✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Abin da ya jawo zaman Hausawa a Enugu’

A 1906, labari ya bayyana cewa ana aikin jirgin kasa daga Kano zuwa Kudu; Mutane sun fito daga kauyuka, suka zo har Kano don ganin…

A 1906, labari ya bayyana cewa ana aikin jirgin kasa daga Kano zuwa Kudu; Mutane sun fito daga kauyuka, suka zo har Kano don ganin abin da yake faruwa.

Suleiman Sale, wani saurayi Bahaushe na cikin wadanda suka yi tururuwa zuwa birnin Kano, kuma ya taka rawa wajen aikin shimfida layin dogon da ke bukatar shafe awanni masu yawa a kowace rana domin yin aikin.

Akwai irinsa da dama da suka yi aikin fadada layin dogon wanda ya ratsa garuruwa da dazuzzuka da kwarurruka da sauransu.

Wannan sabon abu ne kuma mutane da yawa sun shiga an yi aikin da su, inda harkokin tattalin arziki suka sa aikin ci gaba da gudana.

Kasa mai albarka

Kano tana da kasar noma mai albarka kuma tana samar da dimbin amfanin gona a kowace kaka.

Hakan ya sa ya zama dole a samar da tsarin da za a yi amfani da shi wajen kai kayan amfanin gonar da sauran kayayyaki masu daraja daga Kano zuwa gabar teku don jigilar su zuwa Turai.

Don haka gwamnatin mulkin mallaka ta tsara yin titin jirgin kasa a tsakanin Arewa da Kudu, wanda sassansa suka yi reshe daga babban layin don isa ga al’ummomin da suke makwabtaka da shi.

Yin amfani da fasahar kere-keren zamanin, sai aikin ya fara kusantar Kudu, duk da yake aiki ne mai wuya.

Bincike a manhajar Google ya nuna cewa, layin dogo da ake magana a nan na iya kasancewa layin dogo daga Kano zuwa Fatakwal wanda aka fara amfani da shi a 1914.

Ma’ana, an fara gina layin dogon a 1906 lokacin da Sale ya ce ya shiga cikin masu aikin shimfida layin dogon daga Kano.

Daga karshe Sale ya isa Enugu, inda ya zauna ya yi aure, kuma shi ne kakan Suleiman Haruna Sule, Sarkin Hausawan Enugu na yanzu.

Ya kasance jagaba a harkar kasuwancin shanu, kuma ta hanyarsa da wasu ’yan kasuwa Hausawa da dama irin su Baba Girei da Baba Enugu suka shahara, aka fara samun bunkasar cinikin shanu a tsakanin Arewa da Kudu.

Ya zauna a Unguwar Coal Camp a Enugu, inda nan ne asalin mazaunin masu hakar ma’adinai da suke aiki a ma’adanar kwal, ya kuma mallaki gidaje da yawa a yankin.

Yanzu haka jikan Sarki Sule, wato Sarkin Hausawa Enugu na yanzu, Sarki Sulaiman shi ma yana zaune ne a Coal Camp, yana ci gaba da zamantakewar iyali.

A lokacin da na isa fadarsa ana ta shagulgula.

Bayan Sarkin ya dawo daga ziyarar da ya kai, makonni kadan bayan nada shi a matsayin sabon Sarkin Hausawa, makwabta ma ba a bar su a baya ba wajen bayyana farin cikinsu.

Shanu 1,000

Baba Ali ya isa Enugu ne a karshen Yakin Basasa.

Shi ne Shugaban Kasuwar Karar. A cewarsa na iso Enugu ne a 1970.

Ya ce, “Na fito daga Jihar Adamawa.

“A lokacin kwata ta farko tana a inda ake kira Artisan ne.

“Daga nan muka koma Sansanin Kwal, daga can muka koma Awkunanu, sai wata Gariki, daga nan muka dawo nan, inda fadada birni ya riske mu, shi ya sa muka matsa.”

Da yake magana kan sauye-sauyen da ake samu cewa ya yi, “Ba za ku iya kwatanta lokacin baya da yanzu ba, domin a wancan lokacin ba kawai tireloli ke kawo shanu ba, jiragen kasa ma suna kawo shanu, haka daga Kamaru a wancan lokaci mutane kan taho da shanu har zuwa Enugu a kasa.

“Daga Adamawa suke tsallakowa zuwa Binuwai da Nkalagu kafin su zo nan Enugu.

“Wannan ita ce hanyar da suke amfani da ita.

“Ana yin wata daya zuwa kwana 40 kafin a iso a kafa daga Kamaru zuwa Enugu tare da shanun.”

Ya ce wani lokaci a shekarun 1970 an yanka shanu dubu daya a Unguwar Garki da kewayenta a rana daya, ya ce yanzu abubuwa sun sauya.

