Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban amsoshin wasu daga cikin tambayoyin da masu karatu suka aiko.
Daga Hajiya Larai zuwa ga magidanta da iyayensu mata!
Malama Nabila ni uwar maza ce, ’ya’yana bakwai maza kuma ba ni da ’ya mace ko daya, amma mai ’ya’ya mata ba za ta nuna mini komi ba wajen samun kulawa da gata qila sai dai ma in nuna mata.
- Tambayoyin Duniyar Ma’aurata (10)
- Attahiru ya mutu daidai lokacin da zai zama abin alfahari ga kasa — Buratai
Domin yarana tun suna kanana nake nuna masu ba su fa da wani abu mai muhimmanci kamar ni uwarsu sannan ina nuna musu su guji fushina ba alheri ba ne a garesu.
Ina nuna masu su nemi faranta mini rai a koda yaushe shi ne ginshikin cin nasararsu duniya da lahira, inda tun suna ki har karatuna ya shiga gangar jikinsu.
Ba wannan kadai na yi ba, don na yi a aikace sun gani saboda yadda na zauna da tawa uwar mijin abin misali ne.
Ni mutum ce mai tsananin fada Malama Nabila, ita kuma uwar mijina rudewar tsufa ya zo mata da fitina kala-kala.
Sau da yawa sai ta ce dakina take so, haka nan zan kwashe kayan sawana in bar mata dakin da kayan dakina duka.
Sai ta yi watanni a ciki kuma sai ta ce dan sharri an kawo ta dakin suruka an ajiye; ita a maida ita dakinta.
Idan na sa kaya sai ta ce in cire in ba ta tunda danta ne ya saya kuma haka zan cire in ba ta komin kyawunsu ko tsadarsu kuma yawanci mahaifiyata ce take ba ni kyautar kayan saboda sana’arta ke nan.
Dole ne sai maigida ya sayo mata nama da kifi duk dare idan ba haka ba ta kwana tana mita cewa ya ba mu kayan dadi ita ya hana ta.
Wani sa’in kudinshi ke nan zai sayo mata, mu kuwa sai dai a yi dabara a samu abin da aka dafa.
Wani sa’in ni nake ba shi ko na ranto mashi a makwabta ya sayo mata.
A haka mijina ya kara aure, matar tun tana hakuri da fitinar uwar miji har ta kasa hakura.
Wata rana ta bi uwar miji ta yi mata tatas, ni kuwa na bita na nakada mata duka na ce ba za ki jawo mana bala’i ba.
Ta zo ta kwanta ciwon ajali, ta yi kashi nan fitsari nan, ni ke wanke mata jiki in gyara ta tsab, in rungume ta kamar yarinya in ba ta abinci.
Gab da za ta mutu ta kira danta – maigidana ta ce “Wane na yafe maka komi duniya da lahira, ka biya ni ban biyo ka komi ba.
Bukatata daya da kai, shi ne komin runtsi komin wahala, koda wasa kar ka sake ka bata ran wance, in kuwa har ka bata mata rai to na janye yafiyar da na yi maka.
Na haramta maka yi mata kishiya ko bayan raina, in dai ni na haife ka wane, to na umarce ka da hakan!”
To kin ga ribar hakuri ko Malama Nabila? Kin ga ribar kyautatawa? Kowa yana mamakin yadda na yi sanyi-sanyi da lallaba uwar mijina.
To ni abu biyu ne ya taimaka mini wajen jajircewa ta wannan bangaren, na farko da za a kai ni gidan miji wasiyar da mahaifina ya yi mini shi ne a kan in bi uwar miji in kyautata mata fiye da yadda zan bi mijina, fiye da yadda nake masu su da suka haife ni.
Ina ganin girma da kaunar mahaifina ba yadda za a yi in ketare umarninsa.
Na biyu shi ne Hadisin wadanda dutse ya datse da su cikin kogo suka yi tawassuli da kyawawan ayyukansu, daya daga cikin ya bayyana yadda yake hana kananan ’ya’yansa da iyalinsa abinci (madara) har sai iyayensa sun sha sun koshi abin da suka rage sannan ya ba ’ya’yan na shi.
Da kuma sauran Hadissai da suke nuna muhimmanci da albarkar da ke cikin kyautatawa mahaifa musamman mahaifiya.
Yanzu mijina komi zai yi sai ya nemi izini na, da zai kara aure sai da ya nemi izinina kuma sai wacce na zaba kuma daga cikin sharuddan aurensu shi ne dole ta rika mutunta ni ba batun raini ko jin ita ta fini domin tana amarya.
Yanzu biyar sun yi aure daga ciki bakwai din nan, amma ba ranar da ba su zuwa su gaishe ni kuma duk abin da suka saya ma matansu sai sun kawo mini nunkinshi.
Matansu suna girmama ni suna tsananin kyautata mini, in suna son wani abu a wajen mazansu, da ni suke kamun kafa.
Sai mako na gaba za mu karasa jin labarin Hajiya Larai da abin da ya faru tsakaninta da dan kawarta.
Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.