Kungiyar Dattawan Arewa ta ce yankin ba ya adawa da sauya fasalin Najeriya, amma ya fi ganin a mayar da hankali da kwazo wajen magance matsalolin kasar.
Kakakin Kungiyar, Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a Taron Tattaunawar Daily Trust karo na 18 in da ya ce, “Mu ’yan Najeriya ne kuma muna ganin Arewa ba ta samun biyan bukata, babu wanda ke samun biyan bukata.
- Gwamnan Zamfara ya nemi Sheikh Gumi ya yi wa ’yan bindiga wa’azi
- Gobara ta tashi a masana’antar rigakafin COVID-19
- An cafke jami’in tsaron ABU da ke hada baki ana garkuwa da mutane
“Mun yi amannar cewa sai an gyara kasar, kuma dole sai kowa ya shiga za a gyara ta ta kowane bangare a kuma gano abin da zai amfani kowa.
Ya bayyana cewa Arewa ba ta kin a sauya fasalin kasar ba, kuma ba za ta yi adawa da hakan ba sabota ta gamsu cewa kasar na bukatar gyara.
“A shirye muke mu tattauna da kowa daga ko’ina kuma a kowane lokaci a kan wanna batu.
“Amma babu wanda kuma zai tilasta mu amince da duk abubuwan da wasu suka kawo,” inji Dokta Hakeem a taron wanda takensa na bana shi ne: Sauya Fasali: Saboda me? Yaushe? ta Yaya?
Ya ce yayin da Najeriya ke bukatar gyara, wajibi ne a yi wa lamarin kallo na natsanaki, a tunkare shi ta yadda zai amfani dukkannin bangarorin kasar.
“Shi ya sa ni ba zan tsoma baki a batun neman ci gaba ko sauya tsarin jihohi 36 da ake da su ba.
“A baje Najeriya a faifai a gano matsalolinta, shi ne abin da ya kamata,” inji shi.
Dokta Hakeem Baba-Ahmed ya kara da cewa matsaloli biyu ne ’yan Najeriya ke da shi da batun na sauya fasalin kasar.
Ya ce na farko shi ne wasu sun dauke shih a matsayin wani makami, ba tare da sun fahimci ma’anarsa, yadda za a yi shi da kuma kyawawan abubun da ya kunsa ba.
Na biyu kuma shi ne yadda manyan mutane ke baza karairayi game da yankin Arewa a batun na sauya fasalin kasar.
Amma ya ce, “’Yan Arewa ba su taba nisantar wani abu bisa jahilci ba.”