Mun tashi zuwa Otukpo

An haifi Shu’aibu Musa a garin Enugu a 1951 kuma ya fito ne daga zuriyar Sarkin Hausawa.

Ya yi bayani a kan sana’ar shahararren kakan nasa da kuma ci gaban al’ummar Hausawa da suka zo daga Chadi da Kamaru da Maiduguri da jihohin Yobe da Filato.

Da yake sharhi a kan Yakin Basasa ya ce yakin ya shafi cinikin shanu, ya kuma shafi habaka da bunkasar al’ummar Hausawan yankin.

“A wancan lokaci dukkanmu mukan yi tattaki zuwa Otukpo a Jihar Binuwai, kasancewarta iyakar Arewa da Kudu maso Gabas.

Dokar zaman gida

“Ana iya samun dimbin al’ummar Hausawa a Ugwoba da Mil 9 da Sabuwar Garki da Sabuwar Kasuwar Artisan da Titin Owerri da Kasuwar Akwata da Coal Camp da Abakpa da Obollo Afor da Emene da kuma Agbani,” in ji shi.

Suleiman Haruna Suleiman shi ne Sarkin Hausawan Enugu, ya yi tsokaci a kan umarnin kungiyar IPOB na zaman gida, da illarsa ga al’ummarsa

“Ba za mu iya yin komai ba game da lamarin.

“Al’ummar Hausawa a nan na zaune cikin tsoro saboda dokar zaman gida ta kungiyar IPOB da take aiki a ranar Litinin.

Litinin ita ce ranar da muka saba fara kasuwancinmu, idan kun zo kasuwar shanu ranar Litinin, babu mai zuwa, hatta Hausawa mazauna garin suna zuwa nan ne don tsaro, ko kuma su kasance da ’yan uwansu.

“Idan kuna wurin da ba kasarku ba, dole ne ku bi dokokinsu,” kamar yadda ya bayyana.

Asarar Naira miliyan 20

Sarki Suleiman ya yi karin haske kan asarar kudi da dokar zaman gida ta haifar.

Ya ce, “Ba ma yanka shanu a kasuwa ranar Litinin a yanzu.

“A duk rana kuma muna yanka shanu sama da ashirin, wanda akalla kudinsu zai kai Naira miliyan ashirin, ke nan ana asarar Naira miliyan 20 a duk ranar Litinin saboda dokar zaman gida.

Sarki Suleiman ya kara da cewa al’ummarsa ba su cika sha’awar ilimi ba, domin da yawa sun yi imani cewa dalilin zuwan su Enugu shi ne kasuwanci.

Ba sa son sayen filaye da gina gidaje, domin sun yi imani za su kasance a cikin birnin na dan lokaci kadan ne.

Ya ce “Muna kokarin ilimantar da su ta hanyar gaya musu cewa muna nan tun 1906.

“Kakana ya zo Enugu tare da masu aikin jirgin kasa, ma’aikaci ne daga Arewa daga Jihar Kano.

“Wannan shi ne abin da mahaifina ya gaya min.

“A nan muka sauka a Sansanin Kwal, domin Sansanin Kwal shi ne wuri mafi tsufa a Enugu a lokacin, a nan aka haifi mahaifina.”

Suleiman ya ce wasu Hausawa duk da an haife su a Enugu sun fara komawa Arewa.

Ya ce “Mako biyu da suka wuce na je Kano daurin aure, wani dan uwana ya yi aure kuma a wajen bikin akwai Hausawa da dama da suke jin harshen Ibo.

“A Enugu aka haife su kuma suka koma Kaduna da zama.”

’Yan ci-rani

Sarki Suleiman ya ce, “Su ne wadanda suke barin garuruwansu su je wani gari neman aikin yi domin su samu wani abu, duk ana yin haka ne a lokacin rani a Arewa.

“Idan sun zo nan neman aiki suna samun kudi fiye da Arewa.

“Don haka, wasu daga cikinsu suke yanke shawarar zama a nan dindindin harsu yi aure.”

Ya ce  “Duk Hausawan da suke Kudu maso Gabas, sun samo asali ne daga ci-rani.

“Idan ka tuna kakana ya zo nan yana aikin shimfida titin jirgin kasa daga Kano, wannan ne ci-rani. Don haka mun iso nan ne dalilin ci-rani.”

Baba Wakili kuwa cewa ya yi akwai’yan ci-rani sama da 300 a Garki, wadanda suka fito daga jihohin Bauchi da Jigawa da Adamawa da Yobe da Gombe da Kano da Zamfara da Katsina da Kaduna.

Wakili shi ne Shugaban kungiyar ’Yan Ci-rani a Garki.

A cewarsa, “Muna komawa ne a watan Mayu lokacin da aka fara damina a Arewa, inda muke shuka amfanin gona, muna yin girbi sannan mu komo nan Kudu maso Gabas a watan Janairu.

Nakan je Damboa a da Ogbonnaya

Chuka Ogbonnaya ya kwashe sama da shekara ashirin yana sayar da shanu a Garki.

Da yake bayani a kan tafiye-tafiyensa zuwa sassa masu nisa na Arewa irin su Maiduguri da Bauchi, inda yake sayo shanu ya dawo da su Enugu, ya ce, “Kafin zuwan Boko Haram nakan je wurare da dama a Arewa kamar Bauchi da Mubi da Maiduguri da Jigawa da Taraba in sayo shanu.

“Kuma ina zuwa Damboa, amma ba zan iya zuwa can a yanzu saboda rashin tsaro.

“Akwai ’yan kabilar Ibo da dama da ke kasuwancin shanu.”

Dillalan kifi 300

“Akwai dillalan kifi sama da 300 a wannan kasuwar, an haife ni a nan kuma ina jin harshen Ibo,” in ji Abdullahi Garba, Sakataren kungiyar Dillalan Kifi a Kasuwar Akwata.

Ya ci gaba da cewa “Ni Bahaushe ne daga Jihar Kano, daga Dawakin Kudu.

“Akwai Hausawa da yawa da suka zo nan daga Kano, ban san adadinsu ba, amma muna da yawa a nan.”

Nasiru Shehu shi ne Shugaban Hausawa Dillalan Albasa, a wani bangare na kasuwar, ya ce ana kawo albasa daga jihohin Kaduna da Sakkwato, kuma tirelar albasa cikakkiya tana daukar buhu 250.

Da yake tsokaci a kan wuraren ajiya, ya ce “Za ku iya adana albasa a Arewa, amma a Kudu saboda yanayin ruwa ba za a iya adana ta ba, domin albasa ba ta son ruwa da zarar ruwan sama ya sauka a kan albasa, tana saurin lalacewa.

Zuwa ofishin ’yan sanda

Sarki Suleiman ya kuma yi magana a kan matsalolin da matasan Hausawa suke fuskanta a lokacin da suke zuwa Enugu daga Arewa.

A cewarsa, “Ina yawan zuwa ofisoshin ’yan sanda ina belin mutanena.

“’Yan sanda za su kama wani saboda ’yar wukar da ke daure a kugunsa.

“Wadannan ’yan ci-rani kullum suna rike da wukake saboda dabbobin da suke yawo da su a daji.

“Idan dabbobin suka kasa, za su yanka domin ba ma cin dabbar da ta mutu, shi ya sa suke yawo da wukakensu.

“Wani lokaci nakan je ofisoshin ’yan sanda sau da dama a wata guda, a wasu lokutan ana kai yaran kotu ba tare da saninmu ba.”

Sun sayi filaye, su gina gidaje

“Watakila sarakunanmu na Hausawa na baya ba su yi magana a kan wannan ba, watakila kuma don mun yi sake ne.

“Hausawa na farko da suka zo Enugu sun yi aiki tukuru, sun sayi filaye sun gina gidaje ta ko’ina.

“Kuma a wancan lokacin zai yi wuya a ce su je wani yanki na musamman,” in ji Sarkin Suleiman, yayin da yake tsokaci a kan rashin uguwannin Hausawa a Enugu kamar yadda ake samu a wasu jihohin da ke makwabtaka da Enugu a yankin Kudu maso Gabas.

Ina jin kare-karen harshen Ibo da dama

Mohammed Salisu yana sayar da awaki ne a Sabuwar Garki, ya bayyana yadda dokar zaman gida ta shafi cinikin awaki.

“Ya ce dokar, “tana illa sosai ga kasuwanci.

“Ranakun Litinin su ne ranakun da aka fi ciniki.

“Yanzu ana fara kasuwa ce a ranar Talata; Mutanenmu suna kallon zaman gida a matsayin wata alama da ke karfafa mutane su koma Arewa.”

Ya kuma ce, “Mun yi imani cewa duk abin da ya faru, za mu sha wahala kuma mu tsira tare da ’yan asalin kasa.

“Halin da nake a yanzu daidai ne da na ’yan asalin yankin saboda a nan aka haife ni, kuma ina jin kare-karen harshen Ibo daban-daban da ake magana da su a nan Enugu da kuma Abakaliki.”

Salisu, wanda yake da digiri a kan Tarihi da Nazarin Kasashen Duniya, ya yi fatar samun jarin da zai yi amfani da shi wajen bunkasa kasuwancinsa na sayar da awaki.