✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya kamata gwamnati ta yi kan hana almajiranci a Najeriya – Ibrahim Dahiru Bauchi

Kwanaki kun yi taron Majalisar koli ta ’Yan darikar Tijjaniyya a Najeriya a nan Bauchi wani hali ake ciki a yanzu? Alhamdulillahi dalilin da ya…

Kwanaki kun yi taron Majalisar koli ta ’Yan darikar Tijjaniyya a Najeriya a nan Bauchi wani hali ake ciki a yanzu?

Alhamdulillahi dalilin da ya sa muka tara Shehunanmu da Halifofinmu na darikar Tijjaniyya, ita wannan gwamnati mai ci da nufinta na alheri ta kira mu wani taro a karkashin Hukumar Kula da Ilimi a Matakin Farko (UBEC), suka ce suna son za su tallafa wa almajirai da malamai, suka kira mu muka je taron. Mu mun je ne a madadin ’yan darikar Tijjaniyya, gwamnati ta ce tana so ta ga adadin makarantunmu da yawan almajiranmu domin kullum ana maganar almajiranci tana so ta taimaka, amma ba zai yiwu ba sai ta tuntubi masu makarantun. Shi ne muka ce su ba mu lokaci in Allah Ya yarda bayan Sallah za mu tara malamai mu hadu domin mu hada wadannan makarantu, mu bai wa gwamnati dama ta yi mana taimakon da ta yi niyya, mu ma mu taimaka mata yadda za ta samu sukunin da za ta yi shi cikin sauki, baki dayanmu Allah Ya taimaka mana cikin wannan lamari.  

Kuma babban abin da muka cimma shi ne an farfado da Majalisar koli ta Malaman darikar Tijjaniyya kuma majalisar za ta ci gaba da aiki daga nan za mu harhada duk matsalolin makarantun da sauran al’amura domin mu yi maganinsu. Kuma ka ga mun yi taro na farko kwanakin baya a Bauchi, in Allah Ya so kuma yanzu muna kokarin yin taro na gaba a Jihar Kano.

Kun samu kididdigar makarantun da kuke da su?

Har yanzu dai muna tattarawa domin akwai wadanda suka zo taron ba tare da sun san cewa za su kawo adadin makarantun da suke karkashinsu ba, saboda haka muka ba da lokaci domin su kawo, mu hada kafin mu ga inda muka tsaya. Kuma wannan taro ya samu nasara domin kamar yadda ka ji sama da shekara 50 rabon da a yi irin wannan taro da zai tara dukan malaman nan, ka ga Maulana Sheikh Sheriff Ibrahim Saleh Al-Hussein ya turo wakilinsa haka ma Khalifa Isyaka Rabi’u, gidan Malam Sani Kafanga da gidan Shehu Maihula da gidan Shehu Abulfathi Maiduguri da gidan Sheikh Modibbo Jailani a Yola dama dukan wani gida na shehunan darikar suna wurin taron. Alhamdulillahi haduwarmu baki daya kawai ya isa nasara mai girma, tunda kowa ya zo kididdigar makarantu kuwa kamar ya samu domin ga masu makarantun da almajiran nan. Kuma ka ga komai yana da dalilinsa, nufin gwamnati na alheri shi ya sa muka tara wannan alheri saboda haka ita ma gwamnati za mu yi mata addu’a sannan za mu roki Allah Ya bai wa Shugaban kasa Lafiya.

Wane irin taimako gwamnati ta yi muku alkawari?

Mu dai gwamnati ta ce mu ba ta yawan makarantun da muke da su, ita kuma ta san irin taimakon da za ta yi mana. Watakila ta ce za ta zo ta giggina mana ajujuwa da ofisoshi da dakunan taro, mun ji dai an ce za ta tallafa wa malamai a cire wadansu daga ciki ana ba su dan alawus-alawus, amma dai gwamnati ce ta san me za ta yi mana kamar yadda muka fada a wajen taron.

Aganinka me ka sa iyayen yara fitar da su daga makaruntun boko suna sa su a na almajiranci?

Kamar yadda muka fada a wajen taron cewa a Najeriya ta Arewa dalilin da ya sa iyaye suke fitar da ’ya’yansu daga makarantun boko suna sa su a makarantun addini shi ne saboda iyaye suna ganin makarantun boko babu ilimin addini a cikin manhajarsu. Don wani ya ba mu labarin cewa a tsarin manhajar boko in ka gama makarantar firamare ba ka gama daga Alam Tara zuwa Nasi ba. Ka ga kuwa mu a makarantunmu muna da mahaddacin Alku’rani mai wadannan shekarun da ake gama firamare. Lokacin da muka zauna da su muka fada wa gwamnati cewa makarantun da ta gina na Tsangaya ta ba mu mu in Allah Ya yarda kafin yaro ya gama firamare zai haddace Alkur’ani a ciki. Mu a makarantun Sheikh dahiru Usman Bauchi cikin shekara hudu yaro yake haddace Alkur’ani saboda haka in muka samu yaro cikin shekara shida na firamare zai samu ilimin firamare da kuma haddace Alkur’ani. Don haka da gwamnati za ta sanya ilimin addini a cikin manhajar makarantunta da ba yaron da za ka gani yana yawo a kan titi. Saboda ba ya da amsa domin duk abin da ya ce za a ce masa ga makarantar gwamnati inda ake haddace Alkur’ani me ya sa ba ka je ba? Ka ga ta haka dole kowa ya tafi makaranta ita wannan gwamnatin nufinta ke nan Allah Ya tabbatar da alherin abin da ta yi niyya.  Ko a yanzu haka cikin makarantunmu muna karantarwa har da ilimin boko, makarantar da muke hadawa da ilimin boko shekara shida ake haddace Alkur’ani, wadanda ba su da ilimin boko kuma shekaru hudu ne. Ka ga wannan kokari namu na kashin kanmu ne muke yi a gida, yaya kake gani idan gwamnati ta shigo? Abin zai yi kyau sosai in ta shigo iyaye zai zama ba su da wani zabi sai dai su kai ’ya’yansu makaranta in ba su yi ba za a iya kama mahaifin yaro a daure. Tunda yanzu makarantun ana koyar da Alkur’ani da kuma boko sai gwamnatin ta taimaka.