Jarumar masana’antar fim din Kannywood, Ummi Rahab, ta bayyana bangarenta na dambarwar da ke tsakaninta da tauraro kuma ubangindanta, Adam A. Zango.
Ga yadda tattaunawarmu ta kasance da jaruma Ummi Rahab:
Ko za ki iya gaya mana alakarki da jarumi Adam A. Zango?
Adam A. Zango tamkar uba ne a wajena duk da abubuwan da suka faru a tsakaninmu.
Saboda ya taimake ni kwarai da gaske. Shi ne jigo wajen mayar da ni abin da na zama.
Shi ya sa har yanzu nake ganin girmansa a matsayin jagora, wanda ya nuna min hanya.
Amma wannan ba zai hana ni in ci gaba da neman cikar burina na rayuwa a gefe ba.
Yanzu za a iya cewa babu zaman doya da manja a tsakaninku?
Ai na riga na yi bayani, ni uba na dauke shi kuma har yanzu a haka yake.
Ina ganin girmansa amma hanyar jirgi daban da ta mota.
Shin da gaske ne ya cire ki daga wani fim dinsa?
Gaskiya haka ne, amma wannan ba komai ba ne, tunda yana da iko ya saka ko ya cire wanda ya ga dama a fim dinsa.
Babu shakka ina daga cikin wadanda aka shirya za su fito a cikin fim dinsa ‘Farin Wata Sha Kallo’ da ake nunawa a YouTube, amma ban san dalili ba sai suka cire ni.
Ni wannan bai dame ni ba, tunda har yanzu ina nan a jaruma da za ta ci gaba da fitowa a fina-finai.
Kin samu wata damuwa da aka cire ki daga fim din?
Sam. A kan me zan damu? Abin da ba roka na yi ba, ni ba ni da wata matsala tunda zan ci gaba da yin fim.
Akwai wani rikici a tsakaninki da Zango a baya?
In dai kana bibiyar kafafen sada zumunta, to ka san abin da yake faruwa.
Da farko ban yi niyyar magana a kan lamarin ba, saboda dan sabani ne na cikin gida aka yi ta terere da yamadidi da shi.
Da yake Allah Ma jikan bawanSa ne sai ga wadansu mutane can daban da ko saninsu ban yi ba suka zo suna ta kare ni.
Kai har sai da manyan mutane daga ciki da wajen Masana’antar Fim suka saka baki a ciki.
Wannan ne ya sa ka ga na tura wasu sakonni a kafafen sada zumunta, amma ni ban yi nufin cin mutuncin kowa ba.
Shin da gaske ne kin fada wa wata kawarki cewa Adam Zango kishi ne yake damunsa?
Haka ne, na fada wa wadansu aminaina cewa Adam Zango yana kishi ne saboda na fara soyayya da wadansu samari, ya yi kokarin ya hana ni, amma na nuna masa cewa shi fa uba ne.
Da ya ga ba zan yarda da ra’ayinsa ba shi ne ya fara bore.
Amma ya ce ya bata da ke ce saboda kin zama mai kunnen kashi?
Sam ba haka ba ne, gaskiyar lamarin shi ne ya ce in aure shi ni kuma na ki yarda, kada ka dada kada ka kara.
Na yi kokarin ya fahimce ni amma ya ki.
Kuma ai al’umma sun san dabi’arsa ta son auren ’yan mata da yake aiki da su. Ni kuma gaskiya ba haka nake ba.
Tun fa ina ’yar mitsitsiya nake tare da shi. To yaya zan auri wanda yake a matsayin babana?
A kan maganar kunnen kashi kuwa ai kowa ya san Zango bai shahara da yayata sha’anin kula da addini da al’ada ba, kai akwai lokacin da ya sa ni na sanya wata sutura da ta jawo min bakin jini sosai, masoyana suka yi ta caccaka ta cewa kayan ba su dace ba.
Har sai da iyayena suka ce idan na kara sanya irinsu za su hana ni yin fim kwata-kwata.
To yanzu ka fada min wanda ya yi wannan shi ne za a ba wa amanar tarbiyya da har zai ce wani ba ya da kamun kai? Amma dai Allah Ya raya mu gaskiya za ta bayyana.
Kuma ana cewa kin gayyato ’yan tayin fada?
A’a, ban gayyato kowa ba, kawai dai masoyana ne suka ga ba a kyauta min ba, su kuma suka rika kare ni. Wannan shi ya jawo jama’a suka shigo aka yi ta ce-ce-ku-ce.