu abubuwan da masassarar tattalin arziki take haifarwa a Najeriya sun hada da:
Karuwar basussuka da karayar arzikin mutane da bankuna.
Faduwar darajar Naira da rufe masana’antu da kamfanoni.
Karancin bukatar kayayyaki.
Tun bayan samun ‘yancin kai sau nawa Najeria ta shiga masassarar tattalin arziki?
A iya sanina sau uku Najeriya ta shiga masassarar tattalin arziki:
Na farko ya faru a 1987 wanda a zangon farko tattalin arzikin Najeriya ya ragu da kaso 0.5 cikin dari sannan a zango na biyu na wannan shekarar ya sake raguwa da kaso 0.82 cikin dari.
Bayan wannan ya sake faruwa a 2016 zuwa 2017 wanda sai da a ka yi wata 15 a ciki kafin Najeriya ta fita a zango na biyu na 2017.
Sai kuma yanzu da ya sake faru wanda a zango na biyu da ya gabata tattalin arzikin Najeriya ya ragu da kaso 6.1 cikin dari yanzu kuma a zango na uku ya ragu da kaso 3.62 cikin dari.
Wannan masassarar tattalin arziki da aka shiga yanzu ita ce mafi muni domin a baya ba a taba samun lokacin da tattalin arziki ya ragu da kaso 3.62 cikin dari ba, sai yanzu ko a 2016 ya ragu ne da kaso 1.9 cikin dari, a 1987 kuwa da kaso 0.82 ya ragu.
Wadanne darussa ya kamata Najeriya ta koya daga masassarar tattalin arziki da suka faru a baya da yanzu?
- Ci gaba da dogaro da kudaden da ake samu daga fetur ba abu ne da zai haifar wa Najeriya da mai ido ba.
- Yin tanadi a lokacin wadata abu ne mai matukar mahimmanci.
- Samar da masana’antu ko zuba musu hannnun jari da kashe kudade don manyan ayyuka kamar gina makarantu da asibitoci da sauransu abu ne mai matukar mahimmanci.
- Janye kudade, rashin tsai da hauhawar farashi da barin Naira ta nema wa kanta daraja a kasuwa ba sa taimakawa wajen dakile masassharar tattalin arziki.
- Rufe iyakokin kasa, janye tallafin mai, da wutar lantarki da na kayan noma ba tare da yin tanadin abin da zai rage wa talaka radadi ba, abubuwane da ke kara yawaitar hauhawar farashi da rashin aikin yi a lokacin masassarar tattalin arzikin kasa.
-
Shin gwamnati za ta iya aiwatar da kasafin kudin da ta yi?
Abu ne mai wahala domin masassarar tattalin arziki tana zuwa da raguwar kudade da kasa take samu, don kasa ba a iya aiwatar da shiba kamar yadda aka tsara.
Wadanne hanyoyi za a bi don farfado da tattalin arziki kasa?
- Rage kudaden ruwa da bankuna ke caza don farfado da kanana da matsakaitan masanaantu.
- Ci gaba da samar da zaman lafiya a yankin Neja Delta.
- Ci gaba da kashe kudade don gudanar da manyan ayyuka.
- Hana shigo da kayayyakin da masanaantunmu za su iya samarwa a Najeriya.
- Kokari wajen tabbatar da cewa darajar Naira ba ta ci gaba da faduwa ba.
- Kulla alaka da sauran kasashe don bunkasa tattalin arzikin kasa.
- Sannan a samar da wadatacciyar wutar lantarki.
- Da kuma baza koma a bangaren noma, masana’antu da kamfanoni.
- Ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa.
- Rage kudaden haraji da kamfanoni da masana’antu suke biya.
- Bayar da tallifin kudade ga kanana da matsakaitar sanao’i.
- Samar da wadatattun kudade ga masana’antun da suke so su shigo da abubuwan da suke sarrafawa daga waje.
- A fadada komar kudaden harajin da gwamnati take samu.
- Sai kuma daga wa’adin biyan kudade da masu masana’antu da kamfanoni suka karba daga bankuna.