Gwamnan Sakkwato, Dokta Ahmad Aliyu ya bayyana ƙarara cewa gwamnatinsa ta kasa cika alƙawarin da ta yi wa ma’aikatan gwamnatin jihar kusan shekara ɗaya kenan.
Gwamnan ya bayyana hakan a yayin bikin Ranar Ma’aikata da aka gudanar a makon da ya gabata.
Ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a biya kuɗin goron sallah babba na naira dubu talatin-talatin da ya ba da umarnin a bai wa ma’aikatan ƙananan hukumomi amma wasu suka yi sama da faɗi da kuɗin.
Gwamna ya bai wa ma’aikata tabbacin nan ba da jimawa ba za raba kuɗin ga waɗanda ke da haƙƙi kamar yadda tsarin biyan kuɗin sallah ya kasance a shekarar da ta gabata.
A yayin bikin sallah babba na shekarar da ta gabata ce gwamnan ya amince a baiw a kowane ma’aikaci a jihar naira dubu 30 don sauƙaƙa musu bukin sallah babba, sai dai har zuwa yanzu da yawan ma’aikatan da malaman firamare ba su samu nasu ba.
Sai dai baya aka sanar da ma’aikata da malaman ƙananan hukumomin cewa an yi sama da faɗi da kuɗin da aka ce a ba su.
Gwamna ya bayyana cewa ya ba da umarnin a fitar da miliyan 500 duk wata haɗi da wasu naira miliyan 300 domin biyan waɗanda suka yi ritaya daga shekarar 2023 zuwa yanzu.
Ya ba da sanarwar ƙaddamar da shagon sauki na Amadun Alu domin sayar da kayan masarufi a cikin sauƙi ga ma’aikata.
Ya yi kira ga ma’aikata su zama masu kula da aiki da sadaukarwa domin ci gaban jihar.
A jawabinsa, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta jihar, Abdullahi Aliyu ya yaba wa gwamnan kan fifita walwalar ma’aikata.
Shugaban ya gode wa gwamna kan biyan mafi ƙarancin albashi na naira dubu 70 ga ma’aikata.
“Mun samu farin ciki ƙwarai musamman yadda na jagoranci tantance ma’aikata domin fitar da na bogi a tsarin biyan ma’aikata.”
A cewarsa, kwamitin ya samu ci gaba sosai, inda aka cire ma’aikatan bogi da ke cin kuɗin mutane ba da haƙƙi ba.
Ya ce ƙungiyarsu za ta ci gaba da taimakon gwamnati don samun nasara.
Masana a jihar suna ganin gwamna bai da wani dalilin rashin biyan kuɗin ga ma’aikata, lamarin da suka bayyana a matsayin kasawa ce ƙarara daga ɓangaren gwamnatinsa.
Sun bayyana cewa “gwamnati ta kasa ne kawai ba don haka ba umarnin gwamna ba wasa ba ne da har wani zai kasa biyayya gare shi, hakan ya sa gwamnan da kansa bai bayar da wani dalili ba saboda ya kasa ga cika alƙawarin da ya ɗauka.